An cire Tony Blair daga jerin wadanda zasu jagoranci Gaza
Published: 9th, December 2025 GMT
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta yi maraba da bayannan cewa an cire sunantsohon firaministan Burtaniya Tony Blair daga wadanda ake tunanin zasu jagoranci Gaza a shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump a Gaza.
Jaridar Financial Times ta ruwaito a ranar Litinin cewa kasashen Larabawa da na Musulmi ne suka nuna adawa da shigar da M.
Tony Blair ya sha suka a faɗin duniyar Musulmi saboda rawar da ya taka a mamayar da Amurka ta jagoranta a Iraki a shekarar 2003, wanda daga baya aka gano cewa kawai zarge-zargen karya ne.
Wani Jami’in Hamas, Taher al-Nunu, ya ce rahotannin yiwuwar cire Blair ya yi daidai da kiran da kungiyar ta yi ga masu shiga tsakani don hana shi shiga kowace hukuma da ke da alaka da Gaza.
A daya bangaren kuma Al-Nunu ya sake nanata cewa ƙungiyar ta kasance “a shirye don tsagaita wuta na dogon lokaci” muddin gwamnatin Isra’ila ta amince da dukkan sharuddan tsagaita wuta, wani abu da Tel Aviv ta kauce masa zuwa yanzu ta hanyar karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a farkon watan Oktoba.
Jami’in na Hamas ya kuma jaddada cewa duk wani shiri da ya shafi rundunar ƙasa da ƙasa da aka ɗora wa alhakin kwance damarar yaƙi da ƙungiyoyin gwagwarmaya da ƙarfi, “an yi watsi da shi kuma ba a taɓa tattauna shi ba.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon December 9, 2025 Trump Ya Yi Gefe Da Kasashen Turai Dangane Da Tattaunawa Kan Rikicin Ukraine December 9, 2025 Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba December 9, 2025 Najeriya : Matsala ce ta sa jirgin sojinmu yin saukar gaggawa A Burkina Faso December 9, 2025 Saudiya da Qatar Zasu Gina Layin Dogo Mai Sauri Tsakanin Kasashen Biyu December 9, 2025 Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki December 9, 2025 Pakistan ta Bai Wa Taliban Ta Aghanistan Zabi A Tsakanin Mu’amala Da Ita Ko Da ‘Yan Ta’adda December 9, 2025 Kasashen Iran Da Turkiya Za Su Bunkasa Alakarsu A Fagen Ilimi Da Musayar Fasaha December 9, 2025 An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa” December 9, 2025 Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba December 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.
Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa yana da “damuwa ta musamman” kan yadda gwamnati ta kasa daƙile ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga, rikice-rikicen ƙabilanci da kuma yaɗuwar makamai ba tare da kulawa ba.
Ya ce abin da ya fi nuna gazawar gwamnati shi ne yadda aka bar jihohi su kafa ƙungiyoyin sa-kai ba tare da horo na musamman ba, abin da ya ƙara yaɗuwar kananan makamai a ƙasar.
“Abin takaici, Gwamnatin Tarayya ta gaza. Hakan ya bayyana a yadda ta amince da jihohi su kafa kungiyoyin sa-kai ba tare da horo na kwararru ba,” in ji shi.
An kama tsohon fursuna da bindiga ƙirar AK-47 Dalilin yawaitar juyin mulki a ƙasashen ECOWASKwankwaso ya gargadi cewa wasu ’yan siyasa suna amfani da wannan dama wajen kafa kungiyoyin su na musamman, abin da ya kara jefa kasar cikin hadari.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ƙara samun wariyar ƙabilanci da yankuna, inda ya ce ’yan Najeriya musamman daga wani yanki ke fuskantar tsangwama ba bisa ƙa’ida ba, tare da cin zarafi da azabtarwa a sassa daban-daban na kasar.
“Hakan ya kara muni da yadda ake samun cin zarafi, tsangwama da maganganun ƙiyayya a kafafen sada zumunta, wanda ake cusawa da kabilanci da addini. Wannan na barazana ga hadin kan ƙasa,” in ji shi.
Kwankwaso ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa don dakatar da wannan hatsari kafin ya ƙara tsananta.
Ya ce a matsayinsa na tsohon Ministan Tsaro da kuma Shugaban Kwamitin Kula da Yaɗuwar Ƙananan Makamai, yana matuƙar damuwa da yadda makamai ke yaɗuwa cikin sauki a kasar.
Sai dai ya taya Janar Christopher Gwabin Musa murnar nada shi Ministan Tsaro, yana mai fatan zai yi nasara idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace.
“Ina da yaƙinin cewa idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace, yana da ƙwarewa da gogewa da za su taimaka wajen dawo da tsaro da zaman lafiya a kasar,” in ji Kwankwaso.