Aminiya:
2025-12-14@21:24:45 GMT

Yadda aka yi bikin naɗa Rarara sarkin wakar ƙasar Hausa a Daura

Published: 14th, December 2025 GMT

Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Faruk Umar Faruk, ya naɗa fitaccen mawaƙin siyasar nan na Hausa, Dauda Kahutu Rarara, a matsayin Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa.

An yi bikin naɗin sarautar ne a garin Daura a ranar Asabar 13 ga watan Disamba, 2025 domin karrama rawar da Rarara yake takawa wajen haɓaka waƙoƙin Hausa da kuma tasirin da yake da shi a fagen nishaɗi da al’adu.

Jirgin sama ya yi hatsari yayin sauka a Kano Tsaro: Abba ya kafa runduna ta musamman da za ta ke tsaron tashoshin mota a Kano

Tun da farko mawaƙin da kansa ya wallafa goron gayyatar naɗin sauratar da za a yi masa a shafinsa na Facebook, a ranar 9 ga watan Disamba, 2025.

Rarara ya ce: “Ina gayyatar kowa da kowa zuwa wajen naɗin sarautata, mai taken ‘Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa’ sarautar da mai Alfarma Sarkin Daura ya yi min.

“Za a yi naɗin a fadar Mai Martaba Sarkin Daura a ranar Asabar, 13 ga watan Disamba, 2025, insha’Allah Allah.”

Bikin naɗin sarautar ya samu halartar manyan mutane, mawaƙa, jarumai, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibirin, Ali Nuhu da sauransu, inda masoya da magoya bayan mawaƙin suka nuna farin cikinsu.

Masoyan mawaƙin sun bayyana cewa wannan karramawa ta dace da gudunmawar da Rarara ya bayar ga al’adun Hausawa.

Rarara, wanda ya shahara wajen yin waƙoƙin siyasa da na zamantakewa, ya daɗe ana damawa da shi kuma yana daga cikin manyan mawaƙa a Arewacin Najeriya.

Sabuwar sarautar da aka yi masa na nuni da amincewa da gudunmawarsa wajen bunƙasa waƙa a harshen Hausa da kuma tasirinsa a cikin al’umma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Dauda Kahutu Rarara Daura Naɗi Sarauta Sarkin Daura Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bada sanarwan cewa ya amince ya ziyarci birninBeirut babban birnin kasar Lebanon tare da gayyatar tokwaransa na kasar Lebanon Yusuf Rajji, kuma kwana guda bayanda da Rajji ya ki amincewa ya zo tehran don tattaunawa tsakanin kasashen biyu.

Shafin yanar gizo na labarai ‘The National’ ta kasar Amurka ya ce Rajji ya bayyana halin da ake ciki a kasarsa a matsayin dalilin da zai hana shi zuwa Tehran. Ya kuma bada shawarar su hadu da Aragchi a wata kasa don tattaunawa kai tsaye kan shirin gwamnatin kasar na kwance damarar kungiyar Hizbullah.

Aragchi ya ce ya fahinci cewa HKI ce ta hana Rajji zuwa Tehran, amma shi zai je birnir Beirut don tattaunawa kai tsaye da jami’an gwamnatin kasar Lebanon kan shirinsu mai hatsari na kokarin kwance damaran kungiyar Hizbullah. Kafin haka dai gwamnatin kasar Iran ta caccaki gwamnatin kasar Lebanon a kan wannan shirin wanda zai kawo karshen kasar Lebanon a matsayin yentacciyar kasa.

Gwamnatin kasar Iran ce take goyon bayan kungiyar Hizbullah wacce ta yi karan tsaye wa HKI, ta kumahanata mamayar kasar Lebanon har’ila yau take goyon bayan gwagwarmayan Falasdinawa da HKI tun ranar 8 ga watan Octoban shekara ta 2023. Kasashen yamma musamman Amurka sun rasa yadda zasu da kungiyar wacce ta hana HKI burinta na mamayar kasar Lebanon da kuma kafa Isra’ila babba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba December 12, 2025 Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026 December 12, 2025  Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza December 12, 2025 Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro  Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi Akan Doron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe mutum 11 da jikkata wasu 29 a bikin Yahudawa a Ostireliya 
  • Yadda Za Ki Haɗa Sabulun Da Zai Gyara Miki Fata
  • Yadda Rashin Bincike Ke Haifar Da Yawaitar Mutuwar Aure
  • Yadda za ku cike neman aikin jami’an lafiya a Hajjin 2026 da NAHCON
  • Yadda za ku nemi aikin jami’an lafiya a Hajjin 2026 da NAHCON
  • Zan yi amfani da Salah a wasan Liverpool da Brighton — Arn Slot
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut
  • Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
  • Farashin Kayan Abinci Na Sauka Yayin Da Bikin Kirsimeti Da Sabuwar Shekara Ke Matsowa