Aminiya:
2025-12-11@14:45:17 GMT

Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe

Published: 11th, December 2025 GMT

Wani mutum ya mutu, wasu da dama kuma sun jikkata lokacin da wata tirela ta yi karo da wata mota ƙirar akori kura Mitsubishi Canter a Damagum da misalin ƙarfe 12:50 na tsakar dare a ranar Laraba.

Kamar yadda kakakin rundunar ‘Yan sanda Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ya ce tirelar, mai lambar rajista MUS 791 XH, wacce Aliyu Muhammad, mai shekara 30, daga Azare, ƙaramar hukumar Katagum, Jihar Bauchi ke tuƙawa tana tafiya daga Damaturu zuwa Legas lokacin da motar ta kufcewa direban ta afka wa motar da ke gabanta.

Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige

Motar, mai mutane 18 da ke ciki da lamba AA 641 PKM, wadda Usman Muhammad, mai shekara 40 daga ƙauyen Yaskawel ne ke tuƙa ta.

Mai magana da yawun rundunar ya ce, an tabbatar da mutuwar fasinja ɗaya, Ɗahiru Maikuɗi mai shekara 40, daga ƙauyen Yaskawel, a babban asibitin Damagum yayin da wasu da dama suka jikkata.

A cewar rundunar, an tura waɗanda abin ya shafa shida zuwa asibitin Koyarwa da ke Damaturu don ƙarin kula da lafiyar su.

Hatsarin ya haifar da zanga-zanga daga matasan Damagum waɗanda suka koka game da yawan haɗurra a kan babbar hanyar Damaturu zuuwa Potiskum, musamman kusa da Damagum inda ake harkokin kasuwanci da zirga-zirgar masu sufuri a ƙasa ke ƙaruwa musamman a ranakun Lahadi da Laraba.

Jami’an ‘yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar don hana cin zarafin da ake yi wa mutane.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar, Emmanuel Ado ya yi wa iyalan wanda ya rasu ta’azɗiyar rashin mamacin ya jajantawa waɗanda suka jikkata yayin wannan hatsari  yana mai umurtar Jami’in ‘yan sandan yankin da ya yi aiki tare da ƙaramar hukumar kan matakan kariya na dogon lokaci.

Ya gargaɗi masu ababen hawa game da yin gudun wuce ƙima kuma ya yi kira da a bi ƙa’idodin zirga-zirga sosai, yana mai gargaɗin cewa, waɗanda suka karya doka za su fuskanci hukunci.

Kwamishinan ya kuma shawarci mazauna yankin da su guji yin harkokin kasuwanci kusa da babbar hanyar don rage ƙarin faruwar haɗurra.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Kamfanin Mangal ya kori direba kan dauko yara 21 da aka kama a Kogi

An kori direban Kamfanin Simintin Mangal bayan jami’an tsaro sun kama shi da motar kamfanin dauke da yara 21 da ake zargin an yi safarar su ne daga jihohin Arewa.

Gwamnatin jihar ta ce yaran da ke tsakanin shekaru 6 zuwa 17 an kama su ne bisa sahihan bayanan sirri.

Sanawar da Kwamishinan Yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar bayan kama yaran a cikin motar ta yi zargin za a yi amfani da su wajen horar da ’yan ta’adda.

Kamfanin ya nesanta kansa daga lamarin, ya ce direban ya karya dokokin aiki, kuma ya jefa al’umma cikin haɗari.

Yara masara zuwa makaranta barazana ne ga kasa — Shettima Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashenta

Babban Manajan sashin kula da mulki na kamfanin, Musa Umar, ya ce ba da izininsa direban da aka kama ya fita da motar ba, domin iya jigilar siminta kaɗai suke yi ba ɗaukar fasinja ko yara ba.

Gwamnatin Kogi ta ce za a mika yaran ga gwamnatocin jihohinsu bayan tantancewa, yayin da duk wanda aka samu da hannu a safarar zai fuskanci shari’a bisa dokokin hana safarar yara da kare haƙƙin yara.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda za ku cike neman aikin dan sandan Najeriya na 2025/2026
  • Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudinta a Gaban Majalisa
  • Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
  • An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara
  • ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu
  • DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • Saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya soya qwaqwalwarta 
  • Kamfanin Mangal ya kori direba kan dauko yara 21 da aka kama a Kogi
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato