Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago
Published: 12th, December 2025 GMT
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya jaddada goyon bayansa ga wa’adin mulki ɗaya kacal ga gwamnonin, yana mai cewa hakan zai inganta aiki da kuma inganta harkokin mulki.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake rantsar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin Ƙananan hukumomi, mataimakan shugabannin, Kwamishinoni da shugabannin hukumar a ɗakin taro na Hauwa Isah Wali da ke gidan gwamnati, Minna babban birnin jihar.
Bago ya bayyana cewa, saboda zaɓen 2027 ne ya hana shi ya ɗauki tsauraran matakai kan wasu jami’an idan ba don zaben da ke tafe ba, yana mai cewa tsarin wa’adi ɗaya ne zai bai wa shugabanni damar yin taka-tsantsan ba tare da matsin lamba na siyasa ba.
“Ni mai goyon bayan wa’adi ɗaya ne ga gwamnoni domin abin takaicin mun dawo kan batutuwan siyasa, komai na Najeriya cike yake da siyasa, abin takaici ne!
“Akwai abubuwan da zan iya yi a yau, amma zan yi magana ne a kai bayan zaɓe. Dole ne in sallami wasu ma’aikata da ba su da amfani, amma ba zan iya ba saboda zaɓe, sun faɗi jarabawarsu da yawa, ba za a iya yi musu ƙarin girma ba, amma nauyi ne a kan tsarin. Idan da zango ɗaya ne ake yi, da na fi yanke hukunci fiye da wanda nake a yau,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Mohammed Umaru Bago
এছাড়াও পড়ুন:
Shugabannin Sin Sun Yi Taron Koli Na Tattauna Aikin Raya Tattalin Arziki Don Tsara Abubuwan Da Za A Aiwatar A 2026
Mahukuntan kasar Sin sun gudanar da taron koli, na tattauna aikin raya tattalin arzikin kasar, don tsara abubuwan da za a aiwatar a shekarar 2026 dake tafe. An gudanar da taron ne a jiya Laraba da yau Alhamis, inda shugabannin kasar suka tantance abubuwa mafiya muhimmanci, wadanda za a aiwatar, dangane da raya tattalin arzikin kasar a shekara mai kamawa.
Cikin muhimmin jawabi da ya gabatar yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya waiwayi aikin raya tattalin arziki da Sin ta aiwatar a shekarar nan ta 2025, tare da fayyace halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, da ma aikin da aka tsara gudanarwa a shekara mai zuwa.
Yayin taron, an yi amannar cewa shekarar 2025 ta fita daban, kuma za a kai ga cimma nasarar muradun raya tattalin arziki, da zamantakewar al’ummar kasar Sin na shekarar ta bana.
ADVERTISEMENTTaron ya kuma tabbatar da cewa, aikin raya tattalin arzikin Sin na shekara mai zuwa, zai karkata ne ga ayyuka irinsu bunkasa sayayya a cikin gida, da ci gaba wanda kirkire-kirkire ke ingizawa, da kara bude kofar kasar Sin ga sassan waje, da cikakken salon sauyi zuwa ci gaba marar dumama yanayi, da kyautata rayuwar al’umma. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA