Aminiya:
2025-11-03@07:46:34 GMT

Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU

Published: 27th, August 2025 GMT

Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin hira da gidan talabijin na Trust TV.

’Yan bindiga sun sace ma’aurata da ’yarsu mai shekara ɗaya a Katsina DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa

Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita.

Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba.

“Babu saɓani a tsakaninmu da tawagar gwamnati,” in ji shi.

“Mun amince kan abubuwa da dama, sai dai shugabanninsu, Ma’aikatar Ilimi da Gwamnatin Tarayya ba su ɗauki mataki kan kowanne ba.”

Ya danganta yawan ficewa daga Najeriya da malamai da likitoci ke yi saboda ƙarancin albashi da mummunan yanayi da suke ciki.

A asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos inda yake aiki, ya ce aƙalla likitoci 20 sun bar aiki cikin shekara biyu.

“Yanayin daidai yake da na malaman jami’a. Idan ƙarancin albashi ne ke sa mutane barin aiki, me ya sa ba za a ƙara albashi a riƙe su ba?” ya tambaya.

Ya ƙara da cewa ƙasashe da dama a Afirka suna ɗaukar malaman Najeriya aiki.

“A Uganda, a cikin jami’a guda ɗaya za ka iya samun malamai ’yan Najeriya sun kai 20,” in ji shi.

Shugaban ASUU ya kuma nuna damuwa kan mummunan yanayin kayan aiki a jami’o’in Najeriya, inda ya ce hakan na daga cikin dalilan da ya sa ba sa samun matsayi mai kyau a duniya.

Ya ce daga cikin jami’o’i 333 da faɗin Najeriya, guda biyar ne kaɗai ke cikin jirin manyan jami’o’i 1,000 a nahiyar Afirka.

Ya ce malamai ba sa jin daɗin tafiya yajin aiki, amma gwamnati na tilasta musu hakan saboda rashin ɗaukar mataki.

“Yajin aiki yana shafarmu, iyalanmu, da ɗalibanmu. Amma idan gwamnati ba ta yi komai ba, harkar ilimi za ta ci gaba da taɓarɓarewa.”

Ya yi kira ga kafafen yada labarai, iyaye, ƙungiyoyi, sarakuna da shugabannin addinai da su haɗa kai wajen nema wa ɓangaren ilimi sauyi a Najeriya.

“Wannan ba batun ASUU ne kaɗai ba. Muna fafutukar samun ingantaccen tsari ne, da kyakkyawar makoma, da kuma alheri ga ƙasarmu,” a cewarsa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗalibai Gwamnatin tarayya Yajin aiki

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 

 

A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin nasara a shekara mai zuwa.(Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik November 1, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka October 31, 2025 Daga Birnin Sin Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini
  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 
  • Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m