Aminiya:
2025-12-14@21:20:02 GMT

An kashe mai ciki da ɗanta a Kano

Published: 14th, December 2025 GMT

Al’ummar unguwar Sheka Sabuwar Gandu da ke Ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano, sun shiga fargaba, bayan wasu da ba a san ko su waye ba, suka kashe wata mai ciki da ɗanta ɗan wata18 a duniya.

An tabbatar da faruwar lamarin da misalin ƙarfe 8 na dare, lokacin da mijin matar ya dawo gida daga aiki ya tarar ƙofar gidan a kulle.

Hafsan sojin ƙasa ya buƙaci sabbin dakaru su zama masu kishin ƙasa An kashe mutum 11 da jikkata wasu 29 a bikin Yahudawa a Ostireliya 

A cewar maƙwabtan matar, bayan mijin ya tambayi jama’a a unguwar, sai ya shiga gidan, inda ya tarar da gawar matarsa da ta ɗanta.

Daga nan ne al’ummar unguwar suka sanar da hukumomin tsaro.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban jama’a aunguwar, Ahmad Sani, ya ce jama’a sun shiga firgici da tashin hankali matuƙa.

Ya koka da rashin tsaro a yankin, inda ya bayyana cewa duk da gina ofishin ’yan sanda a unguwar, har yanzu ba a turo jami’an tsaro da za su kula da shi ba.

“Dukkanin al’ummar unguwar sun shiga ruɗani. Ba a taɓa samun irin wannan abu ba. Muna cikin damuwa saboda babu jami’an tsaro a nan,” in ji shi.

Ya roƙi Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, da ya ɗauki matakin gaggawa wajen inganta tsaro a yankin domin hana sake faruwar hakan.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ba zai ce komai ba domin rundunar na gudanar da bincike.

A halin yanzu, mazauna yankin sun buƙaci hukumomin tsaro su gaggauta kamo waɗanda suka aikata laifin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda matar aure yaro

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu Ta Umarci EFCC Ta Biya Wani Ƴan Kasuwar Kano Miliyan 5, Ta Nemi Afuwar Su

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Hukuncin Kisa Kan Maryam Sanda December 12, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja December 12, 2025 Manyan Labarai NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba December 12, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ECOWAS ta jaddada aniyar kare dimokuraɗiyya da inganta tsaro a yammacin Afirka
  • Tsaro: Abba ya kafa runduna ta musamman da za ta ke tsaron tashoshin mota a Kano
  • Hafsan sojin ƙasa ya buƙaci sabbin dakaru su zama masu kishin ƙasa
  • Shirin kafa ‘Hisbar Ganduje’ ya tayar da ƙura a Kano
  • Sojoji sun daƙile harin ’yan ta’adda a Borno
  • Kotu Ta Umarci EFCC Ta Biya Wani Ƴan Kasuwar Kano Miliyan 5, Ta Nemi Afuwar Su
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
  • Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano
  • ‘Sojojin Najeriya da na Ivory Coast 200 sun shiga domin tsaftace Jamhuriyar Benin’