Aminiya:
2025-11-08@12:26:03 GMT

Ballon d’Or: ’Yan wasa 5 da ke iya lashe kyautar 2025 

Published: 22nd, September 2025 GMT

Ana ci gaba da takaddama a duniyar kwallon kafa kan wa ya fi cancanta da lashe kyautar Ballon d’Or a matsayin gwarzon dan wasan duniya na  bana.

A ranar Litinin din na za a bayar da Kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 a birnin Paris na kasar Fasansa, ga wanda alakalai suka zaba a matsayin Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa na Duniya.

Ballon d’Or ce kyauta mafi girma ta shekara-shekara ga ’yan wasan kwalllon kafa saboda bajintar da ya nuna ga ƙungiyarsa da ƙasarsa.

Gasar ta bana ta kasance mafi zafi duba da yadda alkaluma ke nuna irin zakakurancin kowanne daga manyan ’yan wasan da ake hasashen za su iya lashe kambin.

An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin tsaro a Kwara Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina

Ga jerin manyan ’yan wasa biyar da aka fi ganin suna da damar lashe ta bana:

Ousmane Dembélé – (PSG, Faransa)

Ousmane Dembélé ne ke kan gaba a jerin masu fafatawa.

Dembele ya ta rawa gani wajen kai PSG ga nasarar lashe kofuna uku – gasar Ligue 1, Coupe de France da kuma kofin Zakarun Turai na farko a tarihin kulob ɗin.

Ya zura kwallaye 21 tare da taimaka wajen cin wasu shida, musamman a muhimman wasanni.

Wannan ne yasa ake kallonsa a matsayin babban ɗan fafatawa.

2. Lamine Yamal – (Barcelona, Sifaniya)

Matashin ɗan shekara 17 zuwa 18 ya yi abin mamaki a wannan kakar.

Yamal ya yi fice a gasar La Liga da kuma Copa del Rey inda ya zura kwallaye 18 tare da taimakawa wajen cin kwallaye da bayar da dama aka ci wasu 21.

Kwarewarsa da kwazo suka sa ake kallon shi tamkar fitacciyar tauraruwa ta gaba.

Sai dai kuma duk da haka, rashin nasara a Gasar Zakaraun Turai na iya rage masa ƙuri’u.

3. Raphinha – (Barcelona, Brazil)

Shi ma Raphinha yana daga cikin manyan ’yan wasan da suka yi fice a bana.

Ya zura kwallaye 34 tare da bayar da damaa ka zura wasu 22 a muhimman wasanni.

Barcelona ta yi nasara a gida, kuma gudummawarsa ta zama abin yabo.

Amma duk da haka, ya na iya fuskantar kalubale wajen daga irin bambanci tsakaninsa da sauran taurarin Barcelona.

4. Vitinha – (PSG, Portugal)

Vitinha na daga cikin ɗan tsaka-tsaki da aka yaba da rawar da ya taka a PSG.

Shi ke tsare tsakiya, yana rarraba kwallo da samar da daidaito tsakanin tsaro da hari.

Duk da cewa ba shi da yawan kwallaye ko taimako irin na ’yan wasan gaba, gudummawarsana da matuƙar muhimmanci.

Sai dai irin wannan rawar kan kananan wurare na iya zama mai ƙarancin tasiri ga masu kada ƙuri’a.

5. Mohamed Salah – (Liverpool, Masar)

Salah ya ci gaba da zama ginshiƙi a Liverpool inda ya taimaka musu su lashe Gasar Firimiyar Ingila da kwallaye da dama da kuma taimakon cin wasu. A matsayinsa na ɗan wasa da ya dade yana taka rawar gani, yana da daraja a idanun masu jefa kuri’a.

Amma rashin kai Liverpool mataki mai nisa a Champions League na iya rage darajarsa a wannan karon.

Abubuwan da ke iya tabbatar da nasara?

Masu shirya gasar sun ce abubuwan da ake la’akari da su wajen zabar Gwarzon Dan Wasan su ne: Hazikancinsa shi kadai, dabi’unsa da iya yanke hukunci da kuma gudummawa ga abokan wasansa dai saurnasu kamar haka:

Lashe manyan kofuna musamman Champions League. Nuna kwazo a manyan wasanni kamar na karshe ko na kusa da karshe. Yawan kwallaye da taimako na da tasiri ga masu jefa kuri’a. Nasarorin kasa-kasa ma na iya ƙara daraja. Salonsa da kuma iya wasa ba tare da keta ba, kamar yadda matashin Yamal ya zo da sabon salo, na iya tasiri. Yiwuwar ba-zata

A halin yanzu, ana kallon Ousmane Dembélé a matsayin babban wanda ke iya lashe wannan babbar kyauta, yayin da Lamine Yamal ke biye masa.

Raphinha, Vitinha da Mohamed Salah kuwa suna nan a sahun gaba suna jiran rarrabuwar ƙuri’u wanda hakan ke iya sa su kai bantensu.

Duk da haka, Ballon d’Or ya saba zuwa abubuwan ban mamaki; duk wani ɗan wasa mai tasiri — mai tsaron raga, mai tsaron gida, ko wani fitacce —na iya mamaye sahun gaba idan ya nuna bajinta a ƙarshen kakar. 

Kazalika kokarin dan wasa na karshe-karshe musamman a Champions League ko wasannin kasashe na iya sauya kuri’un.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kwallaye Raphinha Yamine Yamal

এছাড়াও পড়ুন:

Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce zai ci gaba da yin siyasa matuƙar yana numfashi a doron duniya.

Shekarau ya bayyana cewar siyasa wata babbar hanya ce ta hidima wa jama’a.

Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Don Yaki da Laifuffuka A Maiduguri Abba ya yaba wa sojoji kan hallaka ’yan bindiga 19 a Kano

Yayin da yake hira da ’yan jarida a Kano a yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekaru 70, Shekarau, inda ya ce gina siyasarsa ne bisa tafarkin addini da ɗabi’a.

“Siyasata addinina ce, addinina kuma siyasata ce. Shiga cikin tsarin samar da shugabanni na gari masu gaskiya hidima ce ga jama’a kuma wannan ibada ce a Musulunci,” in ji shi.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa, siyasarsa ba ta da nasaba da son kai, sai dai niyyar ganin an samar da shugabanni masu adalci da kishin al’umma.

“Matukar ina da ƙarfi, zan ci gaba da bayar da gudunmawa. A gare ni siyasa ba aiki ba ne da ake daina yi; nauyi ne na rayuwa gaba ɗaya,” in ji shi.

Shekarau, wanda ya mulki Jihar Kano daga 2003 zuwa 2011, ya yi kira ga jam’iyyun adawa da su haɗa kai domin ƙarfafa dimokuraɗiyya.

Ya kuma yi kira ga shugabanni su mayar da hankali kan matsalolin rashin tsaro, talauci da yunwa.

Ya kuma yaba wa jam’iyyar PDP bisa juriyarta inda ya bayyana cewar har yanzu tana taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya.

Ya kuma yi wa makomar siyasar Najeriya fatan alheri, tare da jadadda cewa zai ci gaba da goyon bayan kowace gwamnati don samar da zaman lafiya da jin daɗin ’yan ƙasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Bukaci Manoma Su Rungumi Tsarin Noma Mai Jure Wa Sauyin Yanayi
  • Yadda PDP Ta Yi Asarar Kudancin Kaduna
  • Jerin Gwarazan Taurarinmu!
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Lebanon
  • Za Mu Ƙara Ƙaimi Wajen Kai Wa ‘Yan Bindiga Hare-Hare Ta Sama – Hafsan Sojin Sama
  • Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
  • Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 
  • Zan ci gaba da siyasa har ƙarshen rayuwata – Shekarau
  • Zulum ya bai wa hukumomin tsaro kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Borno
  • Kocin Super Eagle ya lashi takobin lashe kofin nahiyar Afirka