Taron Abuja kan Tattaunawakan Tattalin Arziki Kasa- “Akwai yiyuwar tattalin arzikin kasa zai murmure a shekarar 2026”
Published: 12th, December 2025 GMT
Taron Abuja kan Tattaunawakan Tattalin Arziki Kasa- “Akwai yiyuwar tattalin arzikin kasa zai murmure a shekarar 2026”
Masana a Taron Abuja na Tattaunawa kan Tattalin Arziki Kasa da ake wa lakabi da Abuja Economic Dialogue 2025 da Kamfanin Ignite Capital ke shiryawa duk shekara da haxin gwiwar Kamfanin Innovision Global Consulting sun yi hasashen cewa, za a samu saukar kayan masarufi da Karuwar samar da ayyukan yi a faxin kasa a shekara mai zuwa ta 2026.
Masana tattalin arzikin da suka yi fashin baki kan yadda tattalin arzikin Nijeriya ke tafiya a cikin watanni tara da suka gabata, a taro sun haxa da Dakta Paul Arinze, Shugaban Kamfanin Bincike da Nazari kan harkokin tattalin arziki mai suna Pedestal Africa da Dakta Umar Kwairanga Kwararre kan harkokin tattalin arziki da ayyukan banki da Dakta Sara Alade tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Babban Banki na Kasa kuma Kwararriya a fagen tattalin arziki da kuma Dakta Nuruddeen Zauru wani masanin tattalin arziki.
A cikin sakonsa na fatan alheri tsohon Mataimaki Shugaban Kasa kuma Sardaunan Zazzau, Alhaji Namadi Sambo ya yi tsokaci kan bukatar cewa, lokaci ya yi da gwamnati za ta xauke cigaban da take ikirarin samu a fannin tattalin arziki daga alkalumma a takarda zuwa aiwatarwa a aikace. Ta yadda talakawa za su ga sauKin da ci gaban da aka samu kasa ba labari ba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a taron tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ta Qasa, Alhaji Abubakar Bukola Saraki, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya dace shugabanni a Nijeriya su san cewa, ba tare da samar da cikakken tsaro da dauwamammiyar wutar lantarki ba tattalin arzikin Nigeriya zai ci gaba da yin kwan gaba-kwan baya.
Saraki ya kuma yi kira da gwamnati da rinka karfafa gwiwar kamfanonin cikin kasa ta hanyar sayen kayayyakin da suke samarwa.
Mai masaukin baki kuma Shugaban Kamfani Ignite Capital, Bukar Abba Kyari ya yaba wa gwamnatin Shugaba Tinubu, kan irin matakan da yake xauka don inganta tattalin arzikin kasa tare da tallafa wa matasa kan harkokin da suka shafi kasuwancin zamani na yanar gizo.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: tattalin arzikin tattalin arziki
এছাড়াও পড়ুন: