2025-12-10@22:23:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5050
«Sheikh Ibrahim El Zakzaky»:
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Jigawa ta bayyana damuwa kan jinkirin shari’a wajen gurfanar da masu laifin rashawa, inda ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 479 da suka shafi cin hanci, amana da sauran laifuka makamanta a wannan shekarar ta 2025. Shugaban Hukumar, Barista Salisu Abdul ne ya...
Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi Allah wadai da sabbin gine-ginen mastugunnan yahudawa yan share wuri zauna guda 764 da isra’ila take ginawa a gabar yammacin kogin jodan , kuma ta bayyana shi a matsayin wani shiri na mayar da yankin ya koma na yahudawa. Wannan matakin yana nuna irin yadda isra’ila ta ke ci...
Shugaban kasar |iran Mas’ud pezeshkiyan da yake Magana a wajen taron ranar mata a kasar iran ya bayyana cewa maza ta da mata suna taka rawa iri daya wajen ciyar da alumma gaba, kan kyawawan ayyukan, kana ya jaddada cewa mata musamman iyaye suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da matasa masu tasowa da kuma...
Jakadan kasar iran na din din din a majalisar dinkin duniya Amir saeid iravani ya jaddada matsayin Tehran na ganin ta hana kisan kare dangi, kuma tayi tir da kisan kare dangi da HKI ta yi a yankin Gaza, kuma ya fadi hakan ne a wajen taron koli karo na 10 na majalisar dinkin duniya...
Daga Aliyu Lawal Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta, musamman masu rauni. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa,...
Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko. Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar. EFCC ta tsare Malami kan binciken...
Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya domin ƙarfafa dangantakar tsaro da haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu. A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan yaɗa labarai Ahmed Dan Wudil ya fitar, ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta shafi muhimman fannoni kamar...
Wani dalibin shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, ya mutu a wani hatsarin mota bayan shi da wasu dalibai sun yi jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe. Aminiya ta samu labari a ranar Talata daga wani mai amfani da Facebook mai suna Inside Edo, cewa hatsarin ya faru ne...
A yau ne dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Ostiraliya. Firaministan ƙasar ya bayyana dokar a matsayin abin alfahari ga Ostiraliya, yana mai cewa za ta shiga tarihi a matsayin muhimmiyar sauyi. Anthony Albanese ya ce ƙasarsa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki. Yara ƙasa da...
Tehran tana daukar bakwancin taron kwamitin bincike da ci gaban na kungiyar BRICS karo na 7Th wanda ya nuna irin yadda kasar Iran take ci gaba a cikin ilmin bincike da kuma na ci gaba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu taron na fadar cewa kasar Iran ta na samun ci...
Taron kasa da kasa na musamman wanda aka gudanar a wata Jami’a a nan Tehran dangane da nasarar da JMI ta samu kan HKI da Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan yulin da ya gabata ya jawo hankalin kasashen duniya da dama, sannan ya sauya yadda ake daukar HKI a yankin, musaman a...
Ministan makamashi na Iran Abbas Ali Abadi ya bayyana cewa; A halin yanzu Iran tana da ilimin aikewa da sanadarori cikin sararin samaniya da za su samar da hadari domin yin ruwan sama Ministan makamashin na Iran wanda ya gabatar da jawabi a gaban majalisar shawarar musulunci ta Iran a jiya Talata ya ce; Aiki...
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto ganawar da aka yi a tsakanin mataimakan ministocin harkokin waje na kasashen Saudiyya, Walid Khariji, da na China Miao Deo da kuma ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci. A yayin wannan taron, ministan harkokin wajen Iran ya bayyana gamsuwarsa da yadda kasar China take daukar matakai na...
Babban magatakardar MDD Antonio Gutress ya yi suka da kakkausar murya akan kutsen da ‘yan sandan Haramtacciyar Isra’ila su ka yi a cikin cibiyar kungiyar Agaji ta “Unrwa” a gabashin birnin Kudus. A bayanin da babban magatakardar MDD ya fitar ya ambaci cewa; Har yanzu ginin na “Unrwa” mallakin Majalisar Dinkin Duniya ne, yana da...
Majalisar Dattawa a ranar Talata ta amince da bukatar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin domin tabbatar da dimokuradiyya a kasar. Majalisar ta kuma ce tana goyon bayan matakin da shugaban ya ɗauka kwanaki kafin haka domin hana yunƙurin kifar da tsarin dimokuraɗiyya a makwabciyar kasar. Gwamnan Jihar Ribas...
Kananan yara sama da 93,200 ne ake sa ran yiwa allurar rigakafin cutar shan Inna da ake gudanarwa a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa. Kazalika, kananan yara sama da 53,800 ne ake sa ran digawa sinadarin vitamin A a yankin. Shugaban hukumar lafiya matakin farko na yankin Aminu Abubakar Kwandiko ya yaba da yadda...
Iran, China, da Saudiyya sun kammala taronsu na uku na Kwamitin Kasashen, inda Beijing ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da karfafa dangantaka tsakanin Tehran da Riyadh. Zaman, wanda mataimakin ministan harkokin wajen Iran Majid Takht-Ravanchi da takwarorinsa na Saudiyya Walid al-Kharaji da na China Miao Deo suka jagoranta aTehran yau Talata, a yayinsa...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta yi maraba da bayannan cewa an cire sunantsohon firaministan Burtaniya Tony Blair daga wadanda ake tunanin zasu jagoranci Gaza a shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump a Gaza. Jaridar Financial Times ta ruwaito a ranar Litinin cewa kasashen Larabawa da na Musulmi ne suka nuna adawa da...
Bayanai daga Lebanon na cewa Isra’ila ta sake kai sabbin hare-hare da jiragen sama a Kudancin Lebanon wanda ya sake nuna yadda take ci gaba da wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta da ta cimma da Lebanon. A ranar Litinin da yamma, jiragen saman yakin Isra’ila sun kai jerin hare-hare ta sama, lamarin da ya haifar da...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi watis da kasashen turai a tattaunawar dawo da zaman lafiya a Ukraine, wanda hakain ya sa kasashen rauni a cikin al-amuran kasar ta Ukraine. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a wani taro mai muhimmanci wanda Volodimir Zelesky shugaban kasar Ukraine ya yi da Firai...
Ana taro kan yadda manzon Allah mohammad dan Abdullahi (a) ya zauna da wadanda ba musulmi ba a rayuwarsa a Madina. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto hukuma mai kula da al-adu da kuma al-amuran addinin Musulunci a nan Iran tana cewa ana gudanar da wannan taron ne a dai dai lokacinda...
Matsalar rashin tsaro ce ta sa na yi waqar “Arewa”-SKD Arewa Muhsin Umar Chiroma wanda aka fi sani suna SKD Arewa, xaya ne daga cikin matasan mawaqan zamani da ludayinsu ke kan dawo wajen tashe, musamman a shafukan sada zaumunta. A hirarsa da Aminiya, saurayin mawaqin ya bayyana abin da ya xauki hankalinsa har ya...
Gwamantin Nigeria ta aike da jiragen yaki zuwa kasar Benin domin taimaka wa gwamnatin farar hula domin dakile yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar. Aikin da jiragen yakin su ka fara yi, shi ne shimfida ikonsu a sararin samaniyar kasar Benin a ranar Lahadin da ta gabata,adaidai lokacin da sojoji da suke biyayya...
Ministan ilimi da kere-kere na Iran Husain Simayi, wanda ya gana da jakadan kasar Turkiya anan Iran Hijabi Kalanjik ya bayyana azamar kasashen biyu domin yin aiki a wannan fagen. Ministan ilimin da kuma fasahar kere-kere na Iran ya kuma ya kuma ce; Iran tana bayar da muhimmanci ga jami’o’in Turkiya wadanda a bisa ma’aunin...
A wani rahoton da jaridar Jerissalam Post” ta buga ta ambaci cewa; Tun bayan farmakin 7 ga watan Oktoba 2023, ana kara samun matalauta da talauci. Rahoton ya yi nuni da cewa karuwar talaucin yana da alaka ne da yadda farmakin 7 ga watan Oktoba ya yi tasiri a cikin tattalin arziki “Isra’ila”. Haka nan...
Daga Aliyu Muraki Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce gwamnonin Arewa sun amince su sayi na’urorin zamani na tsaro da kuma daukar matasa aiki don tallafawa ayyukan tsaro domin magance matsalolin rashin tsaro a yankin. Gwamnan ya bayyana hakan ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Lafia, babban birnin...
Daga Nasir Malali An kashe ’yan bindiga guda goma sha takwas a wani samame da Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta kai a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto. A wata hira ta wayar tarho, wani shaida daga yankin, Malam Aminu Muhammad, ya shaida wa Rediyon Najeriya a...
Wakiliyar musamman ta majalisar dinkin duniya kan yankin falasdinu da aka mamaye Francesca Albanese ya bayyana irin halin da ake ciki a yankunan falasdinu da isra’ila ta mamaye a matsayin babban bala’I, ta ce kuma shi ne kisan kare dangi na farko da ya tada hankali duniya sosai. Da take bayani wajen rufe taron da...
Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi da kuma shugaban kasar Azarbaijan Ilham Aleyev a birnin Baku sun tattauna kan dangantakar dake tsakaninsu da kuma hanyoyin da zaa bi wajen warware kalubalen da ake fuskanta. Kasashen iran da Azarbaijan suna da alakar aladu da tarihi mai zurfi a tsakaninsu, kuma dukkan bangarorin biyu, sun jaddada...
A cikin wani taron hadin guiwa da aka yi takanin iran da sauran jakadun kasashen afrika guda 19 da sauran jami’an kasar iran, sun jadadda game da muhimmancin yin aiki tare a bangaren ilimi, bincike da kuma kiwon lafiya, da kuma yadda zaa kara karfafa alaka tsakanin Iran da kuma nahiyar Afrika. Taron ya nuna...
Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka – Ecowas – ta sanar da tura rundunar ko-ta-kwana domin taimaka wa sojojin Jamhuriyar Benin wajen kakkabe sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar da yammacin jiya Lahadi, ta ce “Shugaban Ecowas, bisa ga amincewar shugabannin kasashen kungiyar ya amince da...
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ya bayyana cewa makamai masu linzamu na dakarun sun fada kan matatar man fetur na Haifa a HKI har sau biyu a yakin kwanaki 12 da ta fafata da Iran a cikin watan Yunin wannan shekara. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya...
Firai ministan kasar Iraki Mohammad Shia Assudani ya bayyana cewa gwamnatinsa bata tushe asusun kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon da kuma Ansarallah ta kasar Yemewn ba. Kamfanin dillancin labaran Ip na kasar Iran IP ya nakalto sudanina cewa gwamnatinsa tana kokarin hana tasowar wani riki a yankin sannan da kuma kaucewa duk wani rikicin siyasa...
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baghaie ya yi tir da kashe fararen hula a garin Kalogi dake Jahar Kurdufan na Sudan. Bugu da kari kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kawo karshen abinda yake faruwa a wannan kasar. Kusan mutane...
Fitacce mai shirya fina-finai dan kasar Iran Majid Majidi ya sami kyauta ta musamman a wurin bikin fina-finai na Eurasia, saboda gagarumar rawar da yake takawa a fagen shiryafina-finai da su ka shahada a duniya. A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka bude bikin a birnin Moscow wanda ya sami halartar ministan al’adu...
An gano gawar wani malamin makarantar Islamiyya kuma mahaifin ’ya’ya bakwai, Malam Awwal Yakubu, a cikin wani kango da ke rukunin gidaje na Talba a birnin Minna, na Jihar Neja. Malam Awwal, yana da makarantar Islamiyya a unguwar Barikin-Saleh, an neme shi sama ko ƙasa tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata. ’Yan bindiga sun...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya tabbatar da cewa har yanzu Amurka ba ta nuna sha’awarta ta shiga “tattaunawa mai ma’ana ba,” yana mai sake nanata cewa dole ne Washington ta fara amincewa da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya na zaman lafiya a karkashin Yarjejeniyar hana yaduwar Makaman Nukiliya ta (NPT). A...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa Hamas ta bayyana cewa za ta mika makamanta ne kawai ” idan Isra’ila ta kawo karshen mamaya, tana mai jaddada cewa ba za a iya kwance damarar makamai ba a cikin yanayin da ake ciki na zaluncin soja da siyasa. Babban jami’i a ofishin siyasa na Hamas kuma babban mai shiga tsakani...
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana sabbin dabarun tsaron Amurka na cimma maradun gwamnatin Isra’ila ne. Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce sabbin dabarun tsaron Kasa na Amurka (NSS) da ke bayyana ka’idojin Washington da muhimman manufofin harkokin waje a zahiri cimma maradun tsaro ne ga gwamnatin Isra’ila ne. Esmaeil Baghaei ya yi wannan...
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a...
Tom Barrack jakadan Amurka na musamman a kasar Siriya ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka ta yi kokarinkifar da gwamnatin JMI a baya har sau biyu amma ta kasa yin haka. Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto Barrack yana fadawa wani kamfanin dillancin labaran UAE a ranar jumma’an da ta gabata, ya...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Bakir Qalibaf ya yi tir da kungiyar kasashen larabawa na yankin tekun Farisa, wadanda suka fidda bayanin bayan taronsu a baya bayan nan suka allawadai da kuma nuna goyon bayansu ga kasar UAE kan mallakar tsibiran Tumb babba da tumb karami da Abu Musa. Kamfanin dillancin labaran IP na...
Kungiyar ‘yan wasan ” Taekwondo” Iran dake kasa a shekaru 21 sun zama gwarazan duniya da aka yi a birnin Nairobi, bayan da su ka sami zinariya 3 da azurfa 1 sai kuma tagulla biyu. Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya nakalto cewa; a jiya Asabar ne aka kawo karshe gasar wasan na ” Taekwondo” wanda...
Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri ta Jihar Jigawa ta yi kiyasin kashe kudade miliyan dubu 161 da milyan 336 domin gudanar da ayyukan hanyoyin mota da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara ta 2026. Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Isah, ya bayyana haka lokacin da ya ke kare kiyasin kasafin kudin...
A wata tattaunawa ta wayar tarho da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da takwaransa na kasar masar Badr Abdelatty sun bayyana cewa isra’ila na ci gaba da kai hare-hare da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta a Gaza da kuma kasar labanon, Ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude...
Fira ministan kasar Qatar shaikh mohammad bin Abdurrahaman al thani yayi gargadi game da ci gaba da kai hare-hare da kame falasdinawa da HKi ke yi a yankin gaza, ya jaddada cewa shirin da shugaban Amurka ya bullo da shi na zaman lafiya zai zama gaskiya ne idan isra’ila ta janye dukkan sojojinta a yankunan...
Rahotanni sun bayyana cewa kungiyoyin kare hakkin bil adama na yankin falasdinu sun yi gargadi game da makircin da isra’ila ke kullawa na kashe Marwan bargusu daya daga cikin shuwagabanin falasdinawa a inda take tsare da shi a gidan yari, samakamon gana masa azaba da aka yi . Babban darektan kungiyar pps Amad Najjar yayi...
Hukumar Kwastam, ta kama kilo 25.5 na hodar iblis a wani jirgin ruwa na ƙasar Brazil mai suna MV San Anthonio a tashar jirgin ruwa ta Legas. An ɓoye hodar cikin ƙananan jakunkuna biyar. ’Yan bindiga sun harbe ɗan sanda har lahira a Edo Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista...
An harbe wani jami’in ɗan sanda har lahira, yayin da yake tsaka da binciken ababen hawa a Benin a Jihar Edo. Kakakin rundunar, CSP Moses Yamu, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a, lokacin da jami’an rundunar suka tsayar da wata baƙar mota ƙirar Lexus, amma ta ƙi tsayawa. ’Yan...
