HausaTv:
2025-12-13@15:35:19 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169

Published: 13th, December 2025 GMT

169-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddeen Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan Shirin.

/////….Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan al-Mujtaba(a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s)  da muke kawo maku.

A cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da Magana dangane da dalilin da suka sa Imam Al-Hassan (a) ya sulhunta da mu’awiya dan Abusufyan, da kuma mika masa shugabancin al-ummar musulmi duk da cewa yasan hakan, ba alkhairi ne ga al-umma ba, amma ba yadda za iyi, saboda bai da mataimaka, bai da sojoji masu ikhlasi wadanda zasu yi yake tare da shi , sojoji wadanda zasu yi biyayya a gareshi. Su kuma yaki makinsa don neman yardarm Allah.

Daga cikin mun ambaci kha’incin da wasu daga cikin kwamandojin sojojinsa suka yi, musamman Ubaidullahi dan Abbas wanda dan Ammin Imam Al-Hassan ne, da sauran kwamandoji daga kabilun kinda da banu Murad. Yada karkyayyaki wanda mu’awiya yayi a cikin rundunar Imam Hassan (a) kuma tare da wani bincike ba rundunar ta amince da labarin karyan kuma suka dauki matakan cutar da Imam Al-Hassan (a).

Banda haka abubuwan da suka faru a yankin Mada’in wadanda suka hada da, wawason kayakin Imam Al-Hassan, (a) har ya kai ga wani ya zo yana jan sajjadan da yake zaune a kai yana son kwac shi daga hannunsa, sannan ni bakharije ya dama masa wuka a cinyarsa. Sannan ya sauka gidan walin Ma’adi’an wani daga cikin danginsa ya bawa gwamnan shawara, kan ya kama Imam Al-Hassan ya nemi aminci daga mu’awiya da shi, inda gwamnatin ya la’aneshi ya kuma barranta daga gareshi.

Har’ila a yau zamu dora a kan haka da cewa. Kwai hadisin manzon Allah (s) ingantacce wanda yake Magana cewa wani lokaci zai zo a cikin tarihin musulmi dansa Imam Hassan a matsayin s ana shugaba zai sulhunta tsakanin manya-manyan kungiyoyi biyu.

Yadisin yana cewa manzon Allah (s) yana cewa

{Lalle dana wannan shugaban ne, kuma mai yuwa Allah zai kyautata al-amarin bangarori biyu na musulmi masu girma}. Wannan hadisin ya yada a cikin musulmi kuma da alamun manzon Allah (s) ya fade shi ba sau guda ba. Sai ya fadeshi ya kuma nanata a wasu wurare masu yawa.

Don haka a lokacinda Imam Al-Hassan (a) yaga abinda ya faru da shi, har zuwa wannan lokacin, ya tuna da wannan hadisin kakansa manzon Allah (s) wanda ya fada dangane da shi da kuma matsayinsa na mai sulhuntawa, tsakanin manya manyan bangarorin musulmi biyu. Zai hana zubar da jininsu a tsakaninsu.

Malaman tarihin sun bayyana cewa Imam Al-Hassan (a) yana daga tsirarun shuwagabanni a duniya wadanda suka mika Mulki ga makiyansu ba tare da an zubar da jini ba.

Don haka jikin manzon Allah (a) babban Imam Al-Hassan (a) Allah yayi amfani da shi don sulhuntawa da tsakanin musulmi saboda kare jikinsu. Wannan hadisin wata mu’ajiza ce ta manzon Allah (a) inda ya fadi abinda zai faru nan gaba, wato yana da ilmin gaibu wanda Allah ya sanar da shi tun kafin al-abarin ya auku kimani shekaru 30 ko fiye da haka. Kuma ya auku kamar yadda fada.

Don haka muna iya cewa wannan hadisin yana daga cikin dalilin da suka sa Imam Al-Hassan (a) yayi sunhu da Mu’awiya dan Abusfyan.

Sai tare da wannan hadisin an kirkiro wani hadisin wanda suka jinginawa manzon Allah (s) wanda yake cewa wai yace lalle Khalifanci a baya na shekaru 30 ne sannan ya kasance Mulki.

Sun kirkiro wannan hadisin ne don su halattawa shuwagabannin da suka gabata abinda suka aikata, sannan su fadawa al-ummar cewa halin da suka fada ciki manzon Allah (s) ya fadeshi dan haka al-umma da amince da wannan halin.

Amma idan mun yi Nazari mai zurfi cikin hadisin, zamu ga cewa, Mulki a cikin al-ummar musulmi an fara shi tun zamanin khalifa na ukku, wato khalifa Uthman dan Affan, zamu ce sarkin bani umayya na farko. Don shi ne yad ora danginsa a kan musulmi suna kuma mulkin kamar yadda suka ga dama.

Kuma duk wanda ya karanta tarihi ya san cewa, danginsa su ne suka jawo masa kisa, saboda yadda suke zalunci shi kuma ya kasa yin kome, har sai da mutane suka gaji suka kashe shi.

Don haka Mulki an fara shi don zamanin khalifa Uthman, mu’awiya ya sake dawo da ita ne, bayan da Imam Ali (a) yayin kokarin maida shugabancin khalifancin Allah a bayan kasa kamar yadda Allah ya so. Amma suka yake shi har sau ukku.

Sai dai a wani hadisin manzon Allah (s) ya sifinta yadda al-amura zata kasance a bayansa, wanda kuma shi ne ya faru a kasa, inda yake cewa (Lalle farkon addininku yana faraway ne da annanabci, da kuma rahama, sannan ya kasance Mulki da kuma mulkin kama karya) wannan kamar yadda Suyudi a kawo a cikin tarihin Khulafa, shafi na 6.

Sannan wani abinda ya faru a zamanin Imam Ali (a) ya kara tabbatar da abinda manzon Allah (a) ya fada a wannan. Don a lokacin Mu’awiya ya sa aka yada labarin cewa ya mutu, don idan labarin ya je kunnen Imam Ali(a) ya je abinda zai fada. Ya san cewa Aliyu (a) shi ne kofar ilmin manzon Allah (s). don yaka abinda kuma ya faru kenan.

A lokacinda labari ya kai kunnen Imam Ali (a) sai yace

{Kun yawaita Magana a kan mutuwar Mu’awiya, na rantse da Allah bai mutu ba, kuma ba zai mutu ba sai ya mallaki karkashin kafafuwa ta} kamar yadda ya zo a cikin littafin Murujuz Zahab JZ 2 shafi na 465.

Banda haka wani zancen Imam Ali (a) ya fadawa dan Imam Al-Hassan(a), kamar yadda ya ruwaitishi da kansa, yana cewa: Wata rana babana ya fada mani, yace -ya Hassan! Yaya zakayi idan al-amarin nan ya koma hannun banu umayya, ? shugabanta mai fadin ciki, mai yelwan ciki, yana ci baya koshi, zai mutu bai ga mai taimaka masa daga sama, (ba mutumin kirki ba ) kuma baida mai bashi uzuri daga doron kasa (kan munanan abubuwan da ya aikata). Sannan ikonsa zai mamaye gabas da yamma, bayi zasu yi biyayya a gareshi, mulkinsa za iyi tsawo, zai tabbatar da sunnonin bidi’a da bata, kuma zai kashe gaskiya da sunnar manzon Allah (s), zai raga duniya a cikin mabiyansa, zai hanata wadanda suka cancanceta, zai kaskanta muminai karkashin ikonsa.    

Fasikai zasu yi karfi karkashin ikonsa, zai maida dukiya abinda jin dadi tsakanin masu taimaka masa, sannan zai maida bayin Allah masu masa khidima, gaskiya zata tsufa karkashin ikonsa, kuma bata zata bayyana, kuma zai kashe wadanda suka yi jayayya da shi a kan gaskiya}..

Wannan kamar yadda ya zo a cikin littafin Al-Ihtijaj  JZ 2 SH 11.

Don haka tare da wannan, Imam Al-Hassan(a) ya zama mai sulhu babba a cikin musulmi, kamar yadda kakansa manzon Allah (s) ya fada a baya.

Sai kuma ‘Isma’ wato tsarki daga yin kuskure. Wasu daga cikin laman shia sun bayyana cewa, sun yi Imani da cewa Imam Al-Hassan (a) Masumi ne daga yin kuskure kamar yadda ayoyin al-kur’ani suka tabbata da hakan, hakama hadisan kakansa manzon Allah (s) suka tabbatar da hakan. Daga cikin ayayin Al-Kur’ani, akwai ayar tsarki wace tazo cikin suratul Ahzab aya ta 33. Inda hadisin Alkisa ya nuna cewa da shi da kaninsa da kakansa da iyayensa ne Allah yake nufi da tafiyar da dauda daga garesu.

Don haka Imam Al-Hassan (a) masumine, baya kuskure don haka sulhun da yayi da Mu’awiya, ba kuskure ba. Duk da cewa ba zamu iya fahintar wasu al-amura da suka faru a cikin al-amuran sulhu ba.

Daga ciki  malaman da suka tafi a kan haka akwai Sayyid Murtdha, Alamul Huda. Sunansa Aliyu dan Hussain, kuma nasabarsa tana komawa zuwa kakansa kuma shugaban al-umma Imam Musa dan Jaafaru Alkazim(a) Limani na 7 daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s). A zamanin Abbasiyawa ya tafa zama shugaban Talibiyin. Yana da kaninsa wanda ake kira Sharid Radhi, wanda kuma ya rubuta littafin Nahjul Balagha.

Sharif Murtdha yana fada dangane da sulhun Imam Al-Hassan (Lalle shi-yana nufin Imam Al-Hassa- ya tabbata shi ma’asumi ne wanda yake samun taimakon Allah, da hujjuji bayyananu, da dalilin masu rinjaye, don haka babu makawa daga mika kai ga dukkan abinda ya aikata, ko da kuwa a cikinsu akwai abubuwansa da baza’a iya fahintarsa dalla-dalla ba. Ko kuma akwai wasu abubuwa wadanda zukata suke kyamarsa) wannan kamar yadda yazo cikin littafinsa Tanzihul Anbiya. Sh.69.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon  A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta December 13, 2025 Ziyarar Da Shugaban Rasha Ya Kai Indiya Ta Kara Karfafa Dangantakar Mosko Da Delhi December 13, 2025 Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na  Venuzuela December 13, 2025 Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Matatar Mai ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699 December 13, 2025 Iran da Rasha sun jaddada aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu December 13, 2025 Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai December 13, 2025 MDD ta amince da kudurin da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agaji a Gaza    December 13, 2025 Benin ta fitar da sammacin kama dan fafutuka Kemi Seba December 13, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Za ta Yi Zama Da Bangarorin Da ke Yaki A Sudan December 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kamar yadda ya wannan hadisin wadanda suka da Mu awiya da mu awiya

এছাড়াও পড়ুন:

Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila

Ghana ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin cin mutuncin ‘yan kasarta a filin jirgin sama na Ben Gurion na Isra’ila, bayan da aka tsare wasu fasinjoji ko kuma aka yi musu korar kare, ta kuma ce tana tunanin daukar irin wannan matakin na ramuwar gayya.

Ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa, ‘yan kasar bakwai da suka hada da ‘yan majalisar wakilai hudu, an tsare su ba tare da wani dalili ba, kuma an sake su ne bayan shafe sa’o’i masu yawa ana tatatunawa ta shiga tsakani na diflomasiyya, yayin da aka kori wasu uku.

Tawagar majalisar ta kasance tana halartar wani taron kasa da kasa kan harkokin tsaro ta yanar gizo a Tel Aviv, yayin da fasinjoji ukun da aka kora a ka tasa keyarsu zuwa Ghana.

Sanarwar ta kara da cewa, “wannan dabi’a ta cin mutunci na  mahukumomin Isra’ila abu ne mai matukar tayar da hankali kuma ba za a amince da shi ba,” ta kara da cewa “Ma’aikatar harkokin wajen kasar za ta gayyaci jami’an ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Accra domin mika musu sako na nuna bacin rai da kakkausar murya.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, “Ikrarin gwamnatin Isra’ila na cewa ofishin jakadancin Ghana ya gaza bayar da hadin kai wajen mayar da ‘yan kasar, kwata-kwata ba shi da tushe,” ta kara da cewa “aikin da jami’an Ghana suka yi a Tel Aviv ya kasance mai daukar hankali tare da bin dokokin kasa da kasa.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5  December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Rashin Bincike Ke Haifar Da Yawaitar Mutuwar Aure
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 2, sun ƙwato makamai a Borno
  • Duniyarmu A Yau: Iran Da Amurka A Yakin Kwanaki 12 Wa Ya Sami Nasara
  • Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
  • Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila
  • Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky