Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta
Published: 11th, December 2025 GMT
Hamas ta yi Allah wadai da Isra’ila da kakkausar murya kan gazawarta wajen cika alkawarin da ta dauka a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza.
Abduljabbar Saeed, memba na ofishin siyasa na Hamas, ya yi bayani na musamman kan tattaunawar da ake ci gaba da yi da masu shiga tsakani game da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a wata hira da Qods News a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa dukkan bangarorin da abin ya shafa sun yarda cewa gwamnatin Isra’ila ba ta cika mafi yawan wajibai nata ba a matakin farko.
Saeed ya koka da cewa, a lokacin matakin farko na tsagaita wuta, Isra’ila ta ci gaba da kashe fararen hular Falasdinawa, ciki har da yara da mata, a Gaza.
Ta kuma aza ayar tambayar cewa ta yaya zai yiwu a matsa zuwa mataki na biyu na tsagaita wuta lokacin da Isra’ila ba ta cika alkawuran da ta dauka a mataki na farko ba.
Saeed ya bayyana cewa yayin da Hamas ke shirye ta tattauna batun kwance damara, dole ne a yi hakan a cikin tsarin da ke girmama hakkokin Falasdinawa, yana mai jayayya cewa idan babu gwamnatin Falasdinawa ta gaske, babu wanda zai mika makamansa ba tare da ya karbi komai ba.
A ƙarshe, ya tabbatar da cewa Hamas za ta ci gaba da tattaunawa da masu shiga tsakani game da halin da ake ciki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan December 11, 2025 Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka December 11, 2025 Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan December 11, 2025 ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Antoni Gutress Ya Yi Allawadai Da Kutsen Da “Isra’ila” Ta Yi A Cibiyar Unrwa
Babban magatakardar MDD Antonio Gutress ya yi suka da kakkausar murya akan kutsen da ‘yan sandan Haramtacciyar Isra’ila su ka yi a cikin cibiyar kungiyar Agaji ta “Unrwa” a gabashin birnin Kudus.
A bayanin da babban magatakardar MDD ya fitar ya ambaci cewa; Har yanzu ginin na “Unrwa” mallakin Majalisar Dinkin Duniya ne, yana da kariya da bai kamata a taba shi ko shiga cikinsa ba.
Haka nan kuma ya yi kira ga “Isra’ilan” da ta yi gaggauta dawo da hurumin ginin na MDD da ba shi kariya,sannan kuma da hana daukar wasu Karin matakai akan gine-ginen MDD.
A nashi gefen, shugaban hukumar Agajin ta “Unrwa” Phillipe Lazarani ya wallafa sako a shafinsa na X cewa; Abinda Isra’ilan ta yi, wani sabon kalubale ne ga dokokin kasa da kasa, ya kuma zama wajibi ta kare da girmama gine-ginen MDD.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai ‘yan sandan haramtacciyar kasar Isra’ila su ka kutsa cikin ginin hukumar agajin ta “Unrwa” a unguwar Jarrah, a gabashin birnin Kudus.
MDD ce dai ta kafa Unrwa ne a 1951 domin taimakawa al’ummar Falasdinawa, sai dai kuma HKI ta haramta kungiyar da haka ta gudanar da ayyukanta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Saudiyya sun sake jaddada fadada dangantakarsu December 9, 2025 Faransa ta ce da hannunta aka dakile juyin mulki a Benin December 9, 2025 RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne December 9, 2025 An cire Tony Blair daga jerin wadanda zasu jagoranci Gaza December 9, 2025 Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon December 9, 2025 Trump Ya Yi Gefe Da Kasashen Turai Dangane Da Tattaunawa Kan Rikicin Ukraine December 9, 2025 Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba December 9, 2025 Najeriya : Matsala ce ta sa jirgin sojinmu yin saukar gaggawa A Burkina Faso December 9, 2025 Saudiya da Qatar Zasu Gina Layin Dogo Mai Sauri Tsakanin Kasashen Biyu December 9, 2025 Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki December 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci