An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia
Published: 9th, December 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia, Mohammed Haliru Arabo, na tsawon wata uku, kan rikicin shugabanci.
Shugaban Majalisar, Danladi Jatau, ne ya sanar da hakan a ranar Talata a Lafia, bayan Shugaban Kwamitin Majalisar kan Harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu, Musa Ibrahim Abubakar, ya gabatar da korafi kan rikicin mulki da ke faruwa a karamar hukumar.
Jatau ya ce matakin ya zama dole domin ba da damar gudanar da bincike kan yadda ake tafiyar da mulkin karamar hukumar, wanda ya ce yana shafar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Ya bayyana cewa dakatarwar ta yi daidai da sashe na 7 da na 128 na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima, wanda ya ba majalisa ikon sanya ido kan harkokin mulki.
Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashenta Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a SakkwatoA cewarsa: “Domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Lafia, dole ne mu gudanar da bincike kan abin da ke faruwa. Bisa ikon da kundin tsarin mulki ya ba mu, shugaban karamar hukumar Lafia ya dakata na tsawon wata uku. Za a ci gaba da gudanar da harkokin karamar hukumar har sai an kammala bincike.”
Kwamitin harkokin kananan hukumomi da masarautu ya samu umarni da ya gudanar da binciken cikin wannan lokaci. A yayin dakatarwar, mataimakin shugaban karamar hukumar, Uba Arikya, zai rike ragamar mulki.
Tun da farko, Musa Ibrahim Abubakar ya gabatar da kudiri a matsayin gaggawa, inda ya nuna damuwa kan yadda aka dakatar da shugaban karamar hukumar na tsawon wata shida ba tare da bin ka’ida ba. Ya ce hakan ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma yana haifar da rashin tabbas a siyasar yankin.
Ya jaddada bukatar majalisar jihar ta shiga tsakani domin tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin kudi da mulkin karamar hukumar.
Kwamitin ya kuma bukaci majalisar ta yi nazari sosai kan lamarin domin kawo karshen rashin tabbas da rikicin da ya kunno kai a Lafia.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dakatar Nasarawa karamar hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashenta
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta ayyana dokar ta-baci a yankin, kwana biyu bayan yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar Jamhuriyar Benin.
Shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray, ne ya sanar da haka a yayin zaman majalisar tsaro ta hukumar karo na 55 a Abua.
Touray ya ce daukar matakin ya zama dole domin shawo kan barazanar da juyin mulki ke wa tsarin dimokuradiyya a yankin, wanda ke bukatar matakan zuba jari na gagagwa domin tabbatar da tsaron al’umma.
A yayin jawabinsa ga ministoci da manyan jami’an gwamnati da ke halartar taron, ya bayyana yadda yawaitar samun juyin mulki a Yammacin Afirka ke barazana ga tsaro da zaman lafiya a yankin.
Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato HOTUNA: Yadda dalibai 100 da aka sace a Neja suka dawoYa ce, “Babban barazana ga yankinmu sun haɗa da ci gaba da katsalandan na sojoji (kamar yadda aka gani kwanan nan a Guinea-Bissau da Jamhuriyar Benin); rashin bin ka’idojin sauyin mulki a Guinea inda shugaban soja ke ƙoƙarin zama farar hula; raguwar damar shiga zabe a ƙasashe da dama; ƙara karfin ’yan ta’adda, kungiyoyi masu laifi da ke dauke da makamai; da kuma matsin lamba na siyasar duniya da ke shafar diflomasiyya da haɗin kan ƙasashen mambobi.”
Touray ya jaddada cewa “zabe ya zama babban abin da ke tayar da rikici a cikin al’ummarmu.”
Ya kuma ambaci yunƙurin juyin mulki da aka yi kwanan nan da tattaunawa da ƙasashen AES (Burkina Faso, Mali da Nijar) da suka fice daga ECOWAS, yana mai nanata bukatar gaggawa ta haɗin gwiwar yankin wajen yaki da ta’addanci da laifukan da ke ketare iyaka.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin da bai taɓa faruwa ba, yana gargadi da cewa, “Idan aka dubi wannan hali, ya dace mu bayyana cewa al’ummarmu tana cikin yanayin gaggawa.”
Touray ya bukaci a riƙa yin taron Majalisar Sulhu da Tsaro akai-akai a shekara mai zuwa, yana mai cewa ECOWAS dole ta “haɗa ƙarfi da ƙarfi don fuskantar barazanar ta’addanci da ’yan fashi, waɗanda ba sa mutunta iyakokin ƙasashe.”
Ya kuma bayyana muhimman wuraren da ministoci za su riƙa kula da su, ciki har da rikicin Guinea-Bissau, tafiyar da sauyin mulki, magance ƙara yawaitar cire mutane daga siyasa, da kuma kare haɗin kan yankin daga matsin lamba na waje.