Aminiya:
2025-12-12@12:28:39 GMT

‘Haduwata da masu garkuwa da ɗan uwana a dajin Zamfara’

Published: 12th, December 2025 GMT

Wani mazaunin Kano, Namadi Bawa, ya bayyana yadda ya shiga cikin daji a Jihar Zamfara domin kai kudin fansa ga ’yan bindiga da suka sace ɗan uwansa, inda ya tarar da su cikin mawuyacin hali na rashin lafiya, kafin daga bisani ya samu ya kubutar da shi. A tattaunawar mutumin da Aminiya, y ace an sace ɗan uwan nasa ne a Gusau babban birnin jihar Zamfara, a kan hanyarsa ta dawowa daga Sakkwato.

A cewar Namadi, ɗan uwansa ya ci karo da shingen da ya yi kama da na jami’an tsaro a hanya, sai dai daga baya aka gano ’yan bindiga ne suka yi masa kwantan bauna tare da wasu fasinjoji.

“Sun kira ni suka tambaya ko na san ɗan uwana, na ce eh. Suka ce sun sace shi kuma yana hannunsu. A lokacin kwana ɗaya kenan da sace shi,” in ji Namadi.

Cinikin kuɗin fansa da tafiya daji domin kai musu

Ya ce masu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa har Naira miliyan 16, amma bayan tattaunawa aka rage zuwa miliyan bakwai.

Namadi ya ce masu garkuwar sun yi gargaɗin cewa ba za su lamunci rage wani abu daga adadin kudin da aka yi cinikin ba, suna gargaɗin cewa muddin suka ƙirga kuɗin suka ga ba su cika ba, za a ga ba daidai ba.

“Sun ja hankali cewa kada a rage ko ƙwandala a ciki, idan aka rage za a ga ba daidai ba,” in ji shi.

Namadi ya bayyana yadda ya je da kansa ya kai kudin cikin daji.

A cewarsa, an umurce shi ya tsaya a wani ƙauye kafin daga bisani a nuna masa hanyar shiga. Daga bisani aka ba shi wata riga ya saka kafin ya isa wurin da aka karɓi kudin.

“Na zaci za su ƙirga kudin, amma sai suka tattaka su da ƙafa, suka ce sun cika. Bayan haka suka ce na gangaro daga kan dutsen da suka kai ni. Na yi ta kallo ko zan ga ɗan uwana, amma daga baya ne suka nuna min shi tare da wasu da aka sace, duk suna kwance cikin yanayin rashin lafiya,” in ji shi.

Yanayin dajin da masu garkuwar

Namadi ya ce yanayin da ya tarar da su ya nuna suna fama da cutar kwalara, inda aka ajiye su a bukka a tsakiyar dajin da ba motar da za ta iya shiga sai babur.

“Na san idan a wannan yanayin ne, ba za su yi dogon zango ba. Ta su za ta kare,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa ɗan uwansa da sauran da aka sace sun shiga mawuyacin hali, inda dole ne aka kai ɗan uwansa asibiti bayan an karɓo shi saboda yanayin da aka same shi.

Namadi ya kuma ce duk da fargaba da tashin hankalin da ya shiga, addu’a ce ta taimaka masa ya dawo gida lafiya.

“Mu ci gaba da addu’a saboda tana da tasiri a kan mutanen nan. Insha Allahu Allah zai kawo ƙarshen su,” in ji shi.

Cin karo da wasu masu garkuwar a hanyar dawowa

Bayan ya karɓo ɗan uwansa, Namadi ya ce a hanyarsa ta fita daga dajin ya sake cin karo da ’yan bindigar sun kamo wasu mutanen, suna kaɗa su zuwa cikin daji.

“Sun ba ni shawara kada na bi ta inda na zo, saboda akwai ƙungiyoyin masu garkuwa da dama a yankin waɗanda ba sa ga maciji da juna da za su iya sake kama mu,” in ji shi.

Daga nan sai ya ce duk da muggan makaman da ’yan bindigar ke da su, ba su fi ƙarfin gwamnati ba.

Ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙoƙari wajen kawar da ’yan bindiga a yankin, tare da fatan addu’ar jama’a za ta taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwalara masu garkuwa Zamfara masu garkuwar ɗan uwansa

এছাড়াও পড়ুন:

An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara

Rundunar ’yan sandan yankin Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wani mutum mai suna Ahmed Abubakar mai shekara 32, bisa zargin ƙoƙarin kai harsasai 1,000 ga ’yan bindiga a Jihar Zamfara.

Kwamishinan ’yan sanda na birnin, Miller G. Dantawaye, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a hedikwatar rundunar a Abuja ranar Laraba.

Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa

Dantawaye ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 3:30 na yamma, kuma tawagar musamman ta rundunar ce ta kama shi bayan samun sahihin bayanan sirri a Unguwar Dodo da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana mu’amala da wani abokinsa da aka gano sunansa Yusuf Mohammed, inda aka gano cewa yana shirin sayo harsasai 1,000 domin kai wa ’yan bindiga da ke cikin daji a Zamfara.

“Bincikenmu ya ƙara nuna cewa wani ɗan uwansa, Ahmed Yakubu, ne ya turo shi kuma yanzu ya cika wandonsa da iska, domin ya sayo ya kuma kai wa ’yan ta’adda da ke aiki a yankin su na Zamfara,” in ji CP Dantawaye.

Ya ce wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda a halin yanzu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama abokin aikin nasa da ya tsere.

Kwamishinan ya jaddada kudirin rundunar na kawar da masu aikata laifuka a Abuja da kewaye, tare da tabbatar da tsaron mazauna yankin.

Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da tallafa wa ’yan sanda ta hanyar bayar da rahoton duk wani abin da ake zargin laifi ta layukan gaggawa na rundunar.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
  • Yadda Bunkasar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ke Samar Da Karin Damammaki Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano
  • Bankin Duniya Ya Daga Hasashen Ci Gaban Tattalin Arzikin Sin Na 2025 Da Maki Kaso 0.4
  • BUA ya tallafa wa ɗaliban Sakkwato 200 da miliyan 40
  • Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
  • Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe
  • Yadda za ku cike neman aikin dan sandan Najeriya na 2025/2026
  • An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara