Majid Majidi Na Iran Ya Sami Kyauyar Girmamawa Daga Cibiyar Fina-finai Na “Eurasia Dake Kasar Rasha
Published: 8th, December 2025 GMT
Fitacce mai shirya fina-finai dan kasar Iran Majid Majidi ya sami kyauta ta musamman a wurin bikin fina-finai na Eurasia, saboda gagarumar rawar da yake takawa a fagen shiryafina-finai da su ka shahada a duniya.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka bude bikin a birnin Moscow wanda ya sami halartar ministan al’adu na kasar Rasha, Olga Lyubimova, mataimakin shugaban kasar Rasha, Vladmir Medinsky sai kuma jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a Rasha Kazem Jalali.
Shugaban Tsangayar FIna-finai ta Eurasia, Nikita Mikhalov ya jinjina wa Majid Majidi saboda fina-finan da ya yi da hakan ya sa aka ba shi kyauta ta musamma da ita ce lambar yabo ta “ Dimond Butterfly”.
A jawabin da ya gabatar, Majid Majidi ya bayyana cewa; Mafi yawancin fina-finan da yake yi, suna da alaka ne da kananan yara da kuma matasa. Haka nan kuma ya ambaci da yin ishara da kananan yaran Gaza wadanda ake zalunta, yana mai fatan ganin zaman lafiya mai dorewa ya mamaye duniya.
Gabanin mika masa lambar yabon, an nuna wasu daga fina-finan da Majidi ya shirya da su ka hada da fim din tarihin manzon Allah ( s.a.w) mai taken; Muhammad; Manzon Allah.
Kimar lambar yabon da aka bai wa Majid Majidi dai ta kai dalar Amurka miliyan daya, da wani dan kasar China mai shirya fina-finai Xh Zheng ya samu,saboda fim dinsa mai taken: “Against the Current”.
Shi dai Majid Majidi an haife shi ne a Tehran a 1959, yana kuma daya daga cikin fitattun masu shirye-finai a Iran.
A shekarar 1997 fim dinsa mai taken; The children of Heaven,’ ya shiga takarar samun kyautar fina-finai ta Amurka.
Wasu fina-finansa da su ka yi suna a duniya sun hada; The Color of Paradise (1999), sai Baran (2001).
Fina-finansa dai sun fi mayar da hankali ne akan matsaloli na kananan yara, talaucii, jajurcewa a gwagwarmaya da hakan ya sa shi yin fice a cikin gida da kuma a duniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa December 7, 2025 Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi) December 7, 2025 Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’ December 7, 2025 Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila December 7, 2025 Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167 December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166 December 7, 2025 Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya December 7, 2025 Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha Tace Ta Kakkabi Jiragen Drones Na Ukrai 116 A Daren Jiya
Majiyar ma’aikatar tsaron kasar Rahsa ta bada sanarwan cewa garkuwan sararin samaniyar kasar ta kakkabo jiragen Drones na yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na kasar Ukrai har guda 116 a daren jiya kadai.
Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon tanakalto majiyar ma’aikatar tsaron na cewa, rasha ta kakkabo jiragen 116 ne a yankuna har 10 a cikin kasar.
Bayanin ya kara da cewa an kakkabo 29 daga cikinsu a yankin Riyazan, 26 a yankin Furunaj, 23 a yankin Biryonsk sai kuma 21 a yankin Bilgurun.
Har’ila yau an kakkabo wasu 6 a Tafrin, 3 a kkursek sai biyu Tambuf. Sannan daya A Tula. Na karshe kuma a Uryol.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yar Iran ta isa wasan karshe na gasar cin kofin duniya na wasan harbi a karo na 4 December 6, 2025 Iran da Rasha sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi 20 da kwangiloli 5 a fannin fasaha December 6, 2025 Putin Na Rasha Ya Ce; Kasarsa Da India Za Su Kara Girman Kasuwancinsu December 6, 2025 Sheikh Kassim Ya Yi Suka Akan Shigar Lebanon Cikin Kwamitin Tattaunawa Da “Isra’ila” Kai Tsaye December 6, 2025 Gwamnatin Iraki Ta Kore Saninta Da Shigar Da Sunayen Hizbullah Da “Ansarullah” A Cikin Na ‘Yan Ta’adda December 6, 2025 Limamin Tehran: Idan Abokan Gaba Su Ka Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa December 6, 2025 Iran Da Pakisatan Sun Amince Da Farfado da Layin Dogo Tsakanin Istambul, Tehran Zuwa Islamabad December 5, 2025 Iran Ta Raya Ranar Haramta Takunkuman Bangare Guda A Duniya December 5, 2025 Trump Ya Yabawa Rwanda Da Kongo DMK Kan Sulhuntawa A Yakin Gabancin Kongo December 5, 2025 Najeriya: Tinubu Ya Nada Wasu Karin Jakadu 65, Sanatoci Da Tsoffin Gwamnoni Na Daga Cikinsu December 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci