Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta bada tabbacin ci gaba da kulawa da harkokin rigakafi da kiwon lafiya baki daya.

Shugaban karamar hukumar, Builder Muhammad Uba ne ya bada wannan tabbacin lokacin taro da ake gudanarwa a kowace rana kan al’amuran rigakafin cutar Polio da aka gudanar a fadar Hakimin Birnin kudu.

Yace karamar hukumar zata kara da bada fifiko wajen tallafawa harkokin rigakafi domin dakile yaduwar cututtuka a yankin.

A don haka, Builder Muhammad Uba ya bukaci iyaye su kara himma wajen bada hadin kai da goyon baya ga jami’an lafiya a duk lokacin da ake gudanar da rigakafi.

A jawabin da ya gabatar mai kula da al’amuran rigakafi na yankin, Malam Abubakar Alhassan Garki yace ana sa ran yiwa kananan yara 194,000 rigakafin cutar shan inna a karamar hukumar.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Yara masara zuwa makaranta barazana ne ga kasa — Shettima

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya ce yawan yara marasa zuwa makaranta a Najeriya a barazana ce da ke buƙatar haɗin gwiwa daga dukkan matakan gwamnati da masu ruwa da tsaki.

Shettima ya yi wannan bayani a taron Zauren Ilimin Najeriya na 2025 da aka gudanar a Abuja, wanda Kungiyar Gwamnonin Najeriya tare da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da abokan hulɗa suka shirya.

Ya ce matsalar ilimi ba za ta iya warwarewa da ƙoƙarin gwamnati kaɗai ba, yana mai jaddada cewa: “Yawan yaran da ba sa zuwa makaranta bukatar gaggawa ce ta ƙasa da ke buƙatar haɗin kai tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi, kananan hukumomi da al’umma.”

Shettima, wanda mai ba shi shawara na musamman Aliyu Modibbo Umar ya wakilta, ya ce dole malamai su samu horo mai kyau, kulawa da kuma kima a matsayinsu na ƙwararru domin a samu ingantaccen ilimi.

An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba

Ya kuma yi kira da a faɗaɗa ilimin sana’o’i da fasaha domin matasa su samu ƙwarewar da za ta taimaka musu a kasuwa. Ya ce hakan na buƙatar kuɗi masu dorewa da aka tsara yadda ya kamata.

Mataimakin Shugaban Kasa ya bayyana cewa duk da ƙarin kuɗin da gwamnati ta ware wa ilimi daga Naira tiriliyan 1.54 a 2023 zuwa Naira tiriliyan 3.52 a 2025, gibin kuɗi ya yi yawa fiye da abin da gwamnati za ta iya ɗauka ita kaɗai.

Ya ambaci ƙarin kuɗin da aka ware wa hukumar TETFUND, UBEC da asusun tallafin ilimi na NELFUND, ciki har da Naira biliyan 86.3 da aka raba wa ɗaliban jami’a sama da 450,000 a ƙarƙashin tsarin lamunin ɗalibai.

Sai dai ya jaddada cewa gina tsarin ilimi mai ɗorewa na buƙatar haɗin gwiwa daga kamfanoni masu zaman kansu, shugabannin masana’antu, ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai, masu bayar da tallafi da al’umma.

Shettima ya ce: “Dole mu wuce tsarin gwamnati kaɗai wajen bayar da kuɗi, mu rungumi haɗin gwiwa da zai tallafa wa dakunan gwaje-gwaje, cibiyoyin bincike, cibiyoyin sana’o’i, ƙungiyoyin kirkire-kirkire da asusun tallafi.”

Ya kuma bukaci kananan hukumomi da masarautu su ɗauki nauyin gine-ginen makarantu, gyara, tsaro da kuma kulawa da malamai.

Shettima ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a taron da su jajirce wajen samar da kuɗin ilimi mai dorewa, yana mai cewa haɗin kai ne kaɗai zai iya sauya tsarin ilimi a Najeriya tare da shirya matasa domin fuskantar duniyar zamani.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yaba Ma Iyaye Bisa Goyon Bayansu ga Shirin Rigakafin Shan Inna a Karamar Hukumar Ringim
  • Yara masara zuwa makaranta barazana ne ga kasa — Shettima
  • An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia
  • Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba
  • Matsalar rashin tsaro ce ta sa na yi waqar “Arewa”-SKD Arewa
  • Zaben 2027: NNPP Ta Sha Alwashin Maye Gurbin Tinubu da Radda
  • Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace
  • Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano
  • Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi