Isra’ilaTa Kashe Wani Bafalasdine Matashi A Wani Hari Da Takai A Arewacin Kogin Jodan.
Published: 14th, December 2025 GMT
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Isra’ila sun karbe wani matashi bafalasdine a wani samame da suka kai a cikin dare a wani gari dake Arewacin gabar yammacin kogin Jodan da isara’ila ta mamaye, wani mazaunin yankin yace sojojin na cin karensu ba babbaka a yankin.
Kamfanin dillancin labaran yankin falasdinu WAFA ya sanar cewa sojojin isara’ila sun bude wuta kan wani yaro matashi dan shekaru 16 da haihuwa Mohammad iyad a arewa masu yammacin garin jenin inda anan take yace ga garunku nan.
Yan sa’oi kafin afkuwar lamarin sojojin Isra’ila sun farma garin inda suka fara binciken gida-gida tare da harbe-harbe da harsashi mai rai, da kuma wurga gurneti, lamarin da ya jawo mayar da martani daga al’ummar garin,
Kungiyar bada agaji ta yankin falasdinu ta ce wani ma’aikacinta guda daya dan shekaru 30 da haihuwa ya jikkata bayan da sojan isra’ila ya harbe shi da harsashi mai rai a kafarsa kafin daga bisani aka yi Asibiti da shi domin yi masa magani.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shuwagabannin Majalisar Kasar Iran Da Na Ethiopia Sun Gudanar Da Taron Manema Labarai December 14, 2025 Ghana Ta Kori Wasu Yahudawa Guda 3 Don Mayar Da Martani December 14, 2025 Araghchi ya bukaci Amurka ta girmama al’ummar Iran da gwamnatinta December 14, 2025 Dan bindiga ya kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula a Siriya December 14, 2025 Mutum biyu sun mutu a harbin bindiga a Jami’ar Brown ta Amurka December 14, 2025 Shugabannin kasashen (ECOWAS) na taro a Abuja December 14, 2025 Kasashen AES zasu kafa bankin dogaro da kai December 14, 2025 Sheikh Na’im Kassim: Idan Duniya Baki Daya Za Ta Taru, Ba Wanda Zai Iya Kwace Makaman Hizbullah December 13, 2025 DRC: Kungiyar M23 Ta Kwace Iko Da Wani Gari Mai Muhimmanci December 13, 2025 Syria: Sojojin “Isra’ila” Sun Kutsa Cikin Yankin Qunaidhara December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe mutum 11 da jikkata wasu 29 a bikin Yahudawa a Ostireliya
Akalla mutanen 11 ne suka mutu, wasu 29 suka jikkata, a yayin wani hari da aka kai a bakin tekun Bondi Beach da ke birnin Sydney na ƙasar Ostireliya.
’Yan bindiga sun kai harin ne a yayin da dubban jama’a ne suka taru a bakin teku domin halartar wani biki mai suna ‘Chanukah by the Sea’, wanda ke nuna fara shagulgulan Yahudawa na Hanukkah.
Rahotanni sun ce wani mutum da ake zargin ɗaya daga cikin masu harin ya mutu, yayin da wani kuma ke cikin mawuyacin hali a asibiti. ’Yan sanda biyu na cikin mutanen da suka jikkata.
Hukumomin Ostireliya sun bayyana lamarin a matsayin harin ta’addanci, tare da jaddada cewa an shirya shi ne domin kai wa al’ummar Yahudawa hari a ranar farko ta bukukuwan Hanukkah.
Taɓarɓarewar rashin tsaro ya nuna rashin shugabanci na gari — Obi Akwai fargaba kan noman ranin banaFiraministan Ostireliya, Anthony Albanese, ya yi Allah-wadai da harin, tare da cewa mummunan ta’addanci da aka aikata ya wuce tunanin ɗan adam.