Yawan Kudin Da Aka Kashe Na Zamantakewa A Watan Agusta A Kasar Sin Ya Kai RMB Triliyan 3.97
Published: 22nd, September 2025 GMT
Na hudu, an yi ta samu ci gaban sayayya sakamakon masu yawon bude ido daga ketare. Bisa ga manufar rage haraji lokacin barin kasa da kasar Sin ke gudanarwa, an shirya shirin “Sayayya a Sin” yadda ya kamata, wanda hakan ya canza fa’idar yawan baki daga ketare da suke yawon shakatawa a kasar zuwa habaka kudin da ake kashewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Li Qiang Ya Gana Da Tawagar Membobin Majalisar Wakilai Ta Amurka
A yau Lahadi 21 ga wannan wata da yamma, firaministan kasar Sin Li Qiang ya gana da tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka da Adam Smith ya jagoranta a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.
A yayin ganawar, Li Qiang ya bayyana cewa, Sin da Amurka manyan kasashe ne dake da muhimmanci sosai a duniya, kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka mai dorewa yadda ya kamata ya dace da moriyar kasashen biyu da begen kasa da kasa. Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen girmama juna, da zama tare cikin lumana, da yin hadin gwiwar samun moriyar juna. Kana kasar Sin tana son kasar Amurka ta yi hadin gwiwa tare da ita don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, ta hakan za a amfana wa kasashen biyu da ma duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp