Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci
Published: 12th, December 2025 GMT
Tafarkin samun ci gaba mai karfi da inganci, da karuwar kuzarin kirkire-kirkire da ci gaba da fadada bude kofa, su ne suka hadu suka samar da wani sabon matsayi ga tattalin arzikin kasar Sin a taswirar tattalin arzikin duniya. Ci gaba mai inganci da fadada bude kofa, ba muhimman jigon ne dake ingiza tattalin arzikin Sin kadai ba, har da nuna yanayin sauyawar abubuwan dake haifar da ci gaba a duniya.
Karfin tattalin arzikin Sin ya dagora ne da sabon karfin samar da hajoji da hidimomi da ke samun ci gaba cikin sauri, wadda ake ganin saurin ci gabanta ta hanyar kirkire-kirkire. Nazarin ya nuna cewa, kaso 93.6 na wadanda suka bayar da amsa, sun yi imanin cewa, kirkire-kirkire na taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki mai inganci na Sin. Wasu kaso 96.6 kuma sun yi imanin cewa, kasar Sin na jagorantar manyan sauye-sauye a tsare-tsaren tafiyar da masana’antu da na tattalin arziki ta hanyar kirkire kirkiren kimiyya da fasaha.
A matsayinta na kasa ta biyu mafi yawan masu sayayya, kasar Sin ce ke da mutane masu matsakaicin kudin shiga mafi yawa a duniya, inda take da gagarumin karfin sayayya da na zuba jari. Nazarin ya nuna cewa, kaso 82.3 na masu bayar da amsu sun yi imanin cewa, kamfanonin kasashen waje za su iya amfani da fa’idojin da suke da shi wajen shiga kasuwar kasar Sin domin kara samun karfin takara a duniya. (FMM)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: yi imanin cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Australia ta Fara Aiwhatar da Dokar Hana Yara Amfani da Shafukan Sada Zumunta
A yau ne dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Ostiraliya.
Firaministan ƙasar ya bayyana dokar a matsayin abin alfahari ga Ostiraliya, yana mai cewa za ta shiga tarihi a matsayin muhimmiyar sauyi.
Anthony Albanese ya ce ƙasarsa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki.
Yara ƙasa da shekaru 16 sun tarar an rufe musu shafukansu a manyan dandanli 10 ciki har da TikTok da Snapchat.
Sai dai ko a rana ta farko, rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikinsu suna samun hanyoyin kaucewa wannan dokar.
Kamfanin Meta, mammallakin Instagram da Facebook, ya ce dokar na tura yara zuwa wasu shafuka da ba su da tsauraran dokoki.