Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa
Published: 10th, December 2025 GMT
Wani dalibin shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, ya mutu a wani hatsarin mota bayan shi da wasu dalibai sun yi jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe.
Aminiya ta samu labari a ranar Talata daga wani mai amfani da Facebook mai suna Inside Edo, cewa hatsarin ya faru ne a ranar Litinin jim kaɗan bayan daliban sun gama jarabawar ƙarshe.
Majiyar ta ce motar ta yi ƙoƙarin wuce wata mota kafin ta kwace ta kuma daki wata babbar mota.
A cewar majiyar: “Wani mummunan hatsari ya faru a Ujoelen, kusa da makarantar firamare, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani dalibi da ya kammala karatu a jami’ar Ambrose Alli, Ekpoma.
“A cewar masu gani da ido, hatsarin ya faru ne yayin da aka yi yunƙurin wucewa da ɗaya daga cikin motocin da abin ya shafa.
“Wannan haɗarin ya jawo rasa iko, wanda ya haifar da mutuwar. Mazauna yankin da ke kusa sun ruga wurin, amma ba a iya ceto wanda ya jikkata ba.”
Haka kuma, Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa daliban sun kasance suna tukin mota cikin ganganci kafin su yi taho-mu-gama da wata babbar mota da ta tsaya a hanya.
An ce wanda ya rasu yana cikin jerin gwanon motocin da daliban da suka kammala karatu suka yi.
NAN ta ruwaito: “An ce yana cikin jerin gwanon sabbin daliban da suka shiga kan hanya a ranar Litinin jim kaɗan bayan bikin kammala makaranta.
“Lamarin ya faru ne lokacin da wanda ya rasu ya yi yunƙurin wuce wata babbar mota mai tafiya, amma ya buge da wata mota da ta tsaya a gefen hanya.”
Ƙoƙarin samun martani daga kwamandan sashe na jihar Edo a Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa (FRSC), Cyril Mathew, ya ci tura, domin lambar ba ta shiga har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Sai dai NAN ya rawaito daga baya Mathew ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu biyar suka jikkata a hatsarin.
Ya ce: “Daliban, bayan sun gama rubuta takardar jarabawa ta ƙarshe, sun shiga hanya cikin jerin gwanon motoci.
“A cikin wannan yanayi, ɗaya daga cikinsu ya yi yunƙurin wuce wata mota, ya kuma buge da wata babbar mota da ta tsaya a gefen hanya,” kamar yadda NAN ya rawaito daga Mathew.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: bIkin kammala makaranta Hatsari wata babbar mota jerin gwanon
এছাড়াও পড়ুন:
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Ta Taya Oluremi Tinubu Murnar Nadin Sarauta a Ile-Ife
Daga Aminu Dalhatu
Uwargidar Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta taya Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, murna bisa nadin ta a matsayin Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua a Ile-Ife na Jihar Osun.
Nadin ya kasance wani bangare na bukukuwan cikar shekaru 10 na Mai Martaba Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II akan karagar mulki na Ooni Ife, wanda ya jawo sarakunan gargajiya, manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane daga sassan kasar nan.
A wata sanarwa da sakatariyar yada Labarai ta Uwargidar Gwamnan, Rabi Yusuf, ta fitar, ta bayyana karramawar da aka yi wa Sanata Oluremi a matsayin abin yabawa, inda ta ce karramawar ta yi daidai da jajircewarta wajen ci gaban kasa, tallafawa mata, da kuma gudummawarta wajen karfafa iyalai da al’umma ta hanyar aikace-aikacen jin kai da manufofin raya al’umma.
Ta kuma yaba wa Ooni na Ife bisa zabar Sanata Oluremi Tinubu domin wannan girmamawa, tana mai cewa wannan zabe ya nuna irin jagoranci, tasiri da dogon lokacin da ta shafe tana hidima ga kasa.
A cewar Hajiya Huriyya, wannan zabe ya nuna rawar da masarautu ke takawa wajen gane karrama wadanda suka yi wa al’umma hidima.
Bikin ya nuna al’adun Yarbawa da kuma muhimmancin gudunmawar da masarautu ke bayarwa wajen gina hadin kan kasa.
Manyan shugabannin gargajiya da suka halarci bikin sun hada da Sarkin Musulmi, Olu na Warri, da Soun na Ogbomoso, da sauransu, wadanda suka hadu domin bikin cikar Ooni shekaru 10 a kan karaga da kuma nadin Sanata Oluremi Tinubu.