2025-07-03@03:29:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 341

«makarantun Tsangaya»:

    Iran ta nuna makamai masu linzami wadanda suka bude kofofin jahannama kan ‘yan sahayoniyya A martanin da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka kai wa Iran, sojojin Iran da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar sun nuna karfinsu na soji a matsayin wani bangare na “Alkawarin Gaskiya na 3”, inda suka harba daruruwan makamai masu linzami na ballistic da hypersonic. A wani bangare na wannan harin na ramuwar gayya, Iran ta kai jerin hare-hare na hadin gwiwa, wanda kaso mafi tsoka na makamai masu linzami kamar Emad, Ghadr, Fattah 1, Sejjil da Khaybar. A halin yanzu rahotonni da hotuna daga haramtacciyar kasar Isra’ila suna kara fitowa kan yadda makamai masu linzamin Iran suka tarwatsa wurare masu muhimmanci na gwamnatin haramtacciyar...
    Lokaci bai kura wa sauran kasashe na koyi da Sin ba. Sun gwada aron tsare-tsaren kasashen yamma, kuma babu inda hakan ya kai su. Don haka za su iya tsara irin dabarun da ya dace da yanayinsu domin kyautata makomar kasashensu da al’ummominsu. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun tsaro na rundunar “Operation Hadin kai” sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 yayin wata arangama a yankin Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin. Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina Manjo Janar Markus Kangye ya ce aikin kawar da ‘yan ta’addan da aka aiwatar ranar Litinin ya faru ne bayan rundunar ta lashi takobin kawar da sauran ‘yan Boko Haram/ISWAP da ke ɓuya a yankin Tafkin Chadi. “Arangamar ta faru ne a lokacin wani aiki na haɗaka wanda aka...
    Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba. Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba. An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun...
    Masu bincike sun gano cewa sojojin HKI sun kashe Falasdinawa akalla 100,000 tun bayan fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara 2023. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kan cewa farfesa Michael Spagat da kuma Khalil Shikaki  Bafalasdine masanin masanin fasahar siyasa a Jami’ar London na kasar Burtania suka jagoranci bincike wanda ya kai ga fitar da wannan sakamakon. Labarin ya kara da cewa masu binciken sun kiyasta mutane a gidaje 2000 a birnin  Gaza kadai wanda falasdinawa kimani 10,000 suke rayuwa, sannan suka yi lissafi suka kaim ga wannan sakamakon. Bincike ya kara da cewa daga watan jenerun shekara ta 2025 falasdinawa 75,200 sojojin yahudawan suka kashe da makamai, sannan wasu kimani...
    Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”.   Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji.   Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar Litinin da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka fara da ɗan fashin dajin tamkar buɗe sabuwar ƙofar ci gaba da yaƙarsa ne.   “Alhamdulillahi an tarar da shi har gida nai inda ba a taɓa zuwa ba, kuma ya ga cewa ana iyawa, kuma an isko shi,” inji Ahmad Manga.   Ya ƙara da cewa “an kuma buga wuta, an yi nasarori da dama inda aka...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Monaco ta ƙulla yarjejeniyar kaka biyu da tsohon ɗan wasan Manchester United da kuma Juventus, Paul Pogba. Pogba mai shekara 32 ya koma a matakin wanda bai da kwantiragi tun daga watan Nuwamba, bayan da Juventus ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninsu. Nijeriya ce kasa ta 12 mafi talauci a duniya — IMF Yadda na hannun daman ’Yar’Adua ya yi tuggun hana ni zama shugaban ƙasa — Jonathan  A watan Maris ɗin bara ne aka dakatar da Pogba shekara huɗu, sakamakon zargin shan abubuwan ƙara kuzarin jiki. Amma yanzu zai koma taka leda bayan da aka rage hukuncin zuwa wata, sakamakon ɗaukaka kara a watan Oktoba. Ya fara taka leda a Manchester United daga nan ya...
    Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin. Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18. Dukkansu sun fito ne daga kauye daya, Kafr El-Sanabseh, a gundumar Menoufia, kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara 21 ne. Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna...
    Masana da jami’ai a Nijeriya, sun yaba wa ci gaba na a-zo-a-gani da karin kuzarin da ake samu a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya, suna masu bayyana kokarin da aka yi zuwa yanzu a hadin gwiwar bangarorin biyu a tafarkin zamanantar da kansu. Masanan sun bayyana haka ne yayin taro na biyu na bayan taron FOCAC da aka yi ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar. Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika dake Nijeriya ce ta shirya taron mai taken “Hada Hannu Wajen Zamanantar da Sin da Afrika da cimma shirye-shirye 10 na Hadin Gwiwa a Cikin Al’ummar Sin da Afrika mai Makoma ta Bai Daya a Ko da Yaushe.” Da yake jawabi, daraktan cibiyar nazarin Sheriff Ghali...
    An ji karar jiniyoyin gargadi a wurare da dama a HKI suna tashi bayan sun hango malamai masu linzami wadanda sojojin Yemen suka cilla daga kasar zuwa haramtacciyar kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kafafen yana labaran yahudawan na cewa sun yi shirin kakkabo makaman kafin su isa. Amma basu bada rahoton yawan barnan da makamai suka yi ba bayan shigowarsu haramtacciyar kasar. Yahudawan sun bayyana cewa an ji karar jiniyar gargadi a yankunan Beersheba, Dimona da kuma garuruwan da suke kewaye da su a safiyar yau Asabar.  Majiyar sojojin kasar Yemen sun bayyana cewa sun cilla makaman kan haramtacciyar kasar Isra’ila ne saboda ci gaba da kissan kiyashin da take a zirin gaza.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Doctor Zainab Muhammad na daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da kudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da kalubalen da wasu matan dake yankin Arewa suke bayyanawa suna fuskanta wurin karantar fannin. Doctor Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci daya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba har da mazan ma na kauracewa wannan karatun. Zainab Kwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?...
    Yawan gawarwakin da aka tsinta bayan harin duk na mabiyansa ne. Ɗaya daga cikin su, Bashari Maniya, wanda tsohon ɗan bindiga ne da ya ce ya tuba kuma ya fara taimaka wa jami’an tsaro, shi ma ya mutu bayan motar da yake ciki ta faɗa rami mai zurfi. Manga ya bayyana cewa ba da bindiga aka kashe Maniya ba, saɓanin jita-jitar da ke yawo. “Sabuwar mota ce, kuma ba su san dajin sosai ba. Yayin da suke gudu a cikin daji, sai suka faɗa cikin wani rami mai zurfi. Motar ta kife, kuma an kasa ciro ta cikin sauƙi,” in ji shi. Ya ce lokacin da aka zo taimaka musu, an same su a cikin motar a sume. Motar ba...
    Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Isra’ila da Iran, bayan zargin ƙasashen biyu da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla. Lamarin na zuwa ne bayan ɓullar rahoton kai wa juna hari daga dukkan ƙasashen biyu, duk da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ’yan sa’o’in da suka gabata. Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharram An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a Nijeriya Trump ya ce ƙasashen sun daɗe suna faɗa da juna, kuma a wannan mataki ana iya cewa ba su ma san abin da suke yi ba. Ya ce: “Ba abin da muke so ke nan ba, ina tabbatar muku cewa ina fushi da abin da suka aikata.” Shugaba Trump ne mutum na...
    Fadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai zabi wanda zai yi masa takarar mataimaki a zaben 2027 a hukumance ne kawai bayan a kammala babban taron jam’iyyar APC a 2026. Kakakin shugaban, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawarsa da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis. Da yake martani kan dalilin da ya sa fadar shugaban ta yi shiru kan zargin cewa Tinubu na son canza mataimaki a 2027 musamman la’akari da yadda ’yan jam’iyyar ke ta nuna goyon bayansu ga shugaban shi kadai, Onanuga ya ce hakan ba gaskiya ba ne. Nan da mako biyu za mu yanke shawara kan shigar wa Isra’ila yaƙi — Trump Muna shawartar Trump kada ya shiga yaƙin Iran da...
    A ci gaba da ƙoƙarinta na tabbatar da kyawawan halaye da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta lalata katan 243 na barasa da galan 100 na barasa da aka haɗa a gida, da aka fi sani da sukudaye. A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Hukumar, Adamu Muhammad ya sanya wa hannu, ta ce an lalata barasa a Damaturu, a wani mataki na aiwatar da dokar hana sha da kayan rarraba barasa a jihar. Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi Tinubu na ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna Shugaban Hukumar Hisbah na jihar, Dokta Yahuza Hamza Abubakar ne ya bayyana cewa aikin ya...
    Kafin wannan, yana riƙe da sarautar Walin Gaya, wanda aka ba shi lokacin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ƙirƙiri sabbin masarautu. Masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da ƙimar sarautun gargajiya bisa tsarin da aka gada. Sai dai matakin ya zo ne mako guda bayan Alhaji Usman ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, kan zarginta da karɓar bashi na dala miliyan 6.6. Gwamnatin Kano ta musanta zarge-zargen, tana mai cewa ba gaskiya ba ne face tsantsar siyasa. Ko da yake masarautar ba ta danganta ƙwace sarautar da wannan suka da Alhaji Usman ya yi ba, lokacin da aka ɗauki matakin ya haifar da zargi da cece-kuce a tsakanin jama’a. Daga kanmu, magana...
    Ta hanyar inganta manufar yafe harajin kwastam a kai a kai, kasar Sin ta samar da yanayin kasuwanci mai karko a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana kallon manufofinta na rangwame a matsayin matakan tabbatar da burin samun ci gaba, inda take kokarin kyautata tsarin cinikayyar waje na kasashen Afirka, da kuma ba da goyon baya wajen raya masana’antu, da habaka tsare-tsaren tattalin arziki a Afirka. Dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tabbatar da ci gabanta da kasashen Afirka na bai daya, shi ne domin ra’ayinta game da dangantakar dake tsakaninta da Afirka, wato al’ummar Sin da Afirka suna da makomar bai daya a nan gaba. A ganin kasar Sin, ita da Afirka suna da tarihi...
    Borussia Dortmund ta soma buɗe wasanninta na gasar FIFA Club World Cup da canjaras a karon-battar da ta yi da kungiyar Fluminense ta Brazil a ranar Talata. Ana dai ganin babbar kungiyar da ta zama gagarabadau a Rio de Janeiro Fluminense a matsayin mafi hatsari a rukunin F wanda ya kunshi har da kungiyar Ulsan HD ta Koriya ta Kudu. Buni ya bai wa manoma 1,000 tallafin aikin gona Amurka na iya kashe jagoran addini na Iran don mun san inda yake — Trump An dai rika kai wa juna hari a yayin wasan da suka barje gumi a filin wasa na Metlife da ke East Rutherford a wajen birnin New York, sai dai mai tsaron ragar Dortmund, Gregor Kobel...
    Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su bayan sun kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasa Indonesiya. A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin ƙasar Indonesiya, bayan da ya ɗauko alhazan da daga birnin Jidda na ƙasar Saudiyya. ’Yan sanda ƙasar Indonesiya sun ce an yi nasarar fitar da ɗauƙacin fasinjojin jirgin su 442 a filin jirgi da ke lardin Sumatra ta Arewa. Ma’aikatar Sufuri ta ƙasar Indonesiya ta ce jirgin ya yi saukar gaggawa ne bayan samun wani saƙon imel cewa an sanya bom a jirgi. Sarki ya...
    “Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma gode wa Tinubu bisa yadda ya bai wa ‘yan Arewa maso Gabas muƙamai masu gwaɓi kafin na nemi a mara masa baya,” in ji Salihu. A lokacin taron, wasu matasa sun kusan kai masa hari, amma ya ce hakan ya faru ne saboda wasu ba su fahimci abin da ya yi ba. Ya kuma jaddada cewa a tsarin jam’iyya, mutum ɗaya ne kawai ake zaɓa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a lokacin zaɓen fidda gwani, kuma shi ne ke da ‘yancin zaɓar mataimakinsa. “Ba a daidaita tikitin shugaba da mataimaki a zaɓen fidda gwani. Ɗan takara kawai ake zaɓa, kuma yana da ‘yancin zaɓar wanda zai mara...
    Sarkin yankin Oke Agbe a Jihar Ondo ya ci Musulmi tara, tare da barazanar koran su da kuma haramta yin addinin Musulunci a garinsa bayan da wasu dodanni suka kai hari a wani masallaci da gidan limami. Aminiya ta samu rahoto cewa, wasu dodanni sun kai hari a masallaci da gidan wani limami, suka lakaɗa wa matansa da ’ya’yansa duka a yankin Oke Agbe, da ke shiyyar Akoko a Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa a Jihar Ondo Jihar Ondo. Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC), ta bayyana cewa, “Basaraken yankin ya yi Musulmin tara da aka ci zalinsu tara, saboda sun yi ihu tare da zagin dodannin, maimakon su riƙa yin kuka suna roƙon dodannin. “Basaraken ya umarci matan limamin su...
    Jam’iyyar APC a Yankin Sanatan Kaduna ta Arewa (Zone 1) ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, don sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu. An yanke wannan shawara ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jami’ar Tarayya ta Ilimi da ke Zaria, inda tsoffin gwamnoni, ministoci, ‘yan majalisa, da kwamishinoni da shugabannin hukumomi na tarayya da jiha suka halarta. EFCC Ta Kama Mutane 11 Kan Zargi Aikata Damfara A Intanet A Kaduna An Karrama Dalibar Kaduna Da Ta Zo Ta Biyu A Gasar Karatun Alkur’ani Ta Duniya Masu ruwa da tsakin sun jero nasarorin da gwamnati mai ci ƙarƙashin APC...
    Wasu Hare-haren da gwamnatin Isra’ila ta kai ya haddasa gobara a wasu matatun mai a lardin Bushehr da ke kudancin kasar Iran. Gobarar ta tashi ne a wurin a ranar Asabar bayan da wasu kananan jiragen yakin Isra’ila guda biyu suka kai hare-hare a kan kayayyakin sarrafa iskar gas da ke yankin kudancin Pars. Hare-haren sun yi haddassa fashe fashe a matatar iskar gas ta Fajr-e Jam, daya daga cikin mafi girma a Iran, da kuma wata karamar matatar mai a mataki na 14 na tashar iskar gas ta Kudu Pars. Har yanzu ba a fitar da kiyasin barnar a hukumance ba. Bayan gobarar, ma’aikatar mai ta Iran ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da harin. Sanarwar ta...
    Farashin Man Fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin da Isra’ila ta kai wa Iran, lamarin da ya tayar da hankalin masu zuba jari. Ana fargabar cewa rikicin da ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin ƙasashen biyu zai iya kawo tangarɗa wajen samar da man fetur daga yankin Gabas ta Tsakiya. An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8 Wani muhimmin wurin da ake safarar man fetur na duniya, wato mashigar Hormuz da ke kusa da Iran na da matuƙar tasiri, domin kashi ɗaya cikin biyar na dukkanin man da ake fitarwa daga nan ne ake bi da shi. Amma duk da haka, kasuwannin hannun jari sun fuskanci faɗuwar...
    Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa. Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai...
    Kwanaki takwas bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin Mokwa, hedikwatar Ƙaramar hukumar Mokwa a Jihar Neja, an gano gawar mutum ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, an tsinci gawar ne a ranar Alhamis a wata gona da ke kan hanyar wucewa kusa da wani wuri da aka fi sani da ‘dam’. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi A cewar shaidun gani da ido, an kasa tantance wanda abin ya shafa saboda gawar ta lalace. An binne shi ne a inda aka gano gawarsa. Wata mazauniyar yankin mai suna Tswata Mai...
    Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan. Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar da shinkafa zuwa tan 58,000, lamarin da ya bai wa gwamnatin tarayya sanya tallafi a bangaren rabar da shinkafa ga jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa. Ministan ya ce akwai bukatar kare masu amfani da kuma kayan da ake nomawa, “kaso 80 cikin 100 na abincinmu manoman cikin gida ne suka samar da su.” A daidai gabar da ake hasashen adadin ‘yan Nijeriya zai kai...
    Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana da yaki, sannan ya tabbatar da cewa a shirye suke su fuskanci duk abinda zai faru. Manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi ga taron dakarun sa-kai na “Basiji a nan Tehran ya kuma kara da cewa;  Babu wani wuri komai zurfi da nisansa a HKI da ba mu tsinkayowa, idan kuwa aka ba mu umarni to za su yi nasara, mu Sanya abokin gaba ya yi nadama. A gefe daya ministan tsaron Iran ya bayyana cewa; Duk wani hari da ake tunanin kawo wa Iran, to kuwa zai fuskanci mayar da martani mai...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar leken asiri ta kasar Iran ta fidda farkon bayanan sirra wanda ta samo daga HKI wadanda kuma suke tabbatar da dangantakar da hukumar IAEA take da shi da HKI da kuma sauran kasashen yamma da hukumomin tsaronsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran tace a cikin bayanan da ma’aikatar ta wallafa ya zuwa yanzu ya nuna irin yadda hukumar IAEA take mika bayanan da ta samu daga cibiyoyin Nukliya na kasar Iran ga HKI. Wanda ya kaiga kissan masana da kwararrun a fasahar makamacin Nukliya a baya. Bayanan sun bayyana yadda hukumar ta IAEA take mikawa dukkan takardun sirri na shirin makamashin nukliya na kasar Iran ga makiyanta don su yi aiki a kai. Banda HKI wadannan bayanan...
    Gwamnan Kebbi, Dakta Nasir Idris (Ƙauran Gwandu) ya jajanta wa al’ummar kasuwar katako ta bayan kara da ke Birnin Kebbi bisa ibtila’in gobara da ta auka musu. Mataimakin Gwamnan, Sanata Umar Abubakar Tafida ne ya wakilci gwamnan a yayin ziyarar jaje da ya kai wa ’yan kasuwar da abin ya shafa. A saurari sauyin da za mu yi wa ɓangaren man fetur a Nijeriya — Dangote NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya A lokacin da ya zagaya domin duba irin ɓarnar da wutar ta yi a kasuwar, Mataimakin Gwamna ya yi kira da su mayar da lamarin ga Allah da kuma ɗaukar wannan ibtila’in a matsayin jarabawa daga gare Shi. Haka kuma, ya miƙa wa ’yan kasuwar gudumawar...
    Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta bayyana cewa jerin wuraren da zata kaiwa hare hare a HKI a duk wani yakin da zata taso tsakanin kasshen biyu, suna hannu. Daga ciki har da ciboyoyin Nukliyar kasar wadanda ta boye su. Tashar talabjin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto majalisar ta na fadar haka a jiya Litinin, ta kuma kara da cewa ta kara samun bayanai masu muhimmanci a wannan fagen, bayan bayanan leken asirin da ta samu a cikin yan kwanakin da sukka gabata. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu sojojin JMI suna cikin shiri fiye da na ko wani lokaci, don maida martani ga makiya. Tace a halin yanzu jerin wuraren da sojojin Iran zasu...
    Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin 9 ga wata sun nuna cewa, a watan Mayun bana, ma’aunin farashin kayayyakin masarufi, watau CPI na kasar, ya ragu da kaso 0.1 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma farashin makamashi ya zama babban dalilin da ya haifar da raguwar. Kana, ma’aunin farashin sarrafa kaya na cikin gida, watau PPI shi ma ya ragu da kaso 3.3 bisa dari, bisa na makamancin lokacin bara, kuma adadin ya ragu da kaso 0.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na watan Afrilun bana. Duk da cewa ma’aunin CPI na watan Mayu ya ragu kadan, amma farashin kayayyaki a wasu bangarori ya canza, al’amarin da ya shaida rawar da...
    Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
    Minitan kiwon lafiya na kasar Iran ya bukaci kamfanonin da suke kera kayalin kiwon lafiya da kuma aikin likita so kara yawan kayakin da ake sayarwa zuwa kasashen waje. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Mohammad Reza Zafarkhan yana wannan kiran a jawabin da ya gabatar a taron bude kasuwar baje koli na kayalin aikin likita da kuma kiwon lafiya a nan Tehran. Ministan ya kara da ce wa duk tare da mummunan takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka ta dorawa kasar wannan bai hana ta ci gaba a fannonin ilmi masu yaw aba. Wanda ya kaita kasa da wasu manya-manyan kasashen duniya a wasu fagagen. Ministan ya bukaci kamfanonin kera kayakin likita da kiwon...
    Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya nanata matsayin Taiwan da jaddada manufar Sin daya tak a duniya yayin tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot a jiya Jumma’a. Ya kuma bayyana adawar Sin da shigar kungiyar tsaro ta NATO cikin harkokin yankin Asiya da Pasifik. Wang Yi wanda mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya nanata cewa, batun da ya shafi Taiwan, batu ne na cikin gidan Sin da ya shafi ’yancin kasar da iko kan yankunanta, wanda ya bambanta da batun kasar Ukraine. Ya ce Sin na daukar amincewa da manufar kasar daya tak da Faransa ta yi da muhimmanci, kuma tana fatan ganin hakan a aikace. Bugu da kari, ministan ya...
    Yanzu mun yi hakan a kananan Hukumomi takwas,zuwa Lahadi mai zuwa,zamu je ta tare. Zamu ci gaba da yin hakan har zuwa watan Nuwamba wanda hakan zai sa mu kammala da kananan Hukumomi 27. Zuwa yanzu ana ganin amfanin abinda aka yi,a duk kananan Hukumomi da muka ziyarta. Ina ganin mun yi rawar gani kan muradai 12,amma kamar yadda na ce al’ummar Jigawa sune wadanda ya dace su yi bayani kan irin ayyukan alkhairi da ci gaban da muka yi a matsayinmu na gwamnati.   Da aka yi ma shi maganar ya ware kashi 30 cikin 100 saboda bangaren ilimi,cewa ya yi ai Jigawa Jiha ce da take da manoma. Domin kuwa kusan kashi 85 zuwa 90 na yawan al’ummar...
    Adadin ‘yan jarida wadanda suka yi shahada a Gaza ya karu zuwa 226 tun bayan fara kisan kare dangi kan yankin Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya tabbatar a yau Juma’a cewa: Adadin ‘yan jaridun da suka yi shahada ya karu zuwa 226, bayan sanar da shahadar dan jarida Ahmed Qaljah. Ofishin ya bayyana cewa: Yawan ‘yan jaridan da suka yi shahada ya karu zuwa 226 tun farkon yakin kisan kare dangi kan zirin Gaza, bayan sanar da shahadar daya daga cikin ‘yan jaridan Falasdinawa: Ahmed Qaljah, wanda ya yi aiki a matsayin mai daukar hoto na gidan talabijin na Al-Arabiya. Ofishin ya yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai hare-haren wuce...
    Abdullahi ya ce, an dauko wanda ya fadan a sume amma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.   Ya kara da cewa, an mika gawar marigayin ga Hakimin Kawon Arewa, Alhaji Hamisu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hakika abin da suke yi shi ne kokarin cika alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta sanya, na taimakon yankunan karkara na kasashen Afirka wajen samun hakikanin ci gaba, inda za a kyautata muhallin rayuwar mutane, da fitar da su daga kangin talauci, maimakon samar da karuwar adadin tattalin arziki kawai. Kana a bayan manufar ta kasar Sin akwai wani tunani mai muhimmanci da kasar ta rike, wato na “Gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya”. A ganin kasar Sin, dukkan al’ummun kasashe daban daban suna zama a duniya daya, don haka suna da makomar bai daya. Saboda haka ya kamata a lura da bukatun sauran kasashe, da tabbatar da ci gaban mabambantan kasashe na bai daya, yayin da...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da gwamnan Jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara, a gidansa da ke Legas. Wannan ganawar na cikin ƙoƙarin warware rikicin siyasa da ya addabi jihar. Jami’an DSS sun kashe ’yan bindiga 45 a Neja ’Yan sanda sun sake hana hawan Sallah a Kano Fubara, ya samu saɓani da ubangidansa na siyasa, Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bayan hauwansa mulki. Saɓani kan ikon mallakar kuɗin jihar da naɗin muƙamai ya janyo rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatin jihar da kuma majalisar dokokin jihar. A watan Maris 2025, Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas tare da dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa, da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar baki ɗaya. Ya naɗa...
    ROOSC Ta Kaddamar Da Rabon Kayan Koyon Karatu a Karamar Hukumar Kaduna Sout Shirin Dawo da Yara Makaranta na Gwamnatin Jihar Kaduna Mai suna ROOSC ya kaddamar da rabon kayan koyon karatu ga dalibai a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Jihar Kaduna. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Makarantar Firamare ta LEA da ke Unguwar Mu’azu, inda manyan masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi, musamman shugabannin addini da na al’umma, suka halarta. Da yake jawabi a wajen taron, Ko’odinetan ROOSC a Jihar Kaduna, Mr. Ezra Angai, ya bayyana cewa wannan shiri hadin gwiwa ne tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da abokan ci gaba da kuma kungiyoyin aiwatar da shirin, domin inganta samun ilimi mai nagarta ga yaran da ba...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah.   Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani dasu yayin bikin sallah sun yi tashin gwauron zabo inda alumma da dama ke ta bayyana damuwar su kan wannan batu. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake...
    Sanarwar tafiyar tasa ta biyo bayan ganawar da Inzaghi ya yi da jami’an Inter a ranar Talata, sanarwar da Inter Milan ta fitar ta ce Kulob din da Simone Inzaghi sun yanke shawarar rabuwa, “Wannan shi ne shawarar da aka dauka bisa yarjejeniyar juna”, shugaban Inter Giuseppe Marotta ya kara da cewa “Ina so in gode wa Simone Inzaghi saboda aikin da ya yi, ya matukar taka rawar gani a shekaru 4 da muka shafe muna aiki tare, don haka Inter Milan na yi mashi fatan alheri a duk inda zai samu kanshi a nan gaba”.   Inzaghi ya lashe gasar Seria A daya, Coppa Italia biyu da kuma Supercoppa Italia sau uku a lokacin da ya ke San Siro,...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ce yanzu lokaci ne da Arewa za ta nuna adalci ta hanyar barin shugaba daga Kudu ya kammala wa’adin mulkinsa. Ya ƙara da cewa, “Idan za a fitar da wani ɗan takarar shugaban ƙasa daga ‘yan adawa a nan gaba, to ya dace ya fito daga Kudu maso Yamma. Wannan ne dai-daito da adalci.” Sanatan ya kuma soki gwamnatin baya da cewa ko da yake kusan dukkan shugabannin tsaro sun fito ne daga Arewa, amma hakan bai dakatar da ta’addanci a yankin ba, kuma bai hana hare-hare da kashe-kashe a jihohin Filato, Binuwai da sauran jihohin Arewa ta Tsakiya ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Farashin kayan miya, musamman kayan gwari ya yi tashin gwauron zabo a yayin da Babbar Sallah ta bana ta kawo jiki. Kuɗin kayan lambu ya ninka sau uku a cikin mako biyu, a yayin da Babbar Sallar ta zo wa iyalai da dama a Najeriya a hagunce, a sakamakon fama da matsananciyar matsalar tsadar rayuwa. Wannan hauhawan farashin, wana ta zarce abin da aka saba gani a lokutan rani, ya kasaara ƙarfin iyalai yin sayayya domin girki abincin Sallah, wanda hakan ya haifar da damuwa, musamman a jihohin Kano, Taraba, Kwara, da Jigawa. Tsadar da ba a taɓa gani ba a Kano Al’umma a Jihar Kano sun koka bisa mummunan tasirin wannan tsadar rayuwa. Wani ma’aikacin gwamnati mai ’ya’ya biyar,...
    Masu sayar da rago a jihar Zamfara sun nuna damuwarsu kan rashin samun ciniki gabanin bikin Eid-el-Kabir, duk da cewa ana samun dabbobi a kasuwanni.   Shugaban kungiyar masu sayar da dabbobi ta jihar Zamfara, Malam Saidu Ibrahim Gusau ya bayyana haka a wata tattaunawa da gidan rediyon Najeriya a Gusau.   Malam Gusau ya bayyana cewa, duk da cewa ana samun raguna da yawa, amma an samu karancin masu saye.   Sai dai ya bayyana fatan cewa lamarin zai iya gyaruwa yayin da bukukuwan Sallah ke kara gabatowa.   “Amma idan abubuwa sun ci gaba da haka, to gaskiya, akwai matsala ta gaske,”   “Har yanzu, na yi imani cewa da sauran kwanaki abubuwa za su iya canzawa, in...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa. A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai zaman kanta mai suna Child Development College da ke Akure, hedikwatar Jihar Ondo, ya hana ɗalibin satar amsa. Bayan haka ne ’yan daban sun tsare Mista Rotifa suka yi masa dukan kawo wuƙa bayan sun jawo shi daga motar ’yan sanda, kafin a ceto shi a kai shi asibiti. Lamarin ya faru ne bayan Mista Rotifa ya ƙwace wayar salula da wani ɗalibi ke amfani...
    Ya buƙaci shugabannin haɗakar su fara tsarin kafa sabuwar jam’iyyar da za ta kasance mai suna ɗaya, falsafa ɗaya, da tsarin shugabancin da zai haɗa kan kowa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar lafiyar kasar Sudan ta bayyana cewa: Ana ci gaba da daukan matakan ganin an shawo kan ci gaba da yaduwar masifar kwalara a kasar Gidan talabijin na Al-Alam ya watsa rahoton cewa: A halin da ake ciki a fannin kiwon lafiya a birnin Khartoum fadar mulkin kasar bayan bullar cutar kwalara yana ta kokarin ya shawo kan matsalar tare da killace mutanen da suka kamu da cutar a wurare na musamman a babban birnin kasar Khartoum, rahotonni sun bayyana cewa: Cutar ta bazu cikin sauri a birnin. Sannan ma’aikatar lafiya ta Sudan da kungiyoyi da dama suna ci gaba da kokarin shawo kan cutar don kada ta zama annoba wadda za ta yadu zuwa jihohi da dama. Wakilin gidan...
    Hon. Nasiru ya kara da cewa Gwamna Radda ya yi kokari wajen yaki da matsalolin tsaro wanda suka addabi Jihar Katsina, inda ya bayyana cewa ana samun sauki sosai a wannan bangare. Ya ce gwamnati ta gyara makarantu da asibitoci a fadin Jihar Katsina, inda aka maida su na zamani tare da daukar ma’aikatan lafiya da kuma malaman makaranta da yawansu ya kai 7,000, wanda ya ce ko haka aka tsaye suna da hujja da dalilin mara masa baya. Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata ne, ‘yan majalisun tarayya guda 15 dukkansu na jam’iyyar APC suka ayyana Gwamna Radda a matsayin wanda za su goya baya a zaben 2027. Sai dai kuma ana dora ayar tambaya...
    A nasa jawabin, shugaban kwamitin shirya musabakar karatun alkurani na karamar hukumar Igabi, Malam Abubakar Sadik Muhammad (Abu Asim), ya ce duk irin nasarar da kwamitin ya samu, ya samu ne bisa goyon bayan da Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani yake ba su. Ya ce shi ne kashin bayan samun nasarar da suka yi a fadin duniya. Ya bukaci daukacin iyaye da su kara zage damtse wajen ganin ‘ya’yansu sun samu ilimi nagartacce da kuma sanya ido wajen kula da tarbiyyarsu. Haka zalika, kwamitin shirya musabakar karatun alkurani ya karrama Zailani da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bai wa addinin Musulunci a ciki da wajen Jihar Kaduna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Bayan mintuna 90 na wasan ba tareda wani ya doke wani ba sai alkalin wasa ya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga, Jamaica ta ci kwallaye 4 inda Nijeriya ta ci dukkan kwallaye 5 da yan wasan suka buga, hakan ya sa yaran na Eric Chelle suka lashe gasar Unity Cup ta bana da ta kunshi kasashen Ghana, Trinidad And Tobago, Jamaica da Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Gane amfanin lamarin da ya shafi ilimi shi yasa, Gwamna Lawal ya kaddamar da dokar ta baci a bangaren ilimi a watan Nuwamba 2023,matakin da aka dauka an yi sa’a ya haifar da da mai ido a bangaren ilimi a Jihar Zamfara. “Fiye da makarantu 500 aka y masu kwaskwarima da samar masu abubuwan da suka kamata tun lokacin da aka kaddamar da dokar ta bacin.An horar da Malaman makarantun gwamnati,ana kuma ci gaba dayin hakan. “Saurin biyan kudaden bashi da Hukumomin WAEC da NECO ya kawo kwanciyar hankali ga daliban da suka kammala makaranta da rubiuta jarabawa, sai dai basu samu ci gaba da karatu ba saboda Hukumomin jarabawar sun rike masu sakamakon jarabawar da suka yi. Daga...
    Cutar kwalara ta yadu a Sudan, kuma ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan asibitoci biyu a Jihar El Obeid na kasar Sudan na ci gaba da fama da tabarbarewar yanayin tsaro da lafiya bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan. A bangaren tsaro kuma, Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces sun kai hare-haren bama-bamai a wasu asibitoci biyu da wasu unguwanni a birnin El Obeid da ke Arewacin Kordofan a tsakiyar kasar Sudan. Wata majiyar soji ta bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa sun afkawa Asibitin Al-Daman da kuma Jami’an lafiya da ke tsakiyar birnin da manyan bindigogi. Sojojin Sudan sun tabbatar da cewa: Sun yi luguden wuta kan sansanonin dakarun...
    Ya ce a nemi bayani daga wurare daban-daban kamar Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomin Nijeriya (NULGE) da Ma’aikatar Kudi, ya kara da cewa sakataren gwamnatin tarayya shi ne shugaban kwamitin aiwatar da hukuncin. Abubuwan da mutane yawa suke gnin ya janyo jinkirta aiwatar da hukuncin shi ne, shigar da sabon sharadi daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), wanda ke bukatar dukkanin hukumomin gwamnati 774 su bayar da akalla shekaru biyu na rahotannin kudinsu kafin su iya karbar kasafin kudadensu kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya. Babban bankin ya bayyana cewa dole ne gwamnatocin kananan hukumomi su cika bukatun kafin su bude asusu don kura musu kudadensu kai tsaye. Ka’idojin da aka gindaya wa kananan hukumomin ya kara janyo tsaiko wajen jinkirta aiwatar...
    Wasu jami’an diplomasiyyar turai sun yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu da cewa za ta fuskanci Karin matsin lamba idan har ba ta sauya halayyarta akan Gaza ba. Jaridar “Washington Post” ta Amurka ta ambato jami’an diplomasiyyar turai suna cewa; sabon tsarin da ake yin aiki da shi na raba kayan agaji a Gaza, ya juya ya zama harigitsi kuma ana bude wuta akan mutane da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar Falasdinawa da dama.” Har ila yau jami’an diplomasiyyar na turai sun ce, ko kadan ba su da aniyar bayar da kayan agajinsu ga masu tafiyar da tsarin da su ne Isra’ila da Amurka.”  Bugu da kari, majiyar diplomasiyyar ta tarayyar turai ta ci gaba da cewa; Hotunan masu ban tsoro...
    Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a. Kasar ta ce wuraren da haramcin ya shafa sun hada da makarantu da tashoshin mota ko na jirgi, wuraren shakatawa, wuraren wasanni ko kasuwanni saboda kada yara kanana su gani. Yadda ambaliyar Neja ta ci mutum 12 ’yan gida daya NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ministar Lafiya da Iyali na kasar, Catherine Vautrin ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ta ce, “Dole a daina shan sigari a wuraren da yara suke. “’Yancin shan sigari ya kare ne a inda ’yancin yara na shakar tsaftatacciyar iska ya fara,” kamar yadda ministar ta shaida wa jaridar Ouest-France...
    PUNCH Metro ta tuna cewa a kwanakin baya jami’an hukumar EFCC shiyyar Ilorin sun kama wasu mutane 17 da ake zargi da damfarar yanar gizo a cikin hadaka a Kananan Hukumomin Ilorin da Ifelodun na jihar. Oyewale ya ce an tare wadanda ake zargin ne a madatsar ruwa ta Asa da yankin Jami’ar Al-Hikmah da yankin Gaa-Odota da ke Ilorin da kuma yankin Ganmo da Amoyo na jihar. “Kamen da aka yi a ranar Talata, 13 ga Mayu, 2025, ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu wanda ya alakanta wadanda ake zargin da ayyukan damfara ta Intanet a jihar. Sanarwar ta kara da cewa, “Kayan da aka kwato daga hannunsu da aka kama sun hada da manyan motocin alfarma...
    Sanarwar bayan taron koli na hadin gwiwar Sin da kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kwamitin hadin gwiwar kasashen Larabawa na yankin Gulf wato GCC, ta jaddada burin sassan uku na bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki, musamman ta hanyar gudanar da cinikayya marar shinge, da kammala yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin ’yanci tsakanin Sin da da GCC. Idan mun waiwayi wannan sanarwa ta hadin gwiwa, za ku gano manufofin da sassan uku ke fatan cimmawa, wadanda suka hada da fatan dunkule shiyyoyinsu waje guda, da kara yin tafiya tare, da neman samun ci gaba mai dorewa. Karkashin wadannan burika, sassan uku za su yi amfani da fifikonsu wajen cimma moriyar juna da karfafa kawance a...
    Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska. Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su. Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau shekara biyu ke nan cif  tun bayan da  shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya a matsayin shugaban ƙasa na 16 tun bayan samun ‘yancin kai.   Daya daga cikin abubuwan da shugaban kasar ya fara yi yayin jawabin karbar mulkin shi ne sanar da kawar da tallafin man fetur. Yayin da yake cika shekaru biyu, ana ci gaba da muhawara mai zafi game da irin nasarorin da aka samu da kalubalen da ake fuskanta da kuma yadda al’ummar ƙasa ke amfana da tsare-tsaren gwamnati. NAJERIYA A YAU: Matsalolin Da Suke Tarnaki Ga Kananan Yara A Najeriya Da Hanyoyin Magance Su DAGA LARABA: “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na...
    A ci gaba da tafka laifukan yakin da HKI take yi a Gaza,Fiye da Falasdinawa 60 ne su ka yi shahada a jiya Laraba. A wani harin da sojojin mamayar su ka kai a yankin Jabaliya, Falasdinawa 5 sun yi shahada, yayin da wani adadi mai yawa su ka jikkata. Wani jirgin sama maras matuki ya kai wani harin a unguwar “Shuja’iyya” wnada ya yi sanadin shahadar mutum daya, sai kuma wasu shahidan 4 a unguwar “Shari’u 5”, da kuma wasu shahidan 4 a garin “Bani-Suhaila”. Wasu rahotannin sun ce, ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a garin ‘Abasan al-kabira’ da ya yi sanadin shahadar mutum daya da kuma jikkatar wasu masu yawa. A yankin Qizan kuwa, ‘yan sahayoniyar sun...
    Shugaban rundunar mayakan sama ta kasa,Air Marshal, Hassan Abubakar, ya bukaci tsoffin daliban makarantar ‘ya’yan sojoji dake Zaria watau NMS da su kasance masu kwazo da da’a a duk inda suke kamar yadda suka koya a makarantar. Ya bayyana haka ne lokacin da ya ke jawabi a matsayin Babban bako na musamman a wurin bukin cika shekara 71 da aka gudanar a filin faretin RSM Zakari Kumasi dake harabar makarantar a zaria. Shugaban rundunar mayakan saman ya bayyana cewa makarantar ta NMS ta yi fice wajen baiwa yara horo a fannonin karatu da kuma ilimin aikin soja wanda hakan ya sa ta samar da manyan sojoji da dama har ma da shi a ciki. Air Marshal Abubakar ya ce bukin...
    Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Shafiu Abubakar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda cinna wuta a wani masallaci a kauyen Gadan, Karamar Hukumar Gezawa, yayin da jama’a ke tsaka da jam’in sallar asuba a ranar 15 ga Mayu, 2024. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da raunana wasu. An samu Shafi’u da laifuka hudu, ciki har da kisan kai da kuma barna ta hanyar gobara. Baya ga hukuncin kisa, alkali ya ba da umarnin a yi masa bulala 150, tare da biya tarar N1,500, sannan kuma a kwace babur dinsa mai kafa uku, inda za a sayar, a yi amfani da kudin da aka samu wajen gyaran masallacin da ya lalace. Yayin shari’ar, masu...
    Wani bafalasdine ya rasa ransa, bayan da harsasai da sojojin yahudawa suka cilla masa a garin Ariha na yankin yamma da kogin Jordan sun fada a kansa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Falasdinawa WAFA ya na fadar haka a yau Talata, ya kuma kara da cewa Mohammed Yahya Asi Jalaytah ya yi shahada ne bayan da albarusan da sojojin suka cilla masa sun fada a kansa sun kuma ji masa munanan raunuka. Labarin ya kara da cewa bayan tsakiyar dare ne sojojin yahudawan suka soma barin wuta da bindigogi da kuma jefa hayaki mai sa hawaye a kan Falasdinawa a garin Ariha, Inda albarusai suka sami Asi Jalaita suka kuma kasashe shi. WAFA...
    Ya ce: “Ya kamata ku nazarci Shugaban Ƙasa sosai. Za ku iya faɗin ra’ayoyin ku; zai saurare ku, amma a ƙarshe shawarar da zai yanke tasa ce. Ina ganin ya dace mu gane hakan.”   Yayin da yake bayani kan taken taron, ministan ya ce Shugaba Tinubu na da cikakkiyar niyya wajen aiwatar da Shirin Sabunta Fata — wanda tsari ne da ya mayar da hankali kan jin daɗin talaka da fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya.   “Shirin Sabunta Fata na da nufin kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’ummar Nijeriya ta hanyar muhimman matakai da za su fitar da cikakken ƙarfin Nijeriya, ta hanyar da ba a taɓa gani ba,” inji ministan.   Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu...
    Daga Bello Wakili Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Ayyuka na Musamman, Mista Tunde Rahman, ya bayyana jerin goyon bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke samu daga cikin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin shaida mai karfi kan tsare-tsaren da gwamnati ta aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata. A yayin wata tattaunawa da ya yi da Radio Nigeria a Abuja, Mista Rahman ya ce goyon bayan da ke fitowa daga gwamnoni na APC, ‘yan majalisar dokoki da shugabannin jam’iyya, na nuna karuwar amincewa da sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Tinubu ya aiwatar. Ya ce wannan ya hada da cire tallafin fetur da daidaita farashin canjin kudade. “Wadannan goyon bayan suna da matukar...
    Fastan nan mai suna Rev. Azzaman David, shugaban majami’ar The King Worship Chapel da ke Kaduna, ya rasu a wani hatsarin mota a ranar Asabar yayin dawowarsa daga Makurdi, jihar Benue zuwa Kaduna. Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) na Jihohin Arewa 19 da FCT, Rev. John Joseph Hayab, ya tabbatar da mutuwar fastan, inda ya bayyana cewa al’ummar Kirista ta yi hasarar babban jarumi. “Evangelist Azzaman ya kasance mai himmar wa’azi, mai kare addinin Kirista, kuma mai fafutukar kare hakkin masu ƙaramin ƙarfi. Rayuwarsa ta kasance cikin jarumtaka da ƙwarin gwuiwa ga gaskiya da adalci,” in ji Hayab. CAN ta yi wa iyalansa, da ‘yan cocinsa, da duk wanda rayuwarsa ta shafa ta’aziyya, tare da addu’ar Allah ya ba...
    Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda hakan ya sa Zamfara ta kasance a baya a fannin ilimi a faɗin Nijeriya. “Da sanin matsalolin da ke tattare da harkar ilimi, Gwamna Lawal ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a watan Nuwamba 2023, matakin da ya samar da sakamako mai kyau ga bangaren ilimi a jihar Zamfara. “Sama da makarantu 500 ne aka gyara tare da samar da kayan aiki tun bayan...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta sanya hannu kan yarjejeniyar Naira biliyan uku domin gina mayankar dabbobi ta zamani a garin Gombe. Hakan wani bangare ne na shirin inganta kiwon dabbobi da tsaftar abinci da kuma rage matsalolin kiwon dabbobi (L-PRES) wanda Bankin Duniya ke tallafa wa. Shirin L-PRES na da nufin kyautata harkar kiwon dabbobi da sarrafa nama cikin tsafta a jihar. An kulla yarjejeniyar ce tare da kamfanin Lubel Nigeria Limited da wa’adin kammalawa na watanni 9, zuwa watan Fabrairun shekarar 2025. An gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin L-PRES da ke G.R.A, a Gombe, inda shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana wannan aiki a matsayin babban ci-gaba a jihar. Sojoji sun kashe mayaƙan...
    Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, James Lashen, ya tabbatar da cewa an kashe mutane huɗu a harin, yayin da babu wani ɗansanda da ya jikkata a faɗan da suka yi da maharan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ana gudanar da zagaye na biyar na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin tawagar Amurka da na Iran a cikin yanayi na kwarewa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana a yau Juma’a cewa: Tattaunawar tana gudana cikin kwarewa da kwanciyar hankali, yana mai cewa abin da ake yadawa a kafafen yada labarai hasashe ne da baya da tushe ko inganci kuma baya da bambanci da shaci fadi. A yau Juma’a da yamma ne aka fara shawarwarin da ba na kai tsaye ba karo na biyar...
    Daga Bello Wakili Dukkan ‘yan majalisun tarayya daga Jihar Katsina sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Radda domin ya sake tsayawa takara a wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben shekarar 2027 mai zuwa. An bayyana wannan matsaya ne a lokacin wani taron hadin gwiwa da ‘yan majalisar suka gudanar, inda Honourable Sada Soli, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jibia da Kaita, ya yi magana a madadin takwarorinsa. Ya bayyana cewa wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin hadin gwiwa da suka yi kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma goyon bayan da al’ummar jihar suka nuna daga kowane bangare. ‘Yan majalisar sun yaba da irin salon shugabanci na Gwamna...
    Mataimakin Daraktan Ayyuka na Operation Haɗin Kai, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya tabbatar da kashe ‘yan ta’addan, yana mai cewa Sojojin na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’addan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Nahiyar Afirkan a karkashin tarayyar Afirka ta kafa cibiyar dake kula da sararin samaniya domin tattara bayanai, wacce ke da matsuguni a birnin “alkahira’ na Masar. Sabuwar cibiyar dai ta fara aiki ne a watan da ya gabata,kuma za ta rika musayar bayanan da take tattarawa da cibiyoyin kasashen da suke a fadin nahiyar. Haka nan kuma cibiyar za ta kyautata ayyukanta ta hanyar harba taurarin dan’adam a sararin samaniya da kafa cibiyoyin bibiyar yanayi domin yin musayarsu da kasashen nahiyar da kuma wajenta.
    Wani dattijo mai aikin kwashe shara da ya shekara 40 yana tara kuɗin domin zuwa aikin Hajji ya samu cika burinsa a bana. A karshe dattijoin dan qasar Indosauke ya samu damar zuwa sauke farali inda ya isa Kasa Mai Tsarki tare da matarsa. Wanni dattijon wanda ya nuna tsananin juriya da jajircewa ya bayyana yadda kwashe shekara 40 yana tara 1,000 na kuɗin ƙasarsu a kullum, domin tara kuɗin da zai sauke farali shi da mai ɗakinsa. A yayin da ake yake hira da Kamfanin Dillancin Labarai na kasar Saudiyya bayan isarsu ƙasar domin sauke farali, dattijoin ya bayyana cewa tun ashekarar 1986 ya fara tara wannan kuɗi bayan samun goyon bayan matarsa. Dangote ya sake...
    Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai a yau Laraba, inda jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar da ke da ruwa da tsaki ya bayyana cewa, aiwatar da matakan da suka dace bisa “Ayyuka guda goma” na hadin gwiwa da Afirka, ya haifar da sakamako mai kyau, wanda ya zuba babban kuzari ga hadin gwiwar Sin da Afirka. Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin Tang Wenhong ya bayyana cewa, an riga an tattauna tare da kasashen Afirka sau da dama, an kuma amince da tsarin “Kasa daya, manufa daya” wajen tsarawa da aiwatar da matakai. Rashin Tsaro: Matasa Sun Yi Zanga-zangar Toshe Babbar Hanya Saboda Satar Mutane A Edo Za A Gudanar Da Baje Kolin...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa wasu daga cikin sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa ƙungiyar Boko Haram ta hanyar ba su bayanai. A wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na News Central, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wanda ke taimaka wa ’yan ta’adda. Hajjin 2025: Kashi 79 na maniyyatan Najeriya sun isa Saudiyya – NAHCON Gwamnati za ta sayar da gidaje 753 da EFCC ta ƙwato a hannun Emefiele  Ya ce: “Akwai masu bai wa Boko Haram bayanaj a cikin sojoji, ’yan siyasa da sauran jama’a. Za mu ƙarfafa leƙen asiri, kuma mu ɗauki tsattsauran mataki a kansu.” Gwamna Zulum ya ce dole...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu nay au zai yi Magana dangabe da “Tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran da Amurka yana tanga-tanga’ wanda ni tahir amin zan karanta. Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa, da alamun tattaunawa tsakanin kasar ta kuma Amurka dangane da shirin nukliyar kasar Iran ba zai je ko in aba, saboda yadda bangaren Amurka a cikin kafafen yada labaransu, daga ciki har da jakadan Amurka kan al-amuran gabas ta tsakiya, kuma shugaban tawagar Amurka a tattaunawar wato Steve Witkoff  ya fito a kafafen yada labarai na Amurka yana fadar cewa duk wata yarjeniyar da za’a cimma da kasar Iran nan gaba dole sai...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da sayen ƙarin motoci guda 10 don taimaka wa sojoji da ’yan sa-kai wajen yaƙi da ’yan Boko Haram da ISWAP. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai Kala-Balge, inda ya gana da ƙungiyoyi daban-daban. An kashe makiyaya 2 a wani hari a Filato Yadda ’yan sanda suka kashe dan fashi suka kwato bindigogi 7 a Abuja Ya ce za a bai wa ’yan sa-kai motoci shida ƙirar Toyota Hilux, ciki har da CJTF, mafarauta da ’yan banga, sannan za a bai wa sojoji ƙarin motoci huɗu masu bindiga. Zulum, ya kuma raba wa iyalai 10,000 da ke fama da talauci a yankin kayan abinci, yawancin waɗanda...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da taron tattaunawa ta Tehran wanda aka bude a ranar Lahadi 18 ga watan mayu a nan Tehran. A ranar Lahadi 18 ga watan Mayu da muke ciki ne aka bude taron tattaunawa da ta Tehran ta farko a nan Iran, don tattauna batutuwan da suka shafi kasashen yankin yammacin Asiya. Inda shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan da kuma ministan harkokin wajen kasar Iran suka gabatar da jawaban farko a taron. An sami halattan baki daga kasashe 53 daga cikinsu akwai jami’an gwamnatoci wadanda suka hada da ministoci  masana da shuwagabannin cibiyoyin bincike da bada shawarori na kasashen duniya da dama. Daga cikin bakin akwai ministan...
    Akalla manoma 90 ne mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP suka kashe a Jihar Borno cikin watani biyar da suka gabata. Mayakan kungiyar sun kuma yi garkuwa da wasu da dama baya ga wadanda suka tsallake rijiya da baya a hare-haren kungoyiyoyin da raunin harbi. Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa kungiyoyin ‘yan ta’addan sun kai hare-haren ne a tsakanin watan Janairu zuwa Mayun nan da muke cikin na shekarar 2025. Hari na baya-bayan nan shi ne wanda mayakan kungiyar ISWAP suka yi ritsa manoman da ke aiki a gonakin wake suka yi wa mutum 50 kisan gilla a yankin Karanti da ke Karamar Hukumar Kukawa a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu. Gwamnatin Kano ta dakatar da haska shirin...
    Gobara ta tashi a Kwalejin Karatun Alƙur’ani da ilimin addinin Musulunci mallakin fitaccen malamin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da ke Rafin Albasa, a Jihar Bauchi, inda ta ƙone ginin makarantar da kayan cikinta. Binciken wakilinmu ya gano cewa gobarar ta lalata bene mai ɗakuna da dama ciki har da ofisoshi, ajujuwa, ɗakunan gwaje-gwaje, ɗakunan kwamfuta, da ɗakunan karatu. Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa Yadda ’ya’yan shugabanni ke musu yaƙi da ’yan adawa An kuma rasa kayan sawa na malamai da ɗalibai, katifu, barguna da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum. Har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Sai dai daraktan makarantar, Sayyadi Aliyu Sise Dahiru, ya ce sun...
    Jiragen na sojojin HKI sun kai hari ne dai a yau Lahadi a kan hanyar da ta raba tsakanin garin Beit-Yahun da Bent-Jubail dake kudancin kasar. A garin Kafar-kalla ma wani jirgin saman marar matuki ya jefa bama-bamai masu sauti a kusa da wani gida da dama an rushe shi. Harin na sojojin HKI yana cikin ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon da take yi wanda ya wuce 2000 tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 27 ga watan Nuwamba na 2024.  Bugu da kari HKI ta girke sojojinta a cikin wasu wurare 5 dake kan iyaka,wanda shi ma keta karjejeniya ce. Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hizbullah ta sha yin kira ga gwamnatin kasar da ta yi duk abinda...
    Bayan da wani matashi ɗan shekara 33 ɗan kasar Japan mai suna Honkon ya yi tarin kuɗi na tsawon shekaru 10 don siyan motar da yake mafarki — na wata sabuwar mota ƙirar Ferrari 458 Spider — sai ya zauna yana kallon yadda motar take ƙonewa cikin sa’a ɗaya da tuƙa ta a karon farko. Kafofin sada zumunta na ƙasar Japan sun yi sharhi game da rahoton baƙin ciki na Honkon, matashin da ya kasance mai shirya wakoki, wanda ya kashe makudan kuɗi game da mafarkin sayan motarsa ta Ferrari, sai dai ya kalle ta tana ci da wuta a ranar da ya tuƙa ta a karon farko. ISWAP ta kashe manoma sama da 50 a Borno Guguwar raba Masarautar...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga shugaban Iraqi Abdul Latif Rashid, wanda kuma shi ne shugaban karba-karba na majalisar shugabannin kasashen kungiyar Larabawa, tare da taya murnar kaddamar da babban taron kungiyar na 34, a birnin Baghdad na Iraqi. Xi Jinping ya bayyana cewa, cikin shekaru sama da 80 da kafata, kungiyar kasashen Larabawa ta kasance mai mayar da hankali kan inganta hadin kai da karfafa yankin Larabawa da furta matsalolin kasashen da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya. Ya kara da cewa, a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen Larabawa wajen zurfafa aminci da ingiza hadin gwiwar moriyar juna da kara musayar...
    Sojoji da mafarauta don halaka mayaƙan Boko Haram biyar tare da daƙile wani hari da ’yan ta’addan suka kai a ƙauyen Warambe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Warambe na daga cikin yankunan da mazanaunansu suka dawo da zama a baya-bayan nan, kuma mayaƙan Boko Haram sun sha yin yunƙurin kurɗawa cikinsa. Shugaban mafarautan wanda ɗan asalin garin ne ya ce a safiyar Juma’a ne maharan suka nemi shiga ƙauyen, “amma muka gana  su, muka kashe mutum biyar daga cikinsu. An miƙa makaman da muka ƙwato daga hannunsu ga sojoji.” Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Kudancin Borno, ya jinjina wa ƙoƙarin jami’an tsaron, musamman wajen ɗaukar mataki cikin gaggawa yana mai ba su ƙwarin gwiwar su ƙara...
    A lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki a watan Mayun 2023, ya ci karo da tsarin kiwon lafiya da ya tabarbare saboda rashin kulawa. Ya ce, “Gwamnatinmu, ƙarƙashin ginshiƙan shirye-shiryen ceto, nan da nan ta fara tantance abubuwan da asibitoci ke buƙata, inda sakamakon ya zama abin tsoro kuma ya nuna akwai jan-aiki. “Alal misali, a jihar da ke da mutane kusan miliyan 6 tare da tarin ƙalubale, na’urar duban ɗan tayi ɗaya ce kawai a cikin dukkan cibiyoyin da gwamnati ta mallaka, kuma shi ma duk faci ne a jikinsa da salataf ko’ina! Nan take na ayyana dokar ta-baci a bangaren kiwon lafiya don dawo da ababen more rayuwa, samar...
    “Don haka, idan kuna tunanin cewa taron bayanin ministoci, kamar yadda wasu ke yaɗa cewa za a mayar da shi zuwa wajen ƙasar, ba gaskiya ba ne.   “Wannan dandamali da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take samarwa, nan ne inda abin ke faruwa, a nan ƙasar.”   Taron ya samu halartar Ministar Harkokin Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙira, Hannatu Musawa; da Ministan Ruwa da Tsaftace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, da kuma Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi.   Sanata Umahi, wanda aka ruwaito ba daidai ba cewa yana daga cikin ministocin da za su gabatar da nasarorin Gwamnatin Shugaban Ƙasa Tinubu a wani taro a London, ya goyi bayan furucin Idris, yana mai cewa rahoton ba gaskiya ba...
    Harajin ya kuma kai kasa da kimanin kaso 11 a cikin dari, wanda ya kai kasa da wanda ake karba, idan aka kwatanta da duniya. “Abinda muka yi shi ne, mun cire daukacin ma’aikatan da karbar kasa kaso uku a cikin darei a cikin tsarin na karabar harajin,” Inji tsohon Shugaban LLP. Ya shedawa manyan Malaman Makaranta  da Jami’an da ke katbar haraji hakan ne, a wani taro da aka gudanar a jihar Legas Nijeriya dai, ta kasance kasar da sama da alumominta miliyan 8o, ke fama da kangin talauci. Hakan ya kuma kara haifar da hauhawan farashin kayan masarufi, musamman yadda kayan suka tashi a 2024, kafin su sauka zuwa kaso 24.2 a cikin dari. Kazalika, hauhauwan farashi da...
    Mun bijoro da wannan batun kalubalen da manoman ke ci gaba da fuskanta ne, musamman duba da cewa, kakar noman bana, ta karato, musamman ganin cewa, an fara samun saukar Ruwan sama, a wasu sassan kasar nan, inda kuma tuni, mahara suka mamaye wasu yankunan kasar da ake yin noma. Akasarin fadin kasar nan, musamman a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma duba da cewa, wadannan yankunan biyu, sun yi fice wajen yin noma, amma abin takaici, ‘yan bindiga daji, ‘yan ta’adda da kuma wasu Fulani Makiyaya, sun mayar da wadannan yankunan fagen daga, inda suka kashe manoma da kuma lalata amfanin gonakansu. Bugu da kari, wadannan bata garin sun kuma kone wasu gidajen alumomin da ke a...
    A ranar Alhamis din nan, wasu hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai sun kai ziyara hedikwatar hukumar ta NOA inda suka yi amfani da damar wajen lekawa daya daga cikin kayayyakin tarihin Nijeriya a baya – ofishin marigayi shugaba Shagari. Bayan kammala ziyarar, daya daga cikin hadiman shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Temitope Ajayi, ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook domin bayyana abin da suka gani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Ofishina ya cika da tarin jama’a suna ta kiraye-kiraye kan wannan mummunan sakamakon da aka samu a jarabawar JAMB ta 2025.   “ASUU za ta kalubalanci wannan sakamakon a gaban babbar kotu idan JAMB ta gaza sake duba sakamakon da kuma bai wa dalibai makin da suka cancanta.” In ji shi   Ya yi kira ga gwamnonin jihohin Kudu-maso-Gabas da su tashi su kalubalanci abin da ya kira da rashin adalci domin hana dalibai daga shiyyar samun shiga manyan makarantu a kasar nan.   LEADERSHIP ta ruwaito cewa, shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, a ranar Laraba ya bayyana shirin sake gudanar da jarabawar ga dalibai da suka fito daga jihohin Kudu maso Gabas da Legas. Daga kanmu, magana ta...
    Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.   Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 aka bayar da rahoton, sun samu maki kasa da 200 daga cikin mafi girman maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi na kasar.   UTME ta wannan shekara, ta gamu da koma baya sosai, wanda ya haifar da damuwa tsakanin ɗalibai, iyaye, da malamai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Sakamakon rikicin siyasa a jihar, ne ya sanya Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa, da dukkanin ‘yan majalisar dokar Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Haka kuma, Shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas tare da naɗa mai riƙon kwarya da zai shugabanci jihar na tsawon wannan lokaci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp