’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu
Published: 18th, September 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama wasu mutane tara da ake zargi da shirin yin garkuwa da kansu tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 7.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce waɗanda ake zargin na da hannu a cikin shirin zamba na Ponzi, kuma ɗaya daga cikin tawagarsu ya shirya da wanda ake zargin ya samu kuɗin fansa daga abokan aikinsu.
An kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin mai suna Suleiman Dauda a Minna babban birnin jihar, inda daga bisani ya ambaci wasu mutum takwas da ake zargin yayin da ’yan sanda ke yi musu tambayoyi.
“A ranar 2 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 10 na dare, an samu rahoto a yankin Tudun-Wada na wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane a kusa da unguwar Mandela da ke Minna, sannan kuma an kira shi ta wata baƙuwar lambar wayar salula ana neman kuɗin fansa Naira miliyan 7.
“A cikin binciken da ake yi, a ranar 3 ga Satumba 2025, an kama wani wanda ake zargi mai suna Suleiman Dauda da laifin aikata laifin, kuma bisa ga tambayoyi, an kama wasu mutum takwas a unguwar Mandela.
“A binciken da aka yi, an ƙwato katin wayar salula SIM guda 21 da satifiket 29 a hannun Suleiman, bisa zargin cewa yana yin rijistar katin SIM ne, ya kuma yarda cewa lambar waya salula da ake neman kuɗin fansa ya ba wanda aka aka yi garkuwan da shi.”
Duk da haka ya bayyana cewa, “Binciken da aka yi ya nuna cewa, waɗanda ake zargin sun fito ne daga wurare daban-daban a ciki da wajen jihar suna gudanar da shirin zamba na Ponzi, kuma an gano cewa ɗaya daga cikin tawagarsu ya shirya da wanda ake zargin ya karɓi kuɗin fansa daga abokan aikinsu.
Abiodun ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike da nufin ganowa tare da cafke wasu, yana mai cewa waɗanda ake zargin an gurfanar da su a gaban kotu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda garkuwa da mutane waɗanda ake zargin da ake zargin
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m
Wani ɗan kasuwa a Jihar Katsina mai suna Anas Ahmadu da matarsa, Halimatu wadda ke ɗauke da juna biyu, da kuma ’yarsu mai shekaru biyu, sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga, bayan sun shafe kwanaki 21 a hannunsu.
An sako su ne a daren ranar Laraba bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan 50, kamar yadda wani ɗan uwansu ya bayyana wa Aminiya.
Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?“Alhamdulillah! Anas, Halimatu da ’yarsu sun kuɓuta. Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa gida, amma sai da aka biya ’yan bindigar kuɗin fansa Naira miliyan 50,” in ji shi.
An sace su ne a ranar 26 ga watan Agusta, 2025 a gidansu da ke Filin Canada Quarters, a Jihar Katsina.
Da farko, mahafan sun nemi Naira miliyan 600, daga baya suka rage kuɗin zuwa miliyan 100, sannan daga ƙarshe suka amince aka biya su miliyan 50.
Saboda dalilan tsaro, ’yan uwansu ba su bayyana inda aka sako su ba.