HausaTv:
2025-12-11@07:38:06 GMT

Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila

Published: 11th, December 2025 GMT

Ghana ta yi Allah-wadai da abin da ta bayyana a matsayin cin mutuncin ‘yan kasarta a filin jirgin sama na Ben Gurion na Isra’ila, bayan da aka tsare wasu fasinjoji ko kuma aka yi musu korar kare, ta kuma ce tana tunanin daukar irin wannan matakin na ramuwar gayya.

Ma’aikatar harkokin wajen Ghana ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Laraba cewa, ‘yan kasar bakwai da suka hada da ‘yan majalisar wakilai hudu, an tsare su ba tare da wani dalili ba, kuma an sake su ne bayan shafe sa’o’i masu yawa ana tatatunawa ta shiga tsakani na diflomasiyya, yayin da aka kori wasu uku.

Tawagar majalisar ta kasance tana halartar wani taron kasa da kasa kan harkokin tsaro ta yanar gizo a Tel Aviv, yayin da fasinjoji ukun da aka kora a ka tasa keyarsu zuwa Ghana.

Sanarwar ta kara da cewa, “wannan dabi’a ta cin mutunci na  mahukumomin Isra’ila abu ne mai matukar tayar da hankali kuma ba za a amince da shi ba,” ta kara da cewa “Ma’aikatar harkokin wajen kasar za ta gayyaci jami’an ofishin jakadancin Isra’ila da ke birnin Accra domin mika musu sako na nuna bacin rai da kakkausar murya.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, “Ikrarin gwamnatin Isra’ila na cewa ofishin jakadancin Ghana ya gaza bayar da hadin kai wajen mayar da ‘yan kasar, kwata-kwata ba shi da tushe,” ta kara da cewa “aikin da jami’an Ghana suka yi a Tel Aviv ya kasance mai daukar hankali tare da bin dokokin kasa da kasa.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5  December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Bindiga 18 Sun Muta a Wata Arangama da Rundunar Operation Fansan Yamma

Daga Nasir Malali

An kashe ’yan bindiga guda goma sha takwas a wani samame da Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta kai a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto.

A wata hira ta wayar tarho, wani shaida daga yankin, Malam Aminu Muhammad, ya shaida wa Rediyon Najeriya a Sokoto cewa, nasarar samamen ta fara ne bayan rundunar ta samu bayanin cewa wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako-mako a kan hanyar Tarah zuwa Karawa a Sabon Birni.

Sojojin sun garzaya cikin gaggawa bayan jin harbe-harbe, inda suka kusan awa guda suna musayar wuta da maharan.

Shaidan gani da idon ya ce sojojin sun  kwato bindigogi da babura takwas, tare da tabbatar da cewa babu jami’in tsaro ko farar hula da ya rasa ransa ko ya ji rauni a samamen.

Da aka tuntube shi ta waya, dan majalisar dokoki mai wakiltar Sabon Birni a Majalisar Dokokin Jihar Sokoto, Honarabul Aminu Boza, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa rundunar hadin gwiwar na ci gaba da gudanar da aikin bincike a maboyar ’yan bindigar tare da taimakon wani dan bindiga da aka kama wanda ke nuna wa sojojin hanya a yayin binciken.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky
  • Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD
  • Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu
  • RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne
  • Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba
  • Pakistan ta Bai Wa Taliban Ta Aghanistan  Zabi A Tsakanin Mu’amala Da Ita Ko  Da  ‘Yan Ta’adda
  • ‘Yan Bindiga 18 Sun Muta a Wata Arangama da Rundunar Operation Fansan Yamma
  • MِِِِDD:  Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya