Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Karin Tallafi Ga ‘Yan Gudun Hijira
Published: 18th, September 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke jihar.
Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron na kwana guda kan shirin ceton rayuka da karfafawa da kuma juriya (LEARP) wanda kungiyar FCDO ta dauki nauyin shiryawa a Abuja.
A wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Bashir Kabiru Ahmad, Kwamishinan ya bayyana cewa a halin yanzu jihar na karbar dubban ‘yan gudun hijira daga al’ummomi sama da 1,008 a fadin kananan hukumomin 14, kamar yadda aka gani a cikin rajistar zamantakewa na jihar.
Alhaji Musa Tsafe ya bayyana cewa, tallafin da ake bukata ya hada da bangarorin Rayuwa, Karfafawa, samun tallafin Kudi da Manufofi da sauran abubuwan da za a iya yi da nufin rage radadin halin da ‘yan gudun hijira ke ciki a jihar.
Alhaji Tsafe ya yabawa abokan aikin raya kasa bisa yadda suke ci gaba da tallafawa ‘yan gudun hijira da sauran marasa galihu a Zamfara.
A cewarsa, aikin da aka tsara domin aiwatar da shi da kungiyar Premier Urgence International (PUI) za ta yi zai kasance muhimmin taimako ga al’ummar jihar Zamfara.
Ya bayyana taron a matsayin wani ci gaba a kokarin jihar na inganta rayuwar ‘yan gudun hijira da marasa galihu musamman mata da yara.
Alhaji Tsafe ya tabbatarwa da abokan huldar cewa jihar Zamfara karkashin Gwamna Dauda Lawal ta samar da tsarin siyasa da samar da yanayin da kungiyoyin agaji ke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
REL/AMINU DALHATU.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: yan gudun hijira
এছাড়াও পড়ুন:
Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
Daga Usman Muhammad Zaria
Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.
Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.
Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin noma daban daban.
A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.
Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.
Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.
Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.
Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.
Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.
Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.
Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.
A garin Chuwasu dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.
Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.
Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.
Yace da farko suna da shakku akan amfani da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.
Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.
Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.
A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.
A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.
Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.
Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.