2025-12-12@09:51:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 17
«Annabi SAW Ya»:
Wata rana, Abu Huraira (RA) yunwa ta kama shi matuka, har yazu wurin mimbarin Annabi SAW da ke cikin masallacin Annabi, sai ya fadi a wurin, duk wadanda suka zo wurin suka ganshi, sai suce Allah Sarki, wane ba shi da lafiya har sai da Annabi ya zo ya ganshi, sai yace masa, Abu Hurairah kana jin yunwa ko? Sai ya amsa da eh. Take Annabi SAW ya ce masa, biyo ni zuwa daki na. Annabi yasa aka kawo masa nono a dan koko kamar yadda aka saba, Abu Hurairah yana jira a ce masa ya sha, sai Annabi SAW ya ce masa ya kira ‘yan uwansa Ahlul suffati, kuma jama’a ne masu yawa, da isowarsu, Annabi SAW ya sa...
Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna...
Idan ka duba tarihin duniya gabadaya da tarihin annabawa, tarihi ne na wayewar duniya tun daga Annabi Nuhu (S.A.) har zuwa Manzon Allah (S.A.W.) kamar duniya tana ‘yar makaranta ce ta fara da Nazare, ta zo Firamare zuwa Sakandire har zuwa Jami’a, sannan aka yaye ta, yanzu da zuwan Manzon Allah an yaye duniya, yanzu duniya ba ta bukatar sai an aiko annabi, ba ta bukata sai an aiko ma’aiki, a’a wanna abu da Manzon Allah ya zo da shi za mu iya kafa dalili da shi mu shirya kanmu ba sai da annabi ba. Wannan abu da Manzon Allah ya zo da shi yanzu ya kafa dalili da shi, da shi muka karantar da kanmu ba sai da Annabi...
Saboda haka mu saki ilimi, mu ba ilimi hanya kar mu ji tsoro, mu je mu nemo shi duk inda yake kayanmu ne. Manzon Allah ya ce “ilimi hikima ce kayan mumini ne, saboda haka kar ka ji tsoro, ba wanda ya fi karfin Allah, ba wanda ya fi karfin Manzon Allah (S.A.W.). saboda haka ba wanda zai je ya shiga halwa ko ya shiga wani tunani ko ya shiga kaza har ya zo “summa dana fatadalla”, ba wanda zai zo nan sai dai Manzon Allah (S.A.W.). Dan haka Sufaye ba sa jin tsoron ko waye zai yi maganar ilimi, ba sa jin tsoron ko wane littafi bare damuwa, haka kuma ba a iya kada su, saboda duk abin da...
Ga alkawarin, komai da Allah Ya yi wa wani, Allah Ya fada. Allah bai boye komai ba, sai abin da ya yi ga Annabi Muhammadu (S.A.W.), nan ko ba a fada ba, amma kowane annabi komai matsayinsa in ka duba sai ka ji sirrin da aka yi da shi. Yanzu game da wannan ma’aiki da annabawan da duk Allah ya tara su, ga abin da Allah Ya ce (ya ku) Annabawa, idan na ba ku littafanku da kyawawan dabi’u da hikima da ma’arifanku (ai, misali, an ba ka wukar yanka da takobin yanka da tagwayen masu ke nan). Sannan wani ma’aiki ya zo maku (Manzon Allah ake nufi) za ku bar wannan sakon da wannan nadin da na yi maku...
Kudubi yana tare da kwayar zarrar kowace halittar Allah, shi yake isar mata da sakon magana, wanda bai zauna da wadannan mazaje ba sai ya ji magana ce mai girma, sai ya ga kamar an maida shi Allah, ya ce mai aka bar wa Allah ragowa, abun ba haka yake ba, abun mammaki da mai fadar wannan yana da wayewar da yake ganin fina-finai na Turawa, da ya ga wannan magana kai-tsaye a sarari. Misali a kan Kudubi, Turawa suna da wani fim da suke shiryawa na Dirakula (Dracula) wani mai shan jini, abun kamar tatsuniya ce suke shiryawa, amma wani ya ce an yi fada ne da Daular Usmaniyya, wato daular Turkiya, akwai abubuwa da ya ba su tsoro...
Wanna taro yana da matukar muhimmanci, taro ne na murnar Annabi SAW, taro ne da haka Halitta ta saba. Duk al’umma tana farin ciki da murnar haihuwar wani mai girma acikinsu, ko wani wanda ya kawo musu cigaba ta hanyar rayuwa ko cigaba ta hanyar kasarsu ko kowa ma yana murnar ranar haihuwarsa, kamar yadda Annabawa suka yi murnar ranar haihuwarsu. Ubangiji tabaraka wata’ala ya yi murnar ranar haihuwar Annabi Yahya AS (wasalamun alaihi yauma wulida wa yauma yamutu wa yauma yub’asu hayya – Aminci ya tabbata a gare shi (Yahya), ranar da aka haifeshi, da ranar da zai koma ga Ubangiji da ranar da za a tashe shi da rai). Annabi Isa AS kuwa, da kanshi ya yi...
Ƙungiyoyin Musulmi maza da mata da ƙananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira). Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Khalifofin mazhabobin Darikun Tijjaniyya da Ƙadiriyya a Ibadan su ne suka jagoranci manyan malaman addinin Musulunci tare da dimbin mabiya wajen yin tattaki na tsawon kilomita 10 da ya zagaya wasu sassan birnin domin nuna farin ciki da murnar wannan rana. An ga ƙungiyoyin Musulmi daban-daban masu halartar zagayen Maulidi sanye da sutura iri ɗaya (amko) suna rera...
Maulidi: Gwamnan Zamfara Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Buƙaci A Dage Da Addu’o’in Samun Zaman Lafiya
“Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW). “Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW). “Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da mu zuwa ga kyawawan ɗabi’u, halaye da ayyuka. “Ya kamata mu yi amfani da irin waɗannan muhimman lokuta na addini domin mu dage da addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Zamfara, Arewa maso Yamma, da ƙasa baki ɗaya. “Allah (T) ya kawo mana ƙarshen ta’addanci da duk wani nau’in aikata laifuka a cikin al’ummarmu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
Malamai sun yi bayanin cewa a cikin wannan Hadisin akwai hukunce-hukuncen Aikin Hajji sama da guda 100 a ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Na zauna da Manzon Allah (SAW), na zauna da Sayyidina Aliyu, na zauna da Sayyidina Hassan da Hussaini, na zauna da Sayyidina Aliyu Zainul-Abidina (Babanka), don haka tambayi duk abin da kake so.” Shi (Jabir) makaho ne a lokacin, ina cikin tambayarsa kenan (in ji Ja’afarus Sadik) sai lokacin sallah ya yi, sai ya tashi a cikin wani dan mayafi da ya daura kuma ya yafa. Amma saboda kankancinsa duk lokacin da ya jefa shi a kafada sai ya fado alhali kuma ga babban mayafinsa a rataye a kantarsa. Sai ya yi mana sallah. Bayan gamawa na tambaye shi ya ba ni labarin Hajjin da Annabi (SAW) ya yi na karshe. Sai (Jabir) ya yi ishara da hannunsa tare da...
Ma’anar addu’ar ita ce, “Allah ina neman tsari da kai, ya Ubangiji mai girma, da hasken fuskarka (yadda ya dace da shi) mai girma, da sarautarka dauwamammiya, daga shaidani abin jefewa, da sunanka Allah, Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad (SAW) da ‘ya’yan gidansa, ka yi aminci a gare shi. Allah ka gafarta mun zunubina, Allah ka bude mun kofofin rahamarka.” Ba a Harami ba kawai, a kowane Masallaci an so a karanta daga kan salatin Annabin nan zuwa karshen addu’ar idan za a shiga. Idan mutum bai iya wannan addu’ar ba, ya yi a’uziyya da bisimillah da salatin Annabi (SAW) da kuma addu’ar da ya iya. Ana so da zarar mutum ya shiga idanunsa sun kalli Dakin Ka’aba,...
A wurin mu Malikawa, mun dauki watannin nan guda uku a matsayin lokacin Hajji, wasu kuma sun ce a’a, daga kwana goman farkon nan na Zhul-hijja, lokacin ya kare, to amma kuma idan aka yi la’akari za a ga cewa akwai sauran ibadodin Hajjin da suka shige wadannan kwanakin goma irin su Jifa da ake dawowa Mina a yi bayan Sallar Idi da Dawafin bankwana. Shi ya sa Malikawa muka dauki watannin ukun baki daya a matsayin lokacin Hajji. Kuma Ibn Hazan ya goyi bayan haka, don ba za a dauki wata biyu da kwana goma a ce musu watanni uku ba. Kamar yadda bayani ya gabata, Hajji ba a ko ina ake daura haramar yin sa ba, yana...
Shi wannan azumi, na wani lokaci ya fi na wani lokaci kamar an so a dinga yin azumi sau Uku a cikin kowanne wata, lokacin kwanan wata yana 13 da 14 da 15, wannan kwanaki hasken wata ya fi haske a cikinsu, to kamar yadda suke haske haka zuciyarka za ta kara haske sabida saduwa da hasken, sannan kuma hawa-hawa na musulunci guda Uku ne (Islam da Iman da Ihsan) to wanda ya riski wannan kwanaki Uku kamar Ya hau dukka wannan Matakan addinin ne. Akwai azumin Litinin da Alhamis, azumin ranar Litinin Annabi (SAW) ne yake yi, an tambaye shi cewa Ya Rasulullahi sabida me kake azumin ranar Litinin? sai ya ce ranar ce aka haife ni, ina godiya...
Takawa ta kebantattun kebantattu: sun hada duk abin alkairi na gama-garin mutane, sun hada duk abin alkairi na kebantattu sannan sun kara da nutso da zurfafawa cikin sanin Allah, ba su ganin wanin Allah, a ko da yaushe suna Fadar Allah ko suna Fadar Annabi (SAW) ko suna fadar Waliyyan Allah. Wadannan Takawa guda Uku, Allah ya fada mana su cikin Alkur’ani yana cewa : “Ba laifi ga wadanda suka yi imani da Allah suka yi aiki mai kyau cikin abin da suka ci, idan suka yi takawa suka yi Imani, sannan suka yi wata takawa kuma suka yi Imani sannan suka yi wata takawa sannan suka yi kyautaye.” Ayar ta sauka ce lokacin da ayar haramta giya ta sauka,...
In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba. Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya...
Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba. Ita kuma juriya cikin dauke bala’o’i, ita ce tsare rai cikin rashin damuwa lokacin da ake cikin tsananin damuwa, mutum ya nuna kamar abu bai faru ba. Ita kuma yafiya ko rangwame, ita ce barin ramuwa ga wanda ya yi maka ba daidai ba. Dukkan wadannan halaye, suna daga cikin wadanda Ubangiji ya ladabtar da ma’aikinsa (SAW) da su. Ubangiji yana fada masa a cikin hakkinsa...