Aminiya:
2025-12-14@22:57:34 GMT

ECOWAS ta jaddada aniyar kare dimokuraɗiyya da inganta tsaro a yammacin Afirka

Published: 15th, December 2025 GMT

Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta yi alƙawarin kare dimokuraɗiyya da kuma inganta tsaro a yankin Yammacin Afirka.

Wannan alƙawarin na zuwa ne a dai-dai lokacin da yankin ke fuskantar matsalolin tsaro da na juyin mulki.

Yadda aka yi bikin naɗa Rarara sarkin wakar ƙasar Hausa a Daura Jirgin sama ya yi hatsari yayin sauka a Kano

An yanke wannan shawara ne a taron shugabannin ƙasashen ECOWAS karo na 68, wanda aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi.

Shugaba Bola Tinubu, wanda Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya wakilta, ya yi kira ga ƙasashen ECOWAS da su zauna lafiya tare da haɗa kai.

Ya yi gargaɗi ncewa ƙungiyar tana samun rauni idan ƙasashe suka rabu.

Ya ce ƙasashen Yammacin Afirka ba wai waje ɗaya suka haɗa ba, face suna da tarihi, al’adu da gwagwarmaya iri ɗaya da ta haɗa su.

Shugaba Tinubu, ya bayyana cewa duk da cewa rashin jituwa na iya faruwa tsakanin ƙasashe, bai kamata hakan ya karya zumunci da makomar ƙasashen yankin ba.

Ya zayyano matsalolin da yankin ke fuskanta, kamar ta’addanci, rikice-rikice, tsattsauran ra’ayi, juyin mulki, laifukan ƙetare iyaka, yawaitar makamai, barazana a Intanet, sauyin yanayi, ƙarancin abinci da sauransu.

Ya ce waɗannan matsaloli ba su da iyaka, kuma ƙasa ɗaya ba za ta iya magance su ba.

Tinubu ya tarbi shugabannin ECOWAS zuwa Abuja, inda ya yi fatan taron zai ƙara amincewa da juna, ƙarfafa haɗin kai, tare da sake ɗora ECOWAS bisa ginshiƙan adalci da makoma ɗaya.

A yayin taron, ECOWAS ta kuma mayar da hankali kan bunƙasar tattalin arziƙi ta hanyar kamfanoni masu zaman kansu.

Shugaban Hukumar ECOWAS, Dokta Omar Alieu Touray, ya sanar da kafa Majalisar Kasuwanci ta ECOWAS.

An naɗa fitaccen ɗan kasuwan Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, a matsayin shugaban farko na wannan majalisa.

Shugaban ƙasar Saliyo kuma Shugaban ECOWAS, Julius Maada Bio, ya bayyana taron a matsayin mai muhimmanci.

Ya ce yankin Yammacin Afirka na fuskantar manyan ƙalubale na tsaro, dimokuraɗiyya da tattalin arziƙi, kuma shawarwarin da za a yanke za su shafi sama da mutum miliyan 400.

Ya kuma bayyana cewa an yi murnar cikar ECOWAS shekaru 50 da kafuwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ECOWAS Haɗin Kai Tattalin Arziƙi Tsaro Yammacin Afirka

এছাড়াও পড়ুন:

Me Ke Kawo Yawaitar Juyin Mulki A Nahiyar Afirka?

Juyin mulki, wani lamari ne da ya zama abun mamaki a shekarun baya amma a ‘yan shekarun nan, a iya cewa, ba abun mamaki ba ne domin ya zama tamkar ruwan dare musamman a Nahiyar Afirka.  Masoynmu masu bibiyarmu, me zai hana, mu tambayi kanmu, shin me ake nufi da juyin mulki kuma me ke kawo shi? Juyin mulki, shi ne ƙwace gwamnatin ƙasa ba zato ba tsammani kuma ba bisa ƙa’ida ba, wanda yawanci sojoji ko ƙungiya mai ƙarfi ke yi, ta hanyar amfani da ƙarfi ko barazana domin cire zaɓaɓɓun shugabanni. A wannan makon, alƙalaminmu zai karkata ne kan sharhi ga wannan muhimmin abu da ke barazana ga wanzuwar dimokuraɗiyya a yankin Afirka, duk da cewa, akwai dalilai masu ƙarfi da ke janyo a yi juyin mulki a ƙasa. Ga bayani a sarari kuma a taƙaice game da manyan dalilan da ake kyautata zaton su suke haifar da juyin mulkin da ake yi kwanan nan a Afirka, musamman daga ƙarshen shekarun 2020 zuwa 2025. Duk da cewa, kowacce ƙasa da na ta irin sanadin, kamar a ƙasashe irin Mali, Burkina Faso, Guinea, Nijar, Gabon, Chad, da Sudan da suka fada hannun mulkin sojoji a ‘yan shekarun da suka gabata. Babban dalilin juyin mulki, bai gaza rashin Shugabanci na gari da cin hanci da rashawa. Gwamnatoci da yawa a ƙasashen da abin ya shafa suna fama da cin hanci da rashawa, rashin kula da ababen more rayuwar jama’a, rashin samar da wutar lantarki, ayyukan yi, ilimi, da kiwon lafiya na gari. Wannan yana raunana amincewar mutane ga gwamnatocin farar hula kuma yana haifar da gurɓacewar mulkin dimokuraɗiyya wanda hakan ke bai wa sojoji uzurin karɓar mulki cikin sauƙi. Wasu daga cikin dalilan sun haɗa da rashin tsaro da yawaitar tashe-tashen hankula. Ƙasashen Sahel, kamar Mali, Burkina Faso, Nijar – sun fuskanci hare-haren ta’addanci daga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi (IS, Al-Qaeda, JANIM), wanda hakan ya haifar da zargin cewa, jami’an tsaron ƙasa sun gaza. A duk lokacin da gwamnatoci suka gaza kare ‘yan ƙasa, sojoji sukan amfani da wannan dama wajen ƙwace mulki da nufin “dawo da tsaro.” Wasu shugabanni, sukan yi yunƙurin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulki don sauya kujerar dimokuraɗiyya ta zama ta dindindin, kuma su yi riƙa tafka maguɗi a yayin zaɓe, kamar Guinea (2021) da Gabon (2023). Wannan sau da yawa ya kan fusata jama’a sai hakan ya zama wani uzuri ga sojoji wajen hamɓarar da gwamnatin. Har ila yau, wasu jama’a saboda fusata da salon mulkin dimokuraɗiyya a ƙasarsu, suna ganin sojoji a matsayin masu ceto, sun yi imanin cewa, sojoji za su kawo musu kwanciyar hankali. Wannan amincewar ta jama’a, yana sa juyin mulki ya yi nasara cikin sauƙi. Jerin juyin mulki da aka yi cikin nasara a Afirka. 1 – Sojojin Mali a 2020 sun tsige Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta saboda rashin tsaro da zanga-zanga. 2 – Sojojin Chad a 2021 sun karɓi mulki a ƙarƙashin ɗan Shugaba Idriss Déby, bayan mutuwar sa. 3 – Sojojin Guinea a 2021 sun tsige Alpha Condé a 2021 bayan yunƙurin tsawaita mulkinsa. 4 – Sojojin Sudan sun rushe gwamnatin raba iko a 2021 5 – Sojojin Burkina Faso a 2022 sun tsige Shugaba Kaboré saboda gazawar dakatar da rashin tsaro. A juyin mulki na biyu kuma, wata tawagar sojoji ta hambarar da Laftanar Kanar Damiba duk a wannan shekara. 6 – Sojojin Nijar a 2023 sun hamɓarar da gwamnatin Bazoum. 7 – Sojojin Gabon a 2023 sun hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo. 8 – Sojojin Guinea-Bissau a watan Nuwamban 2025, sun hamɓarar da gwamnatin Umar Sissoco Embalò. Akwai jerin juyin mulki da aka yi yunƙurin aiwatarwa amma bai yi nasara ba da dama duk a nahiyar ta Afirka. ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Abubuwan Da Ba Ku Ji Ba Kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi December 13, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Karrama Shugaban NPA Da Lambar Yabo Ta Musamman December 13, 2025 Manyan Labarai Dantsoho Ya Yaba Wa Ƙoƙarin Oyetola Na Dawo Da Nijeriya Tsarin Sufurin Jiragen Ruwa Na Duniya December 13, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tsaro: Abba ya kafa runduna ta musamman da za ta ke tsaron tashoshin mota a Kano
  • An kashe mai ciki da ɗanta a Kano
  • َA Yau Ne Za’a Gudanar Da Taron Koli Na Kungiyar ECOWAS A Birnin Abuja
  • Me Ke Kawo Yawaitar Juyin Mulki A Nahiyar Afirka?
  • Yadda Za Ki Haɗa Sabulun Da Zai Gyara Miki Fata
  • Iran da Rasha sun jaddada aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu
  • Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago
  • Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
  • Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda