Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannun kan yarjeniyoyi da dama a tsakaninsu
Published: 11th, December 2025 GMT
Kasashen Iran da Kazakhstan sun sanya hannu kan yarjeniyoyi da da dama na hadin gwiwa a tsakaninsu a wani muhimmin mataki na karfafa dangantaka a tsakaninsu.
A wani biki da shugaban Iran Massoud Pezeshkian da takwaransa na Kazakhstan, Kassym-Jomart Tokayev suka halarta, manyan jami’ai daga kasashen biyu sun rattaba kan takardun fahimtar juna 14 tsakaninsu da suka shafi sufuri da jigilar kayayyaki, al’adu, fannin shari’a, kiwon lafiya, da kuma hadin gwiwar diflomasiyya da kafofin watsa labarai.
Shugabannin sun kuma sanya hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa da ke tabbatar da alkawarinsu na zurfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu
An cimma wannan ne a yayin ziyartar da shugaban kasar Iran ya kai a Astana tare da rakiyar wata babbar tawaga.
Mr. Pezeshkian ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun nuna babban mataki kuma mai mahimmanci wajen karfafa dangantakar ƙasashen biyu.
Ya bayyana kyakkyawan fata game da kudurin Tehran da Astana na habaka ciniki da zuba jari zuwa babban mataki.
Shugaban Iran ya jaddada muhimmancin da Iran ke bai wa dangantakarta da makwabtanta.
Bayan ziyararsa zuwa Kazakhstan, shugaban Iran zai nufi kasar Turkmenistan, inda za a gudanar da taron zaman lafiya na kasa da kasa tare da halartar shugabannin kasashe da dama.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan December 11, 2025 Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka December 11, 2025 Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan December 11, 2025 ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro
Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya domin ƙarfafa dangantakar tsaro da haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu.
A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan yaɗa labarai Ahmed Dan Wudil ya fitar, ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta shafi muhimman fannoni kamar musayar bayanan leƙen asiri, horas da sojoji, haɗin gwiwa a harkar samar da kayan yaki da kuma gudanar da ayyukan tsaro tare.
Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa ’Yan jaridar Daily Trust da Trust TV sun lashe kyautar binciken ƙwaƙwaf ta Wole Soyinka ta banaMinista Matawalle ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Dakta Khaleed H. Al-Biyari ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Masarautar Saudiyya.
Ministar ya bayyana cewa, wannan ci gaban babbar dama ce da za ta ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu da kuma taimakawa wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.
Ya ce, ma’aikatar tsaron Najeriya tana maraba da wannan ci gaba, tare da fatan hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar.