HausaTv:
2025-12-13@15:35:20 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170

Published: 13th, December 2025 GMT

170-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddeen Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan Shirin.

/////….Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan al-Mujtaba(a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s)  da muke kawo maku.

A cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da Magana dangane da dalilin da suka sa Imam Al-Hassan (a) ya sulhunta da mu’awiya dan Abusufyan, da kuma mika masa shugabancin al-ummar musulmi duk tare da cewa ya san hakan, ba alkhairi ne ga al-ummar musulmi ba, amma ba yadda zai yi, ko kuma bai da zabi, saboda bai da mataimaka, bai da sojoji masu ikhlasi wadanda zasu yi yaki tare da shi, sojoji wadanda zasu yi biyayya a gareshi. Su kuma yaki makinsa don neman yardar Allah.

A cikin shirimmu da ya gabata har’ila yau mun fara kawo maki maganar ‘Isma’ ko kuma kariya daga aikata kuskure ko yin ba dai dai ba wanda Imam Al-Hassan (a) yake da shi.

Mun bayyana cewa Ayar Tsarkakewa, aya ta 33 a cikin suratul  Ahzab tana daga cikin wadan nan ayayin Alkur’ani wadanda suke tsarkake wadannan bayin Allah wanda Imam Al-Hassan yana daga cikinsu.

A hadisin wanda malaman sunna da dama suka ruwaitoci, manzon Allah (s) wata rana, ya bukaci matarsa ummu salama (r ) ta kira masa Fatimah da mijinta da yayanta Al-Hassan da Al-hussain(a). a lokacinda suka zo sai ya lullubesu da wata mayafi sakar yemen sannan ya daga hannayensa masu albarka yana cewa, Ya Ubangiji wadanda sune iyalan gidana ka tafiyar da dauda a garesu ka tsarkakasu tsarakaewa, sai mala’ika jibirilu ya sauko ya karanta masa wannan bangaren na aya ta 33 a cikin suratul Ahzaba.

Daga cikin malaman shiga wadanda suka tafi a kan cewa Imam Al-Hassan yana daga cikin wadanda aka tsarkaka, Akwai sayyid Murtadha alamulhuda, wanda sunansa Aliyu bin Hussain kuma mun bayyana kakansa shi ne Musa dan Jaafaru (a) daya daga cikin limamai masu daga cikin iyalan gidan manzon Allah (s). Alamul Huda, ya ce: (Lalle shi-yana nufin Imam Al-Hassa- ya tabbata shi ma’asumi ne wanda yake samun taimakon Allah, da hujjuji bayyananu, da dalilin masu rinjaye, don haka babu makawa daga mika kai ga dukkan abinda ya aikata, ko da kuwa a cikinsu akwai abubuwansa da baza’a iya fahintarsa dalla-dalla ba. Ko kuma akwai wasu abubuwa wadanda zukata suke kyamarsa) wannan kamar yadda yazo cikin littafinsa Tanzihul Anbiya. Sh.69.

Daga nan sai Sayyid Bin Tawoos, sunan Sayyid Aljali bin Tawoos ( r) ya na fada a cikin wasiyyan da yayiwa dansa, dangane da Sulhun Imama Hassan(a) inda yake cewa {Da na! ba abin mamaki bane ga wadanda suka aibata kakanka Alhassan kan sulhu da Mu’awiya, wanda ya kasashe da umurnin kakansa ne, kuma kakansa ma yayi sulhu da kafirai kuma uzurinsa a lokacin a fili yake.

Amma a lokacinda dan’uwansa Alhussain don taimaka masu da kuma amsa tambayarsu, ya yi watsi da sulhu da yazid la’anenne, suna daga cikin wadanda suka kashe shi suka ki binsa, kuma bamu taba jin sun yi fushi a cikin ranakun mulkin yazid kan mummunan kissan da aka yiwa AL-Hussain ba, bamu taba jin sun masa tawaye ba. Bamu ji sun kauda shi daga kan kujerar Khalifanci ba.

Amma munji sun yi fushiwa Abdullahi dan Zubair suka kuma taimaka masa a kan batanrsa, sai al-amarinsu na sabawa gaskiya ya bayyana a fili, kuma  mummunan zabensu ya bayyana a filio,,, shin ana iya nisanta cewa wadannan sun bace daga kan hanya madaidaiciya ba. Bayanda suka kai wannan matsayin na kekacewar zuciya mai girma abin aibatawa).

Da farko, a wannan wasiyyar Sayyid bin Rawoos ga dansa, ya kwatanta sulhun Imam Al-Hassan (a) da sulhun kakansa manzon Allah (s) da kafiran makka, kamar yadda yake a cikin sulhun hudebiyya, sannan kamar yadda sulhun manzon Allah (s) bay a bisa kuskure, kuma banda haka maslaha ce hakama sulhun Imam Al-Hassan yake don shi ma’asumi ne kamar kakansa. (s).

Na biyu kuma, irin jarrabawan da Imam Al-Hassan ya sha a hannun wadannan mutane fasikai, ya tabba cewa su ba mutanen kirki ne ba, saboda basu nuna wata falala da kuma girmamawa ga Imam Al-Hassan(a), ba. Saboda halayensu ne ya yi sulhun don yahuta da sharrinsu.

Kuma sayyin bin Dawoos ya kafa hujja da sharrinsa kan yadda suka aikata kisa mafi muni a tarihin bil-adama, sannan basu yi nadama ba, basu yi wani aiki wanda yake nuna cewa sun yi nadama ba. Sun kashe Imam Hussain (a) a karbala, amma basu yi wani yunkuri na kauda yazid ba.  

Don haka tare da wannan mun yi imanin cewa sulhun Imam Al-Haasan sulhu ne wanda yake kan hanya, kuma shi ne kawai mafita ga musulmi da kuma shi Imam (a) a lokacin.

Banda haka, mun yi Imani kan cewa, da Imam Al-Hussain (a) ne a matsayin Imam Al-Hassan (a) to ba abinda zai yi, in banda abinda yayansa Imam Al-Hassan (a) yayi na sulhu da Mu\awiya dan Abusfyan, saboda su shuwagabanni wadanda basa sabani a tsakaninsu. Saboda mabubbugan ilminsu guda ce, mahaifinsa daga kakansu manzon Allah (s).

Sannan wanda ya karanta tarihin musulunci ya san cewa, Mu’awiya dan Abusufyan, a dai dai lokacinda y afara rigima da banu Hashim, ko Aliyu dan Abitalib (a) sannan dansa Imam Al-Hassan (a) daga baya, yakan bayyana a fili rikonsa da wasu dokokin addinin musulunci da sunnar manzon Allah (s), ba don yayi Imani da su ba, kamar yadda zamu gani nan gaba, said ai don yaudarar musulmi su yi biyayya a gareshi, amma a lokacinda al-amura suka tabbata a hannunsa, sai ya bayyana kafirci da munafurcinsa a fili.

Don haka sulhun da yayi da Imam Al-Hassan (a) ya say a fito da halayensa na gaskiya, na kin addinin musulunci da musulmi. Yayi kokarin shafe addinin musulunci da shafi sunan manzon Allah (s) hatta a cikin kiran sallah amma ya kasa.

Mu’awiya a cikin lokacinda ya karbi shugabancin musulmi zuwa zuwa mutuwarsa kimani shekaru 20 daga baya, ya yi kokarin maida al-amura al-amarin Jahiliya. Sai dai ya kasa cimma gurinsa.

Mai littafin ‘Sulhun Imam Al-Hassan’ Imam Kashiful Ghida, amfanin sulhun Imam Al-Hassan da Mu’awiya da ya takaita da bayyana hakikanin mu’awiya dan Abusufyan bayan ya sami iko ga musulmi da ya wadatar.

Kafin mu bayyana ayyukansa wadanda ya bakanta tarihin addinin musulunci da su, bari mu dubi su waye, iyayensa? Wadanda ya gaji bakar kiyayya ga addinin musulunci da musulmi a wajensu.

Abu Sufyan mahaifin Mu’awiya yana daga cikin makiya addinin musulunci da musulmi, musamman manzon Allah (s), kafin ya mika kai kuma bayan ya mika kai ga manzon Allah (s) a Fatahin Makka.

Da farko shi ne ya jagoranci yaki mafi girma wanda mushrikan makka da kawayensu suka farwa manzon Allah (a) da shi wato yakin Ahzab. Kafin haka manzon Allah (s) ya kashe da dama daga cikin danginsa a yakin Badar. Sannan shi ne ya jagoranci yakin Uhud inda aka kashe musulmi kimani 70, daga cikinsu har da ammin manzon Allah (s) Hamza dan Abdulmuttalib.

Banda haka Abusufyan ne yake taimakawa yahudawa a yakar manzon Allah (a) a duk tsawon rayuwarsa.

Sannan yana matukar kin manzon Allah (s) saboda ya kashe danginsa da dama a yaki na farko a musulunci, ya kashe mutane 70 a yakin Badar daga cikin har da danginsa banu Umayya. Saboda wannan Abusufyan yana kin manzon Allah (s) da kuma addinin musulunci har zuwa fatahin Makka, inda ya shiga hannun manzon Allah (a) aka kawoshi a gabansa, da aka matsa masa ya yarda cewa babu abin bauta da gaskiya sai Allah amma yaki ya yi Imani da manzon Allah(s) kan cewa shi manzon Allah ne. sai da namma aka yi masa barazana sai yace ya yarda. Amma ayyukansa a baya sun tabbatar da cewa bai yi Imani da manzon Allah (s) a matsayin annabi manzon Allah ba. Saboda haka ne aka sanya shi cikin mu’allafatu Qulubuhum. Wadanda ake rarrashinsu su tabbata a cikin musulunci. Allah ya ware masu kaso mai yawa a zakka.

Manzon Allah (s) ya bawa Abusufyan rakubi 100 bayan yakin Hussain, don rarrashinsa yayi imani da musulunci. Amma rayuwarsa ta nuna cewa bai musuluncta ba. Don manzon Allah (s) yana rasuwa, ya kuma ga an sami sabani tsakanin musulmi kan wanda zai gaje shi, kuma bangare sakifa sun sami nasar sai ya je wajen Aliyu dan Abutalib (a), yana cikin halin makokin manzon Allah (a), ya fada masa cewa ta tashi ka karbi hakkinka na khalifancin da aka kwace, kuma wallah sai na cika maka madina da mayakan da zasu  taimaka maka a kan Abubakar.

Sai Imam Ali (a) ya dube shi yana, cewa ka dade kana Kaida ko kuma sharri wa musulunci da musulmi, kuma baka gushe ba. Ko kamar yadda ya fada.

Sannan ya ce masa banaso. Don ya san cewa Abusufyan na neman duk wata dama da wargaza dukkan abinda manzon Allah (s) ya gina, a koma jahilaya kamar yadda take kafin musulunci.

A  nan Abusufyan yana son a tada yayin basasa a cikin al-ummar musulmi sannan shi kuma tare da sauran makiyan addinin musulunci kamar daular Roma a lokacin su kawo farmaki su nika musulmi da musulunci a Madina su kawo karshensa tun bai kai ko in aba. Amma Aliyu (a) ya fahince shi ya kuma ki amincewa da shawararsa.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169 December 13, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon  A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta December 13, 2025 Ziyarar Da Shugaban Rasha Ya Kai Indiya Ta Kara Karfafa Dangantakar Mosko Da Delhi December 13, 2025 Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na  Venuzuela December 13, 2025 Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Matatar Mai ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699 December 13, 2025 Iran da Rasha sun jaddada aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu December 13, 2025 Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai December 13, 2025 MDD ta amince da kudurin da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agaji a Gaza    December 13, 2025 Benin ta fitar da sammacin kama dan fafutuka Kemi Seba December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Imam Al Hassan ya wadanda suka Mu awiya da kamar yadda

এছাড়াও পড়ুন:

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa

Jam’iyyar PDP a ranar Alhamis ta tabbatar da mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.

Jam’iyyar ta tabbatar da rasuwar ce a cikin wata sanarwa da sakatarenta yada labaranta na kasa, Kwamared Ini Ememobong, ya fitar.

Rahotanni sun ce Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa da ke gidan gwamnati, Yenagoa, a ranar Alhamis, inda aka garzaya da shi zuwa Cibiyar Lafiya ta Ƙasa (FMC) da ke Yenagoa.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis.

An haifi Ewhrudjakpo ranar ranar biyar ga watan Satumban 1965, a ƙauyen Ofoni da ke Ƙaramar Hukumar Sagbama, Jihar Bayelsa. Ya rasu yana da shekaru 60.

Kodayake ba a san ainihin dalilin faɗuwarsa ba, majiyoyi sun ce ya faɗi ne ba zato ba tsammani yayin da yake gudanar da ayyukan ofis, lamarin da ya sa dogarai da ma’aikatansa suka yi gaggawar taimaka masa.

Wasu majiyoyi da ke kusa da marigayin sun nuna cewa mutuwarsa na iya zama sakamakon bugun zuciya.

Lamarin ya haifar da ɗan tashin hankali a gidan gwamnati da kuma fadin Yenagoa, inda mazauna garin suka nuna damuwa game da mutumin da suke kira da “Mataimakin Gwamna Mai Aikin Dare.”

Sun ce sau da yawa yana yin aiki har dare ba tare da hutu ba.

A lokacin da ake rubuta wannan rahoto da yammacin jiya, gwamnatin Jihar Bayelsa ba ta fitar da wata sanarwa ba a hukumance a kan lamarin.

Kazalika, da mai taimaka wa mataimakin gwamnan kan yaɗa labarai, Doubra Atazi, da kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ebiuwou Koku-Obiyai, sun ƙi yin bayani lokacin da aka tuntube su.

Sai dai a cikin sanarwarta, PDP ta bayyana kaduwa da alhini kan rasuwar mataimakin gwamnan, tana bayyana shi a matsayin “amintaccen ɗan jam’iyya kuma mai gaskiya.”

Sanarwar ta ce: “Jam’iyyar PDP ta kadu matuƙa da labarin rasuwar Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa kuma ɗan jam’iyya mai aminci, Mai Girma Sanata Lawrence Oborawharievwo Ewhrudjakpo, wanda rahotanni suka ce ya faɗi ya rasu a yau.

“Wannan labari mai tayar da hankali ya jefa Kwamitin Zartarwa na Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, SAN, da kuma dukkan mambobin jam’iyyarmu mai girma, musamman mambobinmu masu aminci a Jihar Bayelsa, cikin baƙin ciki mai yawa.

“Tun yana raye, Sanata Ewhrudjakpo ya kasance ɗan siyasa mai gaskiya da daidaito wanda ya yi siyasa bisa ƙa’ida. Mutum ne da ya yi tsayin daka, jagora ne wanda rayuwarsa ta ta’allaka da imani, gaskiya da ƙarfin hali. Ya tsaya tsayin daka kan waɗannan dabi’u har zuwa ƙarshe.

“Muna cikin baƙin ciki matuƙa da rasuwar wannan jarumin siyasa mai gaskiya, kuma muna roƙon Allah ya ba shi hutu na har abada. Muna mika ta’aziyyarmu ga gwamnati da al’ummar jihar Bayelsa kan wannan babban rashin da ba za a iya maye gurbinsa ba.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Rashin Bincike Ke Haifar Da Yawaitar Mutuwar Aure
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169
  • ’Yan sanda sun ba da tabbacin isasshen tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Borno
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
  • Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa
  • Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka
  • Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila
  • Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky