EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige
Published: 11th, December 2025 GMT
Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama tare da tsare Tsohon Ministan Ƙwadago kuma Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Chris Ngige.
Mai magana da yawun Ngige, Fred Chukwuelobe ne, ya tabbatar da hakan da safiyar ranar Alhamis. bayan wasu rahotanni da aka yaɗa cewar an sace Ngige.
An koro ’yan Najeriya 32 kan kasuwancin miyagun ƙwayoyi a Indiya Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPCChukwuelobe, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “Ngige yana tare da EFCC.
Har zuwa yanzu EFCC ba ta bayyana dalilin da ya sa ta tsare Ngige ba.
Ana sa ran hukumar za ta fitar da sanarwa game da kama shi da kuma binciken da ta ke yi a kansa.
Ngige ya zama mutum na biyu daga cikin tsoffin ministocin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da aka tsare a baya-bayan nan.
Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, shi ma yana hannun EFCC.
Hukumar ta ce tana binciken Malami ne kan wasu kuɗaɗen dala miliyan 310, wanda aka dawo da su Najeriya.
Sai dai ya musanta tuhumar da ake masa, inda ya bayyana cewa zarge-zargen ba su da tushe.
Masu sharhi a shafukan sada zumunta sun nuna damuwa kan yadda ake tsare tsoffin ministoci ba tare da bayyana dalili ba.
A gefe guda kuma, masu sharhi kan harkar siyasa sun ce irin wannan mataki na EFCC na nuna yadda hukumar ke zage damtse wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: tsarewa
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna cin wasu tsirrai, ganye, ko ababen da ke dauke da sinadarai masu haɗari, waɗanda daga baya suke taruwa a jikinsu har su zama guba ga mutum idan aka ci su.
Wasu lokuta ma waɗannan gubobi ba daga abincin dabbar suke fitowa ba, sai dai daga sinadarai da ake amfani da su wajen kiwon su kamar magungunan kiwo, sinadaran rigakafi, ko ma gurɓatattun ruwa da suke sha.
NAJERIYA A YAU: Kudaden Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi Zai Lashe DAGA LARABA: Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan TsaroShin ko ta wadanne irin hanyoyi alumma ke cin guba ta hanyar abincin da suke ci?
Wadanne hanyoyi za a bi don magance afkuwar hakan?
Wadannan da ma wasu tambayoyin shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.
Domin sauke shirin, latsa nan