2025-12-12@09:51:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 41

«Sai Annabi SAW»:

    Wata rana, Abu Huraira (RA) yunwa ta kama shi matuka, har yazu wurin mimbarin Annabi SAW da ke cikin masallacin Annabi, sai ya fadi a wurin, duk wadanda suka zo wurin suka ganshi, sai suce Allah Sarki, wane ba shi da lafiya har sai da Annabi ya zo ya ganshi, sai yace masa, Abu Hurairah kana jin yunwa ko? Sai ya amsa da eh. Take Annabi SAW ya ce masa, biyo ni zuwa daki na. Annabi yasa aka kawo masa nono a dan koko kamar yadda aka saba, Abu Hurairah yana jira a ce masa ya sha, sai Annabi SAW ya ce masa ya kira ‘yan uwansa Ahlul suffati, kuma jama’a ne masu yawa, da isowarsu, Annabi SAW ya sa...
    Annabi (SAW), shi ne farkon wanda kasa za ta tsage wa ya tashi a ranar Alkiyama, shi ne farkon wanda zai shiga Aljannah, shi ne wanda Allah ya kebanta da tsani da wasilah, shi kuma ya kebanci muminai masoyansa da ita. Allah ya girmama Manzon Allah (SAW) da abin da bai girmama wani dan Adam da shi ba. Ya daukaka ambatonsa, ta inda ya hada sunansa da sunan Annabi (SAW). Indai an kira sunan Allah, sai an kira sunan Annabinsa. Allah ya yi masa budi (Fatahi) na Zahiri – Sulhu a Hudaibiyya, Fat’hu Khaibara, da Fat’hu Makkah; da Badini – Fatahi a Sifa, Fatahi a Suna da Fatahi a Zati. Allah ya gafarta wa Manzon Allah (SAW), ya tafiyar da...
    Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna...
    Idan ka duba tarihin duniya gabadaya da tarihin annabawa, tarihi ne na wayewar duniya tun daga Annabi Nuhu (S.A.) har zuwa Manzon Allah (S.A.W.) kamar duniya tana ‘yar makaranta ce ta fara da Nazare, ta zo Firamare zuwa Sakandire har zuwa Jami’a, sannan aka yaye ta, yanzu da zuwan Manzon Allah an yaye duniya, yanzu duniya ba ta bukatar sai an aiko annabi, ba ta bukata sai an aiko ma’aiki, a’a wanna abu da Manzon Allah ya zo da shi za mu iya kafa dalili da shi mu shirya kanmu ba sai da annabi ba. Wannan abu da Manzon Allah ya zo da shi yanzu ya kafa dalili da shi, da shi muka karantar da kanmu ba sai da Annabi...
    Manzon Allah (S.A.W.) yana da tunani mai zurfi, tunanin nan har ya shigar da shi duniyar tunani, duniyar tunani ta zamar masa gaskiya har yana tu’ammali da duniyar tunani, in ji mai wannan littafin masanin falsafa. Manzon Allah (S.A.W.) cikin gaskiya ya shiga ya yi tafakkuri, ya ya ibada, ya yi zikiri har ya koma asalinsa har ya haɗu da haƙiƙarsa ta Muhammadiyya (S.A.W.). Wata rana Annabi yana sallah a nan inda yake da Sahabbai, ya ce ga Al’janna ina kallo ga kuma wuta nan ina kallo, kai dai ba ka ji zafinta ba. Manzon Allah (.S.A.W.) yana da tunani mai zurfi, yana da yalwar tunani da ƙarfi, kai har abin da ƙwaƙwalwarsa take shirya masa sai ya zama gaskiya,...
    Saboda haka mu saki ilimi, mu ba ilimi hanya kar mu ji tsoro, mu je mu nemo shi duk inda yake kayanmu ne. Manzon Allah ya ce “ilimi hikima ce kayan mumini ne, saboda haka kar ka ji tsoro, ba wanda ya fi karfin Allah, ba wanda ya fi karfin Manzon Allah (S.A.W.). saboda haka ba wanda zai je ya shiga halwa ko ya shiga wani tunani ko ya shiga kaza har ya zo “summa dana fatadalla”, ba wanda zai zo nan sai dai Manzon Allah (S.A.W.). Dan haka Sufaye ba sa jin tsoron ko waye zai yi maganar ilimi, ba sa jin tsoron ko wane littafi bare damuwa, haka kuma ba a iya kada su, saboda duk abin da...
    Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki.   Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa.   Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar noma, inda ta ce, manoma mata da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da wadanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000.   Shemau ta kuma mika godiyarta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin kokarin da take yi na bunkasa noman mata a Jihar Zamfara.   Sauran hukumomin da kungiyoyin da suke tare da NAWIA...
    Ga alkawarin, komai da Allah Ya yi wa wani, Allah Ya fada. Allah bai boye komai ba, sai abin da ya yi ga Annabi Muhammadu (S.A.W.), nan ko ba a fada ba, amma kowane annabi komai matsayinsa in ka duba sai ka ji sirrin da aka yi da shi. Yanzu game da wannan ma’aiki da annabawan da duk Allah ya tara su, ga abin da Allah Ya ce (ya ku) Annabawa, idan na ba ku littafanku da kyawawan dabi’u da hikima da ma’arifanku (ai, misali, an ba ka wukar yanka da takobin yanka da tagwayen masu ke nan). Sannan wani ma’aiki ya zo maku (Manzon Allah ake nufi) za ku bar wannan sakon da wannan nadin da na yi maku...
    Kudubi yana tare da kwayar zarrar kowace halittar Allah, shi yake isar mata da sakon magana, wanda bai zauna da wadannan mazaje ba sai ya ji magana ce mai girma, sai ya ga kamar an maida shi Allah, ya ce mai aka bar wa Allah ragowa, abun ba haka yake ba, abun mammaki da mai fadar wannan yana da wayewar da yake ganin fina-finai na Turawa, da ya ga wannan magana kai-tsaye a sarari. Misali a kan Kudubi, Turawa suna da wani fim da suke shiryawa na Dirakula (Dracula) wani mai shan jini, abun kamar tatsuniya ce suke shiryawa, amma wani ya ce an yi fada ne da Daular Usmaniyya, wato daular Turkiya, akwai abubuwa da ya ba su tsoro...
    Duk wani bangaren wayewa da kimiyya da fasaha za ka ga asali malaman Musulunci ne suka zo da shi, babu lokaci isasshe da mun kawo misalai masu yawa. yana daga cikin wayewar nan: tashi a sama zuwa duniyar wata, da duk “technology” din nan na zamani, harkar zane-zane, kade-kade, bushe-bushe. Amma duk aka kwashe wadannan aka bar mu sai dai halal da haram kawai! Su ma din an hana ma halal din gurbin ta, ba mu da wata magana sai dai haram! Da a ce malamai biyar za su taru, to za ka ga ba za su kago komai ba sai haram. Amma sauran malaman kasar Turai kuwa da zarar sun hadu sai ka ga sun kago wata sabuwar kira,...
    Sai yace “A’a ba haram ba ne, kawai dai mutanena ba su san shi ba ne.” Annabi (SAW) ya taɓa cewa kar a ci tafarnuwa a shigo masallaci, aka tambaye shi: “Ya Rasulallah haram ne?” Sai ya ce “A’a ba na haramta abin da Allah bai haramta ba, kawai dai ni ne ba na son shi”, ka ga bambancin ladabin malamai na wancan zamani da na yanzu, a yanzu duk abin da wani Malami ba ya so sai kawai ya haramta shi. Amma duk inda Allah ya ce “hurrimat…” To wannan na Azal da Abadan ne. Kuma dokokin ko wace ƙasa za ka ga duk abubuwan da Allah ya haramta a Alƙur’ani ɗin nan guda 38 su ma sun haramta...
      Wanna taro yana da matukar muhimmanci, taro ne na murnar Annabi SAW, taro ne da haka Halitta ta saba. Duk al’umma tana farin ciki da murnar haihuwar wani mai girma acikinsu, ko wani wanda ya kawo musu cigaba ta hanyar rayuwa ko cigaba ta hanyar kasarsu ko kowa ma yana murnar ranar haihuwarsa, kamar yadda Annabawa suka yi murnar ranar haihuwarsu. Ubangiji tabaraka wata’ala ya yi murnar ranar haihuwar Annabi Yahya AS (wasalamun alaihi yauma wulida wa yauma yamutu wa yauma yub’asu hayya – Aminci ya tabbata a gare shi (Yahya), ranar da aka haifeshi, da ranar da zai koma ga Ubangiji da ranar da za a tashe shi da rai). Annabi Isa AS kuwa, da kanshi ya yi...
    Ƙungiyoyin Musulmi maza da mata da ƙananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira). Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Khalifofin mazhabobin Darikun Tijjaniyya da Ƙadiriyya a Ibadan su ne suka jagoranci manyan malaman addinin Musulunci tare da dimbin mabiya wajen yin tattaki na tsawon kilomita 10 da ya zagaya wasu sassan birnin domin nuna farin ciki da murnar wannan rana. An ga ƙungiyoyin Musulmi daban-daban masu halartar zagayen Maulidi sanye da sutura iri ɗaya (amko) suna rera...
      “Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW).   “Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW).   “Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da mu zuwa ga kyawawan ɗabi’u, halaye da ayyuka.   “Ya kamata mu yi amfani da irin waɗannan muhimman lokuta na addini domin mu dage da addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Zamfara, Arewa maso Yamma, da ƙasa baki ɗaya.   “Allah (T) ya kawo mana ƙarshen ta’addanci da duk wani nau’in aikata laifuka a cikin al’ummarmu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    To Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, a matsayin aike shi ne karshe, shi ya zo da aike na karshe, wanda daga shi aiken Allah (Tabaraka Wa Ta’ala) ya kare. Sai dai na Manzon Allah (SAW) din nan ne za a yi ta bincikawa a yi ta gani saboda na Manzon Allah din nan yanzu ya dace da kowanne zamani. Ubangiji Tabaraka wa Ta’ala shi ne mai cikakken ilimi, shi ya halicci ilimi ma. Allah shi ne farko kanta, shi ne karshe kanta, shi ne a sarari kuma shi ne a boye, ma’ana ya san komai ciki da bai, don haka a wannan matsayi nasa ya zuba ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam wannan ilimai a cikin wannan littafi...
    Ƙungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini. Ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai a Jihar Kwara da wasu sassan Yammacin Najeriya sun shiga ce-ce-ku-ce saboda irin waɗannan kalamai a jan sahabban Annabi (RA). NASFAT ta ce addinin Musulunci ya umarci a yi biyayya ga Allah da Manzonsa (SAW) tare da girmamawa da ƙaunar sahabbai baki ɗaya. Sanarwar da kakakin NASFAT, Alhaji Shamsideen Owolabi Oseni, ya fitar ta ce,“Sahabbai ne suka fara yaɗa addinin Musulunci, suka kare shi, suka...
    Idan aka dubi wannan, bai kamata a riƙa ɓata karatu ana cewa Masallaci ne za a ziyarta amma ba Annabi (SAW) ba. Ya kamata a gyara karatu, a gyara wannan fahimtar. Saboda irin wannan fahimtar ce ta haifar da a zamanin nan an samu rashin girmama Manzon Allah (SAW) har aka dasa bom kusa da shi. Ko ɗaga murya Allah ya hana a yi a gaban Annabi (SAW), to ina ga tada bom? A huɗubar sallar Idil Fiɗir da Limamin Makka ya yi a Harami, ya ce Yahudawa ne suka tada bom ɗin, amma sai ga shi da Saudiyya ta nuna wanda ya yi abin, da sunanshi da kamanninsa har da dogon gemu, ɗan ƙasar ne mai iƙirarin bin Salafiyya...
      Hikimar Rashin Hade Farkon Shekarar Musulunci Da Tarihin Manzancin Annabi (SAW) Masu karatu har yanzu dai muna kan bayani game da abubuwan da suka sa Sahabbai ba su kafa tarihin kirgen shekarar musulunci ba da wasu manyan alherai na Musulunci, sai suka zabi Muharram ta zama farkon shekarar tare da lakaba mata shekarar Hijirah. A makon da ya gabata mun yi bayani kan hikimar ware farkon shekarar daga watan Rabi’ul Auwal zuwa watan Muharram saboda girman haihuwar Manzon Allah (SAW). A yau kuma, za mu ci gaba da bayani a kan ware kirgen farkon shekarar daban da ranar da aka fara aiken Manzanci ga Annabi (SAW). Tun ana sauran shekara uku Manzon Allah (SAW) ya cika shekara 40 da...
    Ba laifi idan an yi murna ta shigar sabuwar shekarar Musulunci. Ba za a bi na wadanda za su bidi’antar da abin ba, domin hatta murnar haihuwar Manzon Allah (SAW) sun ce bidi’a ne. Har kai kanka ma za su iya ce maka bidi’a, saboda ba ka zo a zamaninsa ba. Masu wannan fahimtar Malamai sun ce ba wai suna nufin a koma wa Sunnar Manzon Allah ba ne, suna so ne a koma wa zamanin Annabi (SAW), ka ga ke nan sai mu ajiye su motoci da sauran kayan kere-kere na fasaha sda ake amfani da su yanzu har da su lantarki da su jirgin sama duk a ajiye, a koma amfani da su rakuma da dawaki da jakuna....
    Lallai wannan kalanda ana ce mata ta Musulunci; gaskiya ne, ta Musulmi ce tsantsa sannan kuma ta duk halitta ce domi duk halitta suna amfani da wannan, ko sun sani ko ba su sani ba. Sai dai kawai, mu a cikin ibadojinmu Addininmu Balarabe ne kuma Larabawa da wata suke yin kirgensu, kuma shi ne ya dace da halittar Dan Adam, mun gode Allah. Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, a bana idan Allah ya kai mu watan Rabi’ul Auwal maulidin da za a yi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa. Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki...
    Ibn Baddalu ya ce “Kamshin Madina ya ninka na ko ina”. Imamu Malik (RA) ya yi fatawa a yi wa wani mutum da ya ce kasar Madina lalatacciya ce bulala 30 kuma a kulle shi a kurkuku. Sai aka ce ma sa wannan mutumin babba ne fa? Sai ya ce “Ai ba bulala ya dace a yi ma sa ba, a daki wuyarsa kawai.” Ma’ana a kashe shi. Akwai sabani a kan wadda ta fi daraja tsakanin Makka da aka haife shi (SAW) da Madina wadda ya yi Hijira kuma ya rasu a can. Ko wacce akwai Sahabbai da Malamai da suka goyi bayan fifikonta. Amma a wurin mu Malikawa, Madina ta fi daraja. Sannan da Malikawan da sauran malaman...
    Hadisin Aikin Hajjin Annabi (SAW) ya koyar da cewa sumbantar Hajrul As’wad yayin da aka shiga Ka’aba da kuma sake sumbantarsa yayin fita sunnah ce, amma idan mutum bai samu iko ba; ya yi sumbar ta hanyar nuni da hannu. Hadisin ya kuma nuna mutum zai je ya yi Safa da Marwa. Zai fara da Safa kamar yadda Annabi (SAW) ya yi. Mutum zai hau kan Safa har sai ya ga dutsen, da yake sun rufe shi da gilashi sai a matsa kusa da shi. Idan ya yiwu sai a kalli Ka’aba a ambaci Allah, sannan a yi addu’a. Za a maimaita haka sau uku. Idan mutum ya iya, ya ce “Subhanallahi wal-Hamdulillah wa La’ilaha’illallahu wal-Lahu akbar. La’ilaha’illallahu wahdahu lashariyka...
    Malamai sun yi bayanin cewa a cikin wannan Hadisin akwai hukunce-hukuncen Aikin Hajji sama da guda 100 a ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sannan Annabi (SAW) ya ce “Babu wata rana mafificiya a wajen Allah kamar Ranar Arfa”, haka nan kuma ragowar kwanakin da ke cikin 10 na farkon watan nan, Ranar Arfa ta ninninka su falala. Don a wannan ranar ce Annabi (SAW) ya ce Ubangiji yana sauka zuwa saman duniya (Kamar yadda ya dace da Shi (SWT). Ire-iren waɗannan Hadisan ne ake ce musu “Mutashabihai”. Ana kawo bayanansu ne ta yadda za a yi mana kwatance amma ba kamar yadda ma’anar lamarin yake a hulɗar da ke tsakaninmu ba. Wajibi ne yin imani da Hadisan don rashin yin imani da su ridda ne, amma ba kuma a riƙa fassarawa da yadda ƙananan ƙwaƙwalenmu ke ɗaukawa ba. Duk wanda ya ce zai...
    Na zauna da Manzon Allah (SAW), na zauna da Sayyidina Aliyu, na zauna da Sayyidina Hassan da Hussaini, na zauna da Sayyidina Aliyu Zainul-Abidina (Babanka), don haka tambayi duk abin da kake so.” Shi (Jabir) makaho ne a lokacin, ina cikin tambayarsa kenan (in ji Ja’afarus Sadik) sai lokacin sallah ya yi, sai ya tashi a cikin wani dan mayafi da ya daura kuma ya yafa. Amma saboda kankancinsa duk lokacin da ya jefa shi a kafada sai ya fado alhali kuma ga babban mayafinsa a rataye a kantarsa. Sai ya yi mana sallah. Bayan gamawa na tambaye shi ya ba ni labarin Hajjin da Annabi (SAW) ya yi na karshe. Sai (Jabir) ya yi ishara da hannunsa tare da...
    Ma’anar addu’ar ita ce, “Allah ina neman tsari da kai, ya Ubangiji mai girma, da hasken fuskarka (yadda ya dace da shi) mai girma, da sarautarka dauwamammiya, daga shaidani abin jefewa, da sunanka Allah, Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad (SAW) da ‘ya’yan gidansa, ka yi aminci a gare shi. Allah ka gafarta mun zunubina, Allah ka bude mun kofofin rahamarka.” Ba a Harami ba kawai, a kowane Masallaci an so a karanta daga kan salatin Annabin nan zuwa karshen addu’ar idan za a shiga. Idan mutum bai iya wannan addu’ar ba, ya yi a’uziyya da bisimillah da salatin Annabi (SAW) da kuma addu’ar da ya iya. Ana so da zarar mutum ya shiga idanunsa sun kalli Dakin Ka’aba,...
    Amma an fi so a yi da Rakumi ga wanda yake da iko. A Aikin Hajji, an fi son yawan nama sabanin Layya da aka fi son nama mai dadi da kitse. Shari’a ta yarda mutum bakwai su hada kudi su sayi Rakumin hadaya guda daya. Idan Alhajin da hadaya ta hau kansa bai samu dabbar da zai yi ba, sai ya yi azumi na kwana uku a Makka kafin a fita zuwa Arfa idan zai yiwu. Idan bai samu dama ba sai ya yi bayan Arfa kafin ya bar Makka. Bayan ya dawo garinsu, sai ya yi sauran azumin kwana bakwai. Jimillar azumin kwana 10 ne yake madadin hadayar da bai yi ba. Amma kuma kar ya zama Alhaji...
    A wurin mu Malikawa, mun dauki watannin nan guda uku a matsayin lokacin Hajji, wasu kuma sun ce a’a, daga kwana goman farkon nan na Zhul-hijja, lokacin ya kare, to amma kuma idan aka yi la’akari za a ga cewa akwai sauran ibadodin Hajjin da suka shige wadannan kwanakin goma irin su Jifa da ake dawowa Mina a yi bayan Sallar Idi da Dawafin bankwana. Shi ya sa Malikawa muka dauki watannin ukun baki daya a matsayin lokacin Hajji. Kuma Ibn Hazan ya goyi bayan haka, don ba za a dauki wata biyu da kwana goma a ce musu watanni uku ba.   Kamar yadda bayani ya gabata, Hajji ba a ko ina ake daura haramar yin sa ba, yana...
    –Ya Kamata Malamai Su Karfafa Zamantakewa Ta Wayewar Musulunci A Duk Inda Musulmi Suke   Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh, ya Shehunmu da sauran daukacin Bayin Allah, muna mika sakon gaisuwa da kuma ziyara ta ‘yan’uwantaka ta Musulunci a dukkanin matakai da Annabi (SAW) ya zo mana da shi na Musulunci da Imani da kuma Ihsani. Bayan haka, muna godiya da irin bayanin da aka yi mana a karatunka na Tafsiri na rana ta 11 a game da muhimmancin karfafa zamantakewa ta wayewar Musulunci a tsakanin Musulmi a duk inda suke. Tabbas, lokaci ya yi da masu wa’azin Musulunci ya kamata su daina kafa hujjar yaki da ayoyin Surar Bara’a a wuraren da ba su dace ba, domin akwai...
    A yayin da muka kammala watan azumin Ramadan, muna gabatar da wannan fadakarwa kan abubuwan da suka kamata mu yi da wadanda za mu guje musu a wannan rana ta farin ciki ta Sallah kamar haka: Zakkar Fidir: Zakatul-Fitr ko Zakkar Fid-da-Kai, ita ce sadakar da ake fitarwa a karshen azumin watan Ramadan. Sunnah ce wajiba a kan kowane Musulmi namiji da Musulma mace, babba da yaro, da da bawa, ana so ya fitar da ita ko a fitar masa kafin zuwa Sallar Idi. Kuma ya halatta a fitar da ita kwana uku ko biyu ko daya kafin ranar Sallar Idi Karama don a ba fakirai da miskinadamar sarrafawa su yi farin ciki a ranar Idin. Mai gida zai fitar...
    Shi wannan azumi, na wani lokaci ya fi na wani lokaci kamar an so a dinga yin azumi sau Uku a cikin kowanne wata, lokacin kwanan wata yana 13 da 14 da 15, wannan kwanaki hasken wata ya fi haske a cikinsu, to kamar yadda suke haske haka zuciyarka za ta kara haske sabida saduwa da hasken, sannan kuma hawa-hawa na musulunci guda Uku ne (Islam da Iman da Ihsan) to wanda ya riski wannan kwanaki Uku kamar Ya hau dukka wannan Matakan addinin ne. Akwai azumin Litinin da Alhamis, azumin ranar Litinin Annabi (SAW) ne yake yi, an tambaye shi cewa Ya Rasulullahi sabida me kake azumin ranar Litinin? sai ya ce ranar ce aka haife ni, ina godiya...
    Takawa ta kebantattun kebantattu: sun hada duk abin alkairi na gama-garin mutane, sun hada duk abin alkairi na kebantattu sannan sun kara da nutso da zurfafawa cikin sanin Allah, ba su ganin wanin Allah, a ko da yaushe suna Fadar Allah ko suna Fadar Annabi (SAW) ko suna fadar Waliyyan Allah. Wadannan Takawa guda Uku, Allah ya fada mana su cikin Alkur’ani yana cewa : “Ba laifi ga wadanda suka yi imani da Allah suka yi aiki mai kyau cikin abin da suka ci, idan suka yi takawa suka yi Imani, sannan suka yi wata takawa kuma suka yi Imani sannan suka yi wata takawa sannan suka yi kyautaye.” Ayar ta sauka ce lokacin da ayar haramta giya ta sauka,...
      Jinkirta Sahur Da Gaggauta Buda-baki An karba daga Anas, ya ce, Annabi SAW ya ce “ku dinga yin Sahur, domin shi yin Sahur akwai albarka a cikinsa”, ba burgewa ba ce mutum ya dinga cewa ‘ai ni ban yin sahur’ albarka mai yawa ta wuce shi. An karba daga Sahlu dan Sa’adu Allah ya kara yarda da shi ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce “Mutane ba za su gushe ba cikin alkairi muddin sun gaggauta yin buda-baki” Ma’anar wannan hadisi, sabida Allah ya fada cikin Alkur’ani “summa atimmus siyama ilallai – sannan ku cika azumi zuwa dare” sai Annabi ya koya mana sunnarshi zuwa dai-dai lokacin da ya dace na buda-bakin (ba cikin dare Allah yake nufi ba),...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta DAWN mai hedkwata a birnin Washington ta yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC da ta binciki rawar da tsohon shugaban Amurka Joe Biden da wasu jami’an Amurka suka taka wajen taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza. A bukatar da aka mika wa mai gabatar da kara na kotun ICC Karim Khan a ranar 19 ga watan Janairu, 2025, wacce ta bayyana a ranar Litinin, kungiyar mai zaman kanta ta Democracy Now for the Arab World (DAWN) ta zargi Biden, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, da sakatarensa na tsaro, Lloyd Austin, da taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar kungiyar mai zaman kan ta,...
    Annabi (SAW) yana da Alfadarai Bakwai, akwai wazanda ya rike har ya rasu suna wurinsa akwai kuma wazanda ya bai wa wasu daga cikin sahabbansa. Wacce ya je yakin Hunaini da ita, wani sarkin Larabawa (zan makafatul kinani) ne ya bashi, akwai wacce sarkin Ailatu ya bashi akwai ta sarkin Limatul Jandali, akwai ta Sarki Najjashi, akwai ta sarkin Kisra, akwai ta sarkin Mukaukisu akwai Jindilu. Jindilu itace mashhuriya wacce Annabi ya rasu ya bar ta Sayyidina Aliyu ya ci gaba da hawanta, duk yakukuwan Sayyidina Ali, mafi yawancinsu a kanta ya yi, ranar yakin Wak’atu Jamal, Sayyada A’isha (RA) ta ganshi a kanta, sai ta ce “ya yi kama da zan’uwansa” sai mai rike da akalar rakuminta ya jefar...
    Annabi (SAW) a cikin dukkan kyawawan halaye ba a kamanta shi da kowa. Jabir dan Abdullahi (RA) yana cewa, ba a tava tambayar Annabi (SAW) da wani abu ba ya ce babu. Abdullahi dan Abbas (RA) yana cewa “Annabi (SAW) ya kasance mafi baiwar Mutane da alkairi, lokacin da Annabi ya fi baiwa, shi ne lokacin watan Azumin Ramadana, ya kasance idan ya hadu da Mala’ika Jibrilu, Mala’ika Jibrilu yana zuwa suna Musaffan Karatun Alkur’ani da Annabi (SAW) duk watan Ramadana sau daya, sai shekarar wafati ce suka yi sau biyu. Shi ya sa, duk musulmai suna da baiwa da kyauta amma in watan Ramadana ya zo sai ka ga sun kara ninkawa. An karvo hadisi daga Anas khadimin Manzon...
    In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba. Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya...
    Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba. Ita kuma juriya cikin dauke bala’o’i, ita ce tsare rai cikin rashin damuwa lokacin da ake cikin tsananin damuwa, mutum ya nuna kamar abu bai faru ba. Ita kuma yafiya ko rangwame, ita ce barin ramuwa ga wanda ya yi maka ba daidai ba. Dukkan wadannan halaye, suna daga cikin wadanda Ubangiji ya ladabtar da ma’aikinsa (SAW) da su. Ubangiji yana fada masa a cikin hakkinsa...
    Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara 40. Babbar manufar gudanar da wannan biki ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah Nuhammad (SAW), wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci. Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al’ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci...
۱