Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut
Published: 12th, December 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bada sanarwan cewa ya amince ya ziyarci birninBeirut babban birnin kasar Lebanon tare da gayyatar tokwaransa na kasar Lebanon Yusuf Rajji, kuma kwana guda bayanda da Rajji ya ki amincewa ya zo tehran don tattaunawa tsakanin kasashen biyu.
Shafin yanar gizo na labarai ‘The National’ ta kasar Amurka ya ce Rajji ya bayyana halin da ake ciki a kasarsa a matsayin dalilin da zai hana shi zuwa Tehran.
Aragchi ya ce ya fahinci cewa HKI ce ta hana Rajji zuwa Tehran, amma shi zai je birnir Beirut don tattaunawa kai tsaye da jami’an gwamnatin kasar Lebanon kan shirinsu mai hatsari na kokarin kwance damaran kungiyar Hizbullah. Kafin haka dai gwamnatin kasar Iran ta caccaki gwamnatin kasar Lebanon a kan wannan shirin wanda zai kawo karshen kasar Lebanon a matsayin yentacciyar kasa.
Gwamnatin kasar Iran ce take goyon bayan kungiyar Hizbullah wacce ta yi karan tsaye wa HKI, ta kumahanata mamayar kasar Lebanon har’ila yau take goyon bayan gwagwarmayan Falasdinawa da HKI tun ranar 8 ga watan Octoban shekara ta 2023. Kasashen yamma musamman Amurka sun rasa yadda zasu da kungiyar wacce ta hana HKI burinta na mamayar kasar Lebanon da kuma kafa Isra’ila babba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba December 12, 2025 Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026 December 12, 2025 Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza December 12, 2025 Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi Akan Doron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: gwamnatin kasar kasar Lebanon
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan
Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Dr. Masoud Pezeshkian, ya isa babban birnin Kazakhstan, Astana, bisa gayyatar takwaransa na Kazakhstan.
Mataimakin Firayim Minista na Kazakhstan ya tarbi Shugaba Pezeshkian a filin jirgin saman Astana. Wannan ziyarar ta zo ne bisa gayyatar shugaban Kazakhstan, wadda ke da nufin yin tattaunawa ta musamman tsakanin kasashen biyu.
A daya bangaren kuma Jakadan Iran a Moscow, Kazem Jalali, ya sanar da shirin ganawa tsakanin Shugaban Iran Masoud Pezeshkian da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Turkmenistan.
Wannan ya zo ne a lokacin ziyarar da Putin ya shirya kaiwa zuwa Ashgabat a ranakun 11 da 12 ga Disamba don halartar wani taron tunawa da Ranar Zaman Lafiya da Aminci ta Duniya.
Kasashen Iran da Rasha dai sun kara bunkasa harkokinsu an tsaro da ayyukan soji a cikin watannin baya-baya nan, duk da cewa akwai tsohuwar alaka ta soji a tsakanin kasashen biyu, amma dai a halin yanzu alakar tana samun ci gaba a cikin sauri da ba a taba ganin irinsa ba, wanda kuma ake ganin hakan ba zai rasa nasaba da irin halin Rashin tabbas da ake ciki yankin ba, inda kasashen biyu kawayen juna suke yin aiki kafada da kafada domin tukarar duk wani kalubale.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci