Yadda Rashin Bincike Ke Haifar Da Yawaitar Mutuwar Aure
Published: 13th, December 2025 GMT
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:
Laifi ai na iyayenta ne me ya sa basu yi bincike ba kafin azo wannan gabar. Ya kamata ace ana yin buncike kamar yadda a baya al’adar Malam bahushe ce buncike kafin Aure daga bangaren mijin har na matar. Wani yana gudun kar ya fadi aibin dansa ko ‘yarsa a karshe su rasa masu Aurensu, wanda hakan babbar matsala ce.
Sunana Khadija Auwal Koki, A Jihar Kano:
Eh to, gaskiya laifin mijin ne da kuma danginsa tunda an san maganar aure ba wasa bace ya kamata ace an fadawa juna gaskiya. Ya kamata iyaye su yi bincike da yawa, wajan tabbatar da nagarta da kuma mutuncin dan da za su bawa ‘yarsu, haka shi ma ayi bincike sosai akan yarinyar da zai aura. Da yawan mutane wasu da dama suna zabar su boye gaskiya sun fi san su fito da garya, suna ganin kamar za su fi karbuwa. Bacin ita kuma gaskiya daya ce ramin karya kuma kurarre ne. Idan har ba wani dalili ne mara kyau ba wanda ko da an yi auran za a yi da-na-sani ya sa za a fasa auran ba. To, a ganina a daina soke aure kawai ayi addu’a da fatan alkairi.
Sunana Hafsat Sa’eed
Tun farkon da suka fara soyayya zai aure ta, kamata yayi ayi bincike akai aga shi wane ne, kuma daga ina yake. Wani lokacin matsala daga iyaye ne, basa tsayawa su yi bincike, wani lokacin sukan dauki abin da yarinya ta zo da shi, wani lokacin akan sami akasarin matsala daga mazaje, su zo su yi maka karya su ce ga yadda suke, alhalin ba hakan suke ba. Ko kuma inda za a je a yi binciken su yi karya akan abin da za su fada, sai ka shiga gidan sai ka ga ba haka ba.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, daga Jos a Jihar Filato:
Kamar yadda addinin Musulunci yake koyarwa, bincike yana da matukar muhimmanci, yayin neman aure. Ba kawai binciken tushe ko asalin zuriya da tsatson wanda ake nema da mai nema ba ne, har ma da abin da ya shafi lafiya. Ma’aikin Allah (SAW) a wani hadisi ya tsawatar da sahabbansa daga auren mace daga gidan da bashi da tarbiyya ko tarihi mai kyau, komai kyanta. Don haka za mu fahimci cewa, lallai binciken dangin mata ko miji wajibi ne a addini, kodayake sau da dama soyayya da gaggawa tana rufe mana ido, da hana mu tsayawa mu yi bincike kan wadanda za mu aura. A irin haka ne ake samun zuriya da za su taso da wasu irin bakin al’amura, kamar sata, shaye-shaye, zinace-zinace da ta’addanci, wadanda masana suka ce duk ana gadonsu ne daga iyaye da kakanni. Lallai yana da kyau iyaye da masu shirin aure su natsu su daina gaggawa, su tabbatar sun zabawa ‘ya’yansu abokan zama nagari, da samun zuriya masu albarka.
Sunana Princess Fatima Mazadu, Goben Nigeria:
Cab! Babbar magana, da farko dai Allah ya kyauta ya kuma kawo mana karshen wannan fashe-fashen auren da ake yi a zamanin nan, dan abu ne mai ciwo bayan iyaye sun gama shiryawa ‘ya’yansu, na ta yata jalje da yi mata addu’ar ubangiji ya bata wanda ya fi shi alkairi. Gaskiya mafi akasarin fasa auren zamanin nan gwajin jini, rashin amincewar zuriyoyi guda biyu, rashin yarda da juna wato zuciya na kokonto, da rashin tauhidi na arziki ko wadata. Za ki ga mutum ko gobe ne in wata asara ta hau masa sai an yi canfi ta fannin mace ko namiji. Dukka sunada laifi, Fannin makota da ‘yan’uwa, saboda soyayya ko biyan bukata da gajiyarwa zaman gwaurantaka. Shawara subi a hankali gudun rikicewar al’amari ana tsaka da yi.
Sunana Fatima Nura kila, A Jihar Jigawa:
A ganina laifi ne na bangaren amarya, domin matukar an yi kyakkaywan bincike komai zai bayyana, sabida bincike a aure yana da matukar amfani. Iyaye ya kama su tsananta bincike musamman wajen aikinsa da kuma garinsu da guraren da yake yawan ziyarta. Kwadayi da kuma san duniya matukar mace ko namiji tana da kudi wasu sukan ki bincike, koda wani a dangi yace ayi sai a fara hassada yake ku rabu da shi. Shawara ita ce a kodayaushe muna zurfafa bincike, musamman lamari na aure, domin rayuwa ne ake san ginawa har karshen rayuwa.
Sunana Aisha T. Bello, daga Jihar Kaduna:
Wanan matsalar na faruwa sosai wasu ba sa bincike su san wanda za su bawa auren diyar su, mafi yawanci idan mai kudi ya zo babu wani bincike sai kawai ya bashi. Yanzu kuma duniya ta canza duk in da za ka je bincike babu wanda zai gaya maka gaskiya ko an sani kuwa. Wasu suna jin tsoron yin haka saboda in tayi dadi kada ace sune. Gaskiya haka ta faru a gidanmu da muka tura bincike sai da a ka fada masa an zo bincike. Shawarata dan Allah mutane in an zo bincike kan aure su fadi tsakani su da Allah abun da suka sani kan mutun ban da karya, kada su fadi abu da ba halinsa bane. Su kuma iyayenmu Allah ya basu damar duba wanda yaransu za su aura. Bsnce basa kokari ba, amma su wara sosai, Allah ya shige mana gaba (Amin).
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Abubuwan Da Ba Ku Ji Ba Kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Gwamnonin Bauchi, Neja, Kano, Gombe, da wakilan gwamnan Borno da na Yobe da sauran jihohi duk sun halarci jana’izar.
Daga karshe dai an kwantar da marigayin a cikin masallacinsa sashin Rauda da ke unguwar Makera a cikin garin Bauchi.
Shaikh Dahiru dai an haife sa ne a ranar 28 ga watan June 1927, wanda ya yi daidai da 2nd Al-Muharram 1346 A.H. An samu fadin shekarunsa daban daban wasu su ce shekarunsa 98, wasu su ce 101, wasu kuma su 102. Hakan ya faru ne sakamakon wasu na amfani da ranar haihuwar da aka haifesa na boko yayin da wasu kuma ke lissafi da watan musulunci na hijira.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya sama da 100 yayin da 18 daga cikin Allah ya musu rasuwa kafin mahaifin nasu, mafi wawancin ‘ya’yansa suna Haddace Al-‘Kur’ani tun suna ‘yan kasa da shekaru bakwai. Bayan nan, ya bar mata hudu, jikoki 406, tattaba kunne 100.
Wani abun da duniya ba ta sani ba kan rasuwar Shaikh Dahiru tun a 1950s a Sudan magayin ya kasance na gabatar da tafsiri ta salo na daban ba irin wanda aka sanshi da shi ba. Kazalika daga baya ya dawo ya sauya yanayin tafsirin sa ba tare da mai jaa masa baki ba sai dai fassarar Jalalaini wanda Allaramma Malam Muhammad Bajoga, babban almajiransa ke masa.
An shaidi Marigayin da don zumunci da ziyarar da son ‘yan uwansa, domin kuwa an bayyana cewar irin lungu da kauyuka da ya shiga wajen koyar da Kur’ani ba za su misaltu ba. Ya bayar da gudummawa wajen koyar da miliyoyin mutane Kur’ani kuma ya kafa dubban makarantun koyar da addinin a Nijeriya da wasu sassan Afrika.
LEADERSHIP Hausa ta labaro cewa babban rashin lafiyar da Shaikh Dahiru ya fi fama da ita tsawon shekaru wanda ba kowa ne ya sani ba ita ce ciwon ido. Ya rasu baya gani. Hakan ya samo asali ne tun bayan rashin lafiyar da idon nasa ke yi wanda aka yi ta masa aiki da ba shi maguna a Nijeriya, Dubai, da London daga karshe ya ce a bar masa idon haka ya rasu da ita ba tare da gana gani ba.
Sai dai wani abun burgewa da rayuwarsa har ya rasu yana da cikakken hankalin gano komai da tino komai da zarar aka ce masa abu kaza zai tuna ko a ce amsa ga wane a gabanka zai tuno dukkanin rayuwar da suka yi a baya.
A halin da a ake ciki iyalai da almajiran sun amince da tabbatar da babban dan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wato Khalifa Ibrahim a matsayin magajin Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda zai ci gaba da jagorantar tafiyar kamar yadda ya kamata.
A gefe guda bayan wannan matakin, iyalai da almajiran marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun ayyana cewar daga yanzu dukkani lamaran jagoranci za su ke amsar izinin ne daga wajen Shariff Ibrahim Saleh Al’husainiy wanda ya kasance Khalifan Darikar Tijjaniyya a fadinkƙasar nan.
Sun ayyana cewar a yanzu haka dukkanin biyayyarsu ya koma ga Sharif Saleh. A bisa wannan, yanzu almajiran Sheikh Dahiru sun mika dukkanin biyayyarsu ga Sharif Saleh.
Babban dan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi shi ne ya sanar da wannan matakin da muba’yi’arsu a lokacin da tawagar Sharif Saleh suka kawo ziyarar ta’aziyyar rasuwar Shaikh Dahiru a ranar Lahadi, daga cikin tawagar har da babban limamin babban masallacin kasa, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari.
Babban dan Shehin ya ci gaba da cewa tun kafin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bar musu wasiyya da cewa in ya rasu Sharif Saleh ne zai jagoranci sallarsa kuma ya musu nuni da yi masa biyayya a bangaren lamuran addini.
Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya ce lamarin jagoranci ba lamari ne na wasa ba, don haka sun maida dukkanin biyayyarsu ga Sharif Saleh Ibrahim Saleh Al’husain wanda ya ke fitaccen malamin Darikar Tijjaniyya ne a kasar nan.
Dan Shehin ya sake rokon Sharif Saleh da cewa daga yanzu dukkanin lamuran da za su gudanar a rayuwa su na neman ya ke ba su izni kafin su yi. Ya ce yanzu komai za su koma saurara daga gareshi ne a matsayinsa na Khalifan Tijaniyya a Nijeriya.
Ya tabbatar da cewa yanayin dangatar kusanci da ta abota da ke tsakanin Sheikh Dahiru Usman da Sheikh Sharif Saleh babu mai isa misaltawa, ya ce sun kasance aminai na kut wadanda suke tafiyar da lamuransu a tare-tare a kowani lokaci.
Babban dan Shehin ya tunatar da al’umma kan muhimmancin hadin kai da biyayya wa Khalifanci domin samun tsira duniya da lahira.
Tun da farko da ya ke magana Farfesa Ibrahim Ahmad Makari, ya ce duk duniya ba wanda zai ji zafin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi kamar Khalifa Sharif Saleh saboda kusancin da ke tsakaninsu ta addini da ta abota.
Yadda Duniya Ke Ta’aziyya Da Jajantawa
Wakilinnmu ya labarto cewa yawan wadanda suke zuwa domin mika ta’aziyyarsu bisa wannan babban rashin ba zai misaltu ba saboda jama’a daga sassa daban-daban na duniya na zuwa domin mika ta’aziyyarsu. Kama daga kungiyoyin Darika, Izala, Shi’a, masu kudi, ‘yan kasuwa, sarakuna, malamai, hukumomi, gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisu, daban-daban da dai sauransu. Kadan daga cikin su hada da.
Sarkin Musulmai, Alhaji Sa’ad Abubakar da wakilai na musamman da Shugaban kasa, tare da tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso su ma sun jajanta a ziyarar da suka kai.
Tawagar shugaban kasa wanda ministan kudi Wale Edun, da ministan kasafin kudi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ne suka wakilci shugaban kasa BolaTinubu Tinubu da gwamnatin tarayya a wajen wannan ta’aziyyar da ya gudana a Babban Masallacin Marigayin da ke unguwar Makera a cikin garin Bauchi.
Sannan tsohon ministan wasanni Solonmon Dalung shi ma ya zo ta’aziyyar da wasu fitattun mutane ciki har da sanatoci.
Tawagar su Sultan da sauran masu kawo ta’aziyyar sun nuna matukar kaduwa da rasuwar fitaccen Malamin tare da bayyana irin kyawawan dabi’u da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Kur’ani da addinin musulunci. Sun yi addu’ar Allah ya masa rahama ya gafarta masa sannan sun jajanta wa dukkanin iyalan Mamacin.
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad shi ne wanda ya karbo manyan bakin. Gwamna Bala ya nuna irin dimbin jama’a da suke amsa a wajen ta’aziyyar da yadda yake tabbatar wa duniya irin nagarta da tasirin Sheikh Dahiru Usman a duniya baki daya. Ya ce babban rashi ne wanda suka yi da ba zai misaltu ba.
Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu shi ne ya yi godiya a madadin iyalan Mamacin inda nuna godiya kan yadda suke ganin dinbin jama’a daga sassa daban-daban na kasar nan, ya nuna hakan da irin zaman lafiya da Sheikh Dahiru ya yi da jama’a a lokacin da ya ke raye.
A ranar Talata mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya jagoranci tawagar Majalisar dattawa domin mika ta’aziyya bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, bayan gabatar da uduri na musamman a zauren Majalisar domin karrama Shaikh Dahiru da yaba wa irin gudunmawar da ya bayar a lokacin da ya ke raye.
Kazalika, shi ma Kakakin Majalisar Wakilai na tarayya Hon. Tajudden Abbas ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar wakilai a wajen ta’aziyyar wanda ya gudana a Masallacin marigayin da ke unguwar Makera a cikin garin Bauchi. Mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Auwal Jatau ne ya amshi tawagar.
Da su ke mika ta’aziyyar, Sanata Barau ya bayyana cewar rasuwar Sheikh Dahiru babban rashi ne da Nijeriya da ma Afrika suka yi, ya ce dukkanninsu sun ji matukar zafin rashin babban Malamin wanda ya zama uba, jagora kuma hadimin addinin Musulunci.
Ya ce a zaman majalisar na ranar Talata ta gabatar da wani kudiri na musamman wanda dukkanin sanatoci suka yi alhini da juyayin rasuwar Shaikh Dahiru Usman Bauchi, “Dukkanin Sanatoci ba kawai zallar musulmai ba har da Kiristocin cikinmu kowa ya nuna irin babban rashin da aka yi, da jinjina masa kan hidimar da yayin wa addinin musulunci da bayar da gudummawarsa wajen kyautata zaman lafiya da hadin kai a kasar nan.”
“Mun zo ne a madadin majalisar dattawa a bisa kudirin musamman da aka gabatar, don haka muna jajanta wa gwamnatin jihar Bauchi, iyalai, al’ummar jihar da Musulmai baki daya.”
Ya ce rashin Shaikh Dahiru rashi ne da duniya ta yi, “Ayyukan da Shaikh Dahiru ya yi sun wuce Nijeriya, sun wuce maganar Afrika, yana daga cikin malaman da ake ji da su a duniya baki daya.”
Barau ya yi addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa. Sannan ya nemi iyalansa da su ya kokarin koyi da kyawawan dabi’u na mahaifinsu.
Tawagar majalisar dattijai ta hada da Sanata Sani Musa, shugaban kwamitin kudi; Sanata Muttati Dan Dutse, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da manyan makarantu; Sanata Shehu Buba Umar, Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kiwo; Sanata Abdul’aziz Yar’adua, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sojoji; da hamshakin dan kasuwar mai Jack Rich, shi ma ya shiga tawagar majalisar dattawa.
Daya daga cikin ‘ya’yan magayin, Dr. Bashir Dahiru Bauchi, ya gode wa tawagar Majalisar Dattawan bisa ziyarar da jajantawa.
A bangaren kakakin majalisar wakilai kuwa, Hon. Tajudden Abbas ya ce sun zo ne domin su wakilci dukkanin ‘yan majalisun tarayya su 360 domin mika ta’aziyyarsu bisa wannan babban rashin da Nijeriya ta yi.
“Wannan rashin ba rashi ne na mutanen Bauchi ba, ba rashi ne na Nijeriya ba, kima da daukaka na Malam Dahiru ya zama na duniya ba ma Afrika ko Nijeriya ba; duk wani malami mai amsa sunan malamanta ya san daukaka da irin rayuwa da babbanmu, kakanmu Malam Dahiru ya yi a tsawon rayuwarsa na hidima wa addini a wannan kasar.”
Ya ce yawan dalibai da Shaikh din ya koyar sun ce a ce Nijeriya ne kadai don haka ya ce rashin ke na duniya. Sun mika ta’aziyyarsu wa gwamnatin Bauchi, Sarkin Bauchi, iyalai da ma jama’a Bauchi.
Daga cikin tawagar Majalisar wakilai akwai shugaban mai tsawatarwa na majalisar, Hon. Usman Bello Kumo; shugaban kwamitin kasafi, Hon. Abubakar Kabir Bichi; shugaban kwamitin harkokin mai, Hon. Alhassan Ado Doguwa; mataimakin shugaban marasa rinjaye, Aliyu Sani Madaki; shugaban kwamitin kula da harkokin tashoshin ruwa, Hon. Nnolim Nnaji da dai sauransu.
Sai kuma ‘yan majalisar tarayya daga Bauchi kamar su Bappa Aliyu Misau, Ali Garu da dai sauransu. Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin Alhaji Surumbai Sheikh Dahiru Bauchi ne ya yi jawabin godiya a madadin iyalai, inda ya ce wa ‘yan majalisun dokokin wannan rashin gaba daya ne aka yi, don haka ya ce sun gode da ziyarar.
Su ma dai shugaban jam’iyyar PDP na kasa, bangaren Barista Kabiru Tanimu Turaki, SAN, ya jagoranci tawagar jam’iyyar don kai ziyarar ta’aziyya kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Shaikh Dahiru Usman Bauchi.
Barista Turaki, ya roki Allah Madaukakin Sarki Ya jikan Shaikh Dahiru Bauchi da rahama, Ya gafarta masa, Ya kuma sanya shi cikin Aljannatul Firdausi.
A gefe guda, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentaweh Yilwatda, shi ma ya jagoranci manyan jagororin jam’iyyar wajen mika ta’aziyyarsu kan wannan babban rashi. Ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban rashi ba kawai ga Jihar Bauchi ba, har ma ga Najeriya da duniya baki daya.
Tsofaffin manyan jami’an gwamnati, ciki har da Tsohon Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Kasa, Janar Aliyu Gusau (Rtd.); Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido; Sanata Abdul Ahmad Ningi; tare da sauran sanatoci, ‘yan majalisar wakilai, da malamai daga cikin gida da kasashen waje, su ma sun kai ziyarar ta’aziyya.
Wani Wasiyya Ya Bari Kan Masa Maulidi?
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewar bayan ya rasu bai amince ba kuma bai yarda a ware rana ta musamman a ranar 2 ga watan Al-Muharram domin ake yin Mauludin tunawa da ranar haihuwarsa ba.
Marigayin ya bayyana haka ne daga cikin wasiyyar da bayar, cikin tawali’u da kankan da kai ya ce shi bai kai wanda za a ke gudanar da Maulidin tunawa da shi ba kamar yadda ake yi wa Manzon Rahama, irin su Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim Inyass.
Marigayi ya bayyana cewar shi kawai Mukaddami ne daga cikin Mukaddaman Shehu, kuma hadiminsa sannan surukinsa inda ya bayyana cewa hakan ma kawai ya ishe sa alfahari.
Shehu Dahiru Bauchi ya nuna cewa idan har an ce kowani Mukaddamin Shehu za a ke masa Maulidin tunawa da shi to kowani rana ma zai zama na gudanar da maulidodi ne domin yawan Mukaddaman da ake da su.
Ya bayyana da bakinsa cewa: “Amma ni ban yarda a ce wata rana za a yi taro yau 2 ga watan Muharram ranar da aka haifi Shehu Dahiru muke yin Maulidi ban yarda ba, kada a yi min bayan rayuwana.
“Amma na ji wani yana cewa Rabi’ul Auwal ya kunso mana (ya zo mana) da Annabi Muhammadu (SAW), Safar ya kunso mana Shehu Tijjani (R), Rajab ya kunso mana Shehu Ibrahim (R) ya ce wai Muharram ya kunso musu Shehu Dahiru to wannan kada a sake fada, kada na sake ji.
“Ni ba kowa ba ne cikin wannan tsarin ni Mukaddami ne. Ni Mukaddami ne daga cikin mukaddaman Shehu. Yanzu kowani Mukaddamin Shehu sai an masa Maulidi ranar haihuwarsa nawa kenan? akwai ranar da za ta wuce ba a samu Maulidi ba?
“In an ce kowani Mukaddamin Shehu za a masa Maulidi akwai ranar da ba Maulidi ke nan a Nijeriya? To ban yarda kada a sa sunana a cikin wadanda ake ma wannan abu,” in ji shi.
Ya sake fayyace wasiyyar tasa da cewa, “Kuma ko na mutu kada a ce yau ranar biyu ga watan Muharram za a yi Maulidin Shehu Dahiru ban yarda ba, ban yarda ba; A bar ni kamar sauran ‘yan uwana Mukaddamai.”
Ya sake nanata cewa shi “Ni ba kowa ba ne illa mukaddami cikin Mukaddamin Shehu kuma wannan ya isheni alfahari, hadiminsa kuma surukinsa, Alhamdillahi.”
A gefe guda ya ce Maulidin tunawa da Shehu Ibrahim da ake yi a watan Rajab shi ne ya fara gudanar.
Ga Jerin Sunayen Nagartattun ‘Ya’yan Magariyin
1. Marigayi Sayyadi Muhammadu Bello, 2. Sayyadi Dr. Muhammad Hadi, 3. Sayyadi Shehu Ibrahim “Yaya-Shehu” 4. Sayyadi Shehu Tijjani “Yaya-Malam” 5. Sayyada Aisha. 6. Sayyadi Dr. Surumbai (Abubakar) 7. Sayyidi Ali 8. Sayyada Fatima 9. Sayyadi Usman 10. Sayyadi Mustafa 11. Sayyadi Dr. Bashir 12. Sayyadi Mushiri 13. Sayyada Zainab 14. Sayyada Maryam 15. Sayyadi Ahmad 16. Sayyadi Dr. Fatihi 17. Sayyada Bilkisu 18. Sayyada Ummul Kulthum (Ummula) 19. Sayyada Khadija 20. Sayyadi Mustafa 21. Sayyada Amina 22. Sayyada Ru’kayya 23. Sayyadi Nasiru 24. Sayyada Hafsatu 25. Sayyada Maimuna 26. Sayyada Safiyya 27. Sayyadi Abdullahi 28. Sayyada Saudatu 29. Sayyada Hindu 30. Sayyadi Aminu 31. Sayyada Juwairiyya 32. Sayyadi Habibu 33. Sayyada Ramlatu 34. Sayyada Asma’u 35. Sayyadi Umaru 36. Sayyadi Naziru 37. Sayyada Ru’kayya 38. Sayyada Madina 39. Sayyadi Hassan 40. Sayyadi Mubasshiru 41. Sayyada Lubabatu 42. Sayyada Mariya; Matar Aminina, Sidi Abubakar A. Mohammed 43. Sayyadi Mansur 44. Sayyadi Musa 45. Sayyadi Nuru 46. Sayyadi Makki 47. Sayyadi Munzir 48. Sayyadi Daha 49. Sayyadi Surajo 50. Sayyada Ummu-Hani 51. Sayyada Hassana 52. Sayyada Hussaina 53. Sayyada Muhsinah (Gambo) 54. Sayyada Ummul-Khairi 55. Sayyadi Murtada 56. Sayyada Nafisa 57. Sayyada Raiha 58. Sayyada Baraka 59. Sayyada Aisha 60. Sayyada Khadija 61. Sayyadi Madani 62. Sayyadi Hashimi 63. Sayyadi Adamu 64. Sayyadi Nuru 65. Sayyada Ummu-Sulaim 66. Sayyada Sadiya 67. Sayyadi Mahmud
68. Sayyadi Munta’ka 69. Sayyadi Jamalu 70. Sayyada Rahma 71. Sayyadi Mukhtar 72. Sayyadi Hafiz 73. Sayyadi Mahi 74. Sayyada Ummul-Khairi 75. Sayyada Hassana 76. Sayyada Umamatu 77. Sayyada Maryam 78. Sayyada Fatima 79. Sayyadi A’kibu 80. Sayyada Khadija 81. Sayyada Aisha 82. Sayyadi Muhammad Hadi 83. Sayyadi Ahmad 84. Sayyadi Abdul-Malik 85. Sayyada Dayyiba 86. Sayyadi Dahiru (Khalipha) 87. Sayyadi Dayyib 88. Sayyada Hussaina 89. Sayyada Bilkisu 90. Sayyada Baraka 91. Sayyadi Muniru 92. Sayyada Fatima-3 (Az-Zahra) 93. Sayyada Asma’u 94. Sayyada Ais
ha 95. Sayyada Aisha.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA