A ci gaba da al’adar fiye da shekaru 30, Ministan Harkokin Wajen Sin Wang Yi ya ziyarci kasashen Afirka da dama a tsakanin 5-11 ga watan Janairun 2025 don sake tabbatar da dangantakar diflomasiyya da kuma binciko sabbin hanyoyin hadin gwiwa. Wannan ziyarar ta sake tabbatar da manufar ci gaba da cin moriyar juna a tsakanin bangarorin biyu.

 

Baje kolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka na hudu a Changsha

An gudanar da wannan taron baje kolin na hudu daga 12 zuwa 15 ga watan Yunin bana a Changsha, babban birnin lardin Hunan. Baje kolin ya tattaro kusan kamfanonin Sin da Afirka 4,700, kuma an baje kolin kayayyakin Afirka sama da 800 daga kasashe da dama.

An gudanar da taron ne tare da bikin cika shekaru 25 na taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), wanda hakan ke jaddada tsarin ci gaba na dogon lokaci na ci gaba da huldar Sin da Afirka.

 

Fadada ciniki da katse shingen haraji zuwa sifili ga kasashen Afirka

A shekarar 2025, cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka ta ci gaba da bunkasa sosai, cinikayyar Sin da Afirka a cikin watanni biyar na farko bayan katse shingen haraji ta karu da kashi 12.4% a shekara. Sin ta dakatar da haraji kashi 100 bisa 100 ga dukkan kasashen Afirka 53 wadanda suke da huldar diflomasiyya da kasar. Wannan manufar ta rage shingen ciniki sosai kuma ta inganta damar shiga kasuwa da fitar da kayayyaki daga Afirka. Wannan fadada manufofin ciniki ya nuna yadda aka sauya tsarin yarjejeniyar cinikayya daga yarjejeniya ta dan wani lokaci daya ko mai iyaka zuwa hadewar kasuwa mafi tsari kuma ta dogon lokaci.

 

Mu’amalar jama’a, al’adu, ilimi da bude ido

Tattaunawar Jama’a da Jama’a ta Afirka da Sin wacce ta gudana a watan Mayu na 2025 a Lusaka, Zambia, ta tattaro kungiyoyin jama’a, shugabannin kasuwanci, ‘yan kasuwa, da masu tsara manufofi daga Afirka da Sin. Ta jaddada hadin gwiwa tsakanin al’ummar bangarorin biyu fiye da yadda bangare daya kacal ke mu’amalarsa.

A irin wannan tattaunawar ta hadin gwiwa da ta gudana a wani taron hadin gwiwa na 2025 a birnin Jinhua na lardin Zhejiang, an sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi 33, wadanda suka shafi ciniki, saka hannun jari na kasashen waje, kwangilar injiniyanci, gina rumbunan ajiya a kasashen waje, wadanda darajarsu ta kai yuan biliyan 40.11 (kimanin dalar Amurka biliyan 5.63).

Bayan kasuwanci, taron Jinhua ya hada da musayar al’adu da yawon bude ido, inda aka gudanar da bikin baje kolin al’adu da yawon bude ido na Afirka na farko.

 

Hadin gwiwar kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire da hukumar tarayyar Afirka

A watan Satumba na 2025, Hukumar Tarayyar Afirka (AUC) da Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha ta Sin sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna don zurfafa hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha. Daga 19-21 ga watan Nuwamban 2025 kuma, an gudanar da taron hadin gwiwa kan ci gaban kirkire-kirkire na Sin da Afrika a birnin Wuhan, da nufin daidaita hadin gwiwar kimiyya da fasaha kan bukatun ci gaban Afirka, ciki har da makamashi mara cutar da muhalli (green energy), biranen kimiyya, ci gaba mai dorewa, da sauransu.

 

Hadin gwiwar fasaha a ɓangaren kula da muhalli

Cibiyar Hadaka ta Sin da Afirka mai Amfani da Tauraron Dan Adam (CACSA), ta fadada hadin gwiwarta da Afirka a shekarar 2025. Tun kafuwarta a shekarar 2023, ta rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi da kasashen Afirka 16, inda ta kafa na’urori 14 na kula da sararin samaniya masu amfani da tauraron dan adam wadanda ke tallafawa sama da hotuna 70,000 masu inganci daga hangen nesa. Wannan yana tallafawa tsare-tsaren birane, sa ido kan yadda ake amfani da kasa, kula da tekuna ko koguna, sa ido kan muhalli, da sauransu.

Ta hanyar shirye-shirye a fannin kimiyya, samar da makamashi mara cutarwa ga muhalli, da kayayyakin more rayuwa na dijital, Sin da Afirka suna zurfafa hadin gwiwa ba wai kawai a fannin kayayyakin more rayuwa da aka fi sani kamar hanyoyi, layin dogo, tashoshin jiragen ruwa ba, har ma a fannoni masu muhimmanci na “zamani” da karni na 21 ke bukata don ci gaba.

 

Masu karatu, mu tambayi kanmu mana, me wannan gagaruman sabbin nasararorin hadin gwiwar Afirka da Sin ke nufi a nan gaba?

Daga cinikayya, da samar da ababen more rayuwa zuwa hadin gwiwa na dabarun fasaha da zamantakewa ta zamani da suka hada da kimiyya da fasaha, tattalin arzikin dijital, samar da makamashi mara cutarwa ga muhalli, da kirkire-kirkire. Hakan yana nuna ci gaba daga hadin gwiwa mai karfi irin na baya zuwa ga hadin gwiwa mai fadi a bangarori daban-daban na zamani, masu amfanarwa ga juna. Yarjejeniyar Kimiyya da kirkire-kirkire ta 2025 tare da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) da hadin gwiwar CACSA shaida ne na wannan ci gaban sauyin.

Idan aka aiwatar da wadannan yarjejeniyoyin hadin gwiwar yadda ya kamata, wannan hadin gwiwa mai zurfi zai iya taimakawa Afirka wajen hanzarta gyara da ci gaban masana’antunta da komawa cikin zamani. Har ila yau, hakan zai sanya Sin da Afirka a matsayin abokan tarayya wajen tsara sabon tsarin ci gaban duniya mai bangarori daban-daban.

 

 

 

 

 

 

 

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Babbar Kasuwar Fim Ta Sin Babbar Damar Nollywood Ce December 11, 2025 Ra'ayi Riga Ya Kamata Amurka Ta Daina Sa Hannu Cikin Harkokin Najeriya December 4, 2025 Ra'ayi Riga Duniya Za Ta Kara Kyau In Ba A Nuna Fin Karfi December 4, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kimiyya da fasaha hadin gwiwar hadin gwiwa

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa.

Tsarin ya mayar da hankali kan daidaita ranakun makaranta, da tsara lokutan darussa bisa bukatun shekaru da matakin karatu, da kuma kara aiki a kan basira, da kirkire-kirkire, da koyon sana’o’i, domin shirya dalibai su zama masu amfani a harkokin tattalin arziki tun daga matakin makaranta.

NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?

Shin ko wadanne alfanu ko akasin haka wannan canji zai haifar a fannin ilimi a kasar nan?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Yaba Wa Jami’an Tsaro Kan Ceto Dalibai 100 Da Aka Sace A Neja
  • Pezeshkian: Duniya Tana Bukatar Amintaccen Madogara, Zaman Lafiya Da Kuma Hadin Kai
  • Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba
  • Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci
  • BUA ya tallafa wa ɗaliban Sakkwato 200 da miliyan 40
  • Babbar Kasuwar Fim Ta Sin Babbar Damar Nollywood Ce
  • Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu  
  • NAJERIYA A YAU: Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi
  • Ganawa A Tsakanin Mataimakan Ministocin Waje Na Kasashen Saudiyya, China Da Minista Arakci Na Iran