Zan yi amfani da Salah a wasan Liverpool da Brighton — Arn Slot
Published: 12th, December 2025 GMT
Mai horar da Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Liverpool, Arne Slot ya ce zai sanya Mohammed Salah cikin jerin ’yan wasan da za su bugawa Liverpool wasa da Brighton a ranar Asabar.
Slot wanda ya samu saɓani da Salah kan ajiye shi a benci a wasanni uku a jere, ya ce yana da yaƙinin cewa, Salah zai ci gaba da bugawa ƙungiyar wasa.
Ya kuma ƙara da cewa, zai ci gaba da tattaunawa da ɗan wasan domin ya ci gaba da taka leda a Anfield.
Salah mai shekara 33, baya cikin jerin ‘yan wasan da suka doke Inter Milan a Italiya a ranar Talata, wanda hakan ke bayyana tsamin rashin jituwa tsakaninsa da Arne Slot.
Liverpool dai zata karɓi baƙuncin Brighton a wasan mako na 16 da ƙarfe 3 na ranar Asabar.
Mo Salah, ɗan asalin ƙasar Masar, ya bugawa Liverpool wasanni 420 tare da zura ƙwallaye 250 cikin zamansa a ƙungiyyar.
Ɗan wasan zai bar Liverpool domin dawowa ƙasar Masar a ranar 15 ga watan Disamba, kwanaki 6 gabanin fara kofin nahiyyar Afrika da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Arne Slot
এছাড়াও পড়ুন:
Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan bana na Turkiyya
Ɗan wasan gaban Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Galatasaray ɗan asalin Najeriya, Victor Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na bana, a bikin bayar da kyaututtuka ta GQ Türkiye na maza na 2025.
Ɗan wasan mai shekara 26 ya sami kyautar mafi girma a bikin da aka gudanar mai ban sha’awa.
Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699 Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a BinuwaiYa sami kyautar ne saboda rawar da ya taka a Galatasaray a kakar wasa ta bara, inda ya zura ƙwallaye 37 kuma ya taimaka wajen zura ƙwallo sau bakwai a wasanni 41, wanda hakan ya sa Galatasaray ta lashe gasar Turkiya.
Osimhen ya karya tarihin Galatasaray na zama ɗan wasan da ya fi tsada a tarihin Ƙungiyar bayan ya koma akan kuɗi Yuro miliyan 75 daga Napoli.
Osimhen ya ci gaba da yin abin a yaba a wannan kakar, inda ya riga ya zura ƙwallaye 11 a wasanni 14 da ya bugawa ƙungiyar da ke birnin Istanbul.
Galatasaray na matsayi na ɗaya akan teburin babbar gasar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Turkiyya da maki 36 a wasanni 15 da ta buga yayin da Trabzonspor ke matsayi na biyu.