HausaTv:
2025-12-08@18:41:48 GMT

Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki

Published: 8th, December 2025 GMT

Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka – Ecowas – ta sanar da tura rundunar ko-ta-kwana domin taimaka wa sojojin Jamhuriyar Benin wajen kakkabe sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar da yammacin jiya Lahadi, ta ce “Shugaban Ecowas, bisa ga amincewar shugabannin kasashen kungiyar ya amince da tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Jamhuriyar Benin nan take.

Dakarun sun kunshi sojoji daga kasashen Najeriya da Saliyo da Cote d’Ivoire da kuma Ghana. Kuma za su taimaka wa gwamnati da kuma dakarun Jamhuriyar Benin wajen kare martabar kundin tsarin mulki da na kasar ta Benin.”

Rahotanni daga jamhurriyar Benin na nuni da cewa an kama sojoji da dama bayan wani yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba , Mutanen da aka kama sun haɗa da waɗanda ake zargi da jagorantar yunƙurin juyin mulkin.

A wata sanarwa da ya yi a gidan talabijin, ministan harkokin cikin gidan kasar Alassane Seidou, ya bayyana cewa dakarun kasar sun yi nasarar dakile yunkurin bayan da sojoji suka bayyana a gidan talabijin na kasar suna ikirarin cewa sun tsige shugaba Talon.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025  Macron Na Faransa Ya Yi Wa Najeriya Alkawalin Taimakawa Akan Matsalolin Tsaro December 8, 2025 Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka  Teke Fuskanta December 8, 2025 Majid Majidi Na Iran Ya Sami Kyauyar Girmamawa Daga Cibiyar Fina-finai Na “Eurasia Dake Kasar Rasha December 8, 2025 Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa December 7, 2025 Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi) December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Jamhuriyar Benin

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato

Sojoji sun kashe wasu da ake zargin ’yan bindiga ne da suke ƙoƙarin yi garkuwa da ayarin ’yan kasuwa a kan hanyar Tarah–Karawa da ke Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

’Yan kasuwar na kan hanyarsu daga ƙauyen Tarah zuwa kasuwar mako a Sabon Birni ne lokacin da ’yan bindiga suka kai musu hari a Kwanan Akimbo da misalin karfe 8 na safe.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin da ke sansani a Kurawa sun ji karar harbe-harbe, suka garzaya wajen, inda aka yi musayar wuta na kusan sa’a guda.

“Sojoji sun yi musu luguden wuta, daga baya ’yan bindigar suka ja da baya suka tsere zuwa maɓoyarsu a can bayan rafin.

Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso An kama tsohon fursuna da bindiga ƙirar AK-47

“Mun ƙirga gawarwakin ’yan bindiga tara a yankinmu, sannan aka gano wasu hudu a dajin kusa da rafin. Sojoji kuma sun kwashe makamai da babura da dama suka kai Kurawa,” in ji wani mazaunin.

Ya ƙara da cewa mutane biyu ne suka samu raunuka, suna karbar magani a asibiti, amma dukkan ’yan kasuwar sun tsira ba tare da wani rauni ba. “Babu asarar rayuka a ɓangaren sojoji,” in ji shi.

Al’ummomin Kurawa da maƙwabtansu sun yi murna da nasarar da sojojin suka samu.

Ɗan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza, ya ce an gano gawarwakin aƙalla tara daga cikin ’yan bindigar, kuma bincike na ci gaba.

“An kwato makamai da babura da dama daga hannunsu. Ina fatan sojojinmu za su ci gaba da irin wannan aiki,” in ji shi.

Wannan lamari ya faru ne kwana guda bayan da ’yan bindiga suka kai hari ƙauyukan Gatawa da Shalla da ke Sabon Birni da Isa, inda suka kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da mata da dama.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato
  • Dalilin yawaitar juyin mulki a Afirka ta Yamma
  • Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin
  • Yadda muka daƙile yunƙurin juyin mulki a Benin — Sojin Saman Najeriya
  • Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa
  • Fadar Shugaban Kasar Benin ta ce Har Yanzu Talon Ne a Kan Mulki
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Benin
  • Jigajigan Majalisar Ribas 17 Sun Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
  • Cikakken jadawalin rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026