Ben Gafir Ya Yi Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam
Published: 12th, December 2025 GMT
Ministan taron Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ben Gafir ya sha alwashin rushe kabarin Sheikh Izzuddin al-Kassam dake kusa da birnin Haifa. Ben Gafir ya wallafa hotonsa na tsokana a shafinsa n asada zumunta a kusa da makwancin shahararren malamin addinin mususuluncin tare da motar buldoza a kusa da shi, tana rusa wata hema da aka gina daura da kabarin, wacce mutane suke yin salla a cikinta da kuma yin addu’oi.
Sheikh Izzuddin al-Kassam da reshen soja na Hamas ke dauke da sunansa, malamin addini ne wanda ya yaki Birtaniya da ‘yan sahayoniya a lokacin da suke share fagen gina haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya yi shahada ne dan lokaci kadan gabanin shelanta kafuwar wannan haramtacciyar kasa a 1948. Makwancinsa ya a garin Naishar dake kusa da Haifa, a arewacin Falasdinu dake karkashin mamaya. Ben Gafir ya ce; Wajibi ne mu rushe kabarin Sheikh Kassan dake garin Naishar, kuma a yau mun dauki hanyar yin hakan, saboda mu fara da rushe hemar dake kusa da kabarin. A cikin watan Ogusa ta ne Ben Gafir ya fada a gaban majalisar Knesset ta ‘yan sahayoniya cewa; wajibi ne a rushe kabarin Kassam baki daya. Tun daga wancan lokacin ne aka cire na’urar daukar hoto da take nuna abinda yake faruwa a wurin, sannan kuma aka kori mai yake tsaron wajen. A gefe daya,kungiyar Hamas ta bayyana abinda Ben Gafir yake nufin aiwatarwa da cewa; kai wa kololuwar lalacewa ce ta ‘yan sahayoniya. Jami’i a kungiyar Hamas Mahmud Murdawi ya ce, wannan matakin na Ben Gafir keta hurumin matattu ne da kuma wuraren addini,kuma laifin yaki ne. Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ‘yan sahayoniya suke kai wa wannan kabarin na Izzuddin Kassam hari, sai dai matakin da Ben Gafir yake son dauka a yanzu shi ne wuce gona da iri na koli akan wuraren masu tsarki na Falasdinawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi AkanDoron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan December 11, 2025 Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yan sahayoniya rushe kabarin Ben Gafir ya
এছাড়াও পড়ুন:
Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa dole ne musulman kasar Yemen maza da mata sun bi tafarkin addinin musulunci na kaiwa ga daukaka idan suna son daukaka.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran nakalto Al-Huthi yana fadar haka a jiya Laraba da yamma a lokacinda yake magana kan zagayowar ranar haihuwar Fatimah Azzahra diyar manzon Allah (s).
Malamin ya kara da cewa, Fatimah (a) abin koikoyo ne ga dukkan musulmi maza da mata a sanin Allah da halaye masu kyau don samun kusance ga Allah madaukakin sarki.
Al-Huthi ya kara da cewa a halin yanzu musulmi a ko ina suke a duniya suna fuskantar matsaloli, musamman musulman kasar Falasdinu wadanda HKI ta kashe dubban mutane daga cikinsu a cikin yan shekaru da suka gabata. Sun kashe mata da maza yara kanana hatta wadanda suke cikin iyayensu basu barsu ba.
Ya ce mafita ga musulmi itq ce koyi da iyalan gidan manzon Allah (s) musamman Fatima (a) don samun guzurin samun karfin fuskantar makiya a ko ina suke.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan December 11, 2025 ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci