Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su
Published: 12th, December 2025 GMT
Da yake zantawa sa wakilinmu jim kadan bayan Kamala atisayen, mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Tsaron Daji na kasa (NFSS) mai kula da Ayyuka, Manjo Muhammad Abubakar Abdullahi mai nurabus, ya ce hukumar na kara samun kaimi wajen amfani da sabbin dabaru da tsare-tsare don kare dazukan kasar.
DCG Mohammed, ya bayyana suna gudanar da irin wannan atisayen musamman duk karshen shekara na Arewa maso yamma bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da ingantaccen tsaro a dazukan Nijeriya.
Ya bayyana cewa NFSS za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro domin lalata maboyar ’yan bindiga da sauran miyagu da ke cikin dazukan kasar.
DCG Mohammed ya bayyana cewa bayan kammala atisayen, za a tura dakaru daban-daban zuwa muhimman dazuka da ake fuskantar barazana domin karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da cewa Najeriya ta samu zaman lafiya mai dorewa.
Ya ce: “Mun tara wadannan jami’ai ne domin tabbatar da cewa kowannensu ya samu cikakken horo da kuma fahimtar dabarun aiki a daji, kuma samu kayan aiki na zamani da za su ba su damar cin nasara a kowanne fanni.”
Wani jami’in leken asiri na hukumar ya bayyana cewa horon ya kunshi koyon yadda ake shige da ficen dazuka da dabarun gano layukkan sadarwar ’yan ta’adda, da kuma hanyoyin katse su ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Shugaban Sashen Leken Asiri na Arewa maso Yamma, Habibu Shehu Yakawada, ya ce jami’an hukumar sun shirya tsaf wajen amfani da gogewa da kwarewarsu a matsayin tsofaffi da masu aikin tsaro domin inganta tsaron daji.
Ya kara da cewa hukumar na da jami’ai a fadin kasar kuma za ta ci gaba da aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin samun dawwamammen sakamako.
A nasa jawabin,Wakilin Shugaban karamar Hukumar Nassarawa da ke Jihar Kano, Sani Jibrin SK Tudun Murtala wanda ya wakilci gwamnatin Jihar Kano, ya tabbatar da ci gaba da bayar da goyon baya ta fannoni daban-daban. Ya bayyana tsaro a matsayin alhakin kowa, tare da nanata kudirin Gwamnatin Jihar Kano na kare rayuka da dukiyoyi, yana kuma jinjina wa jami’an tsaro.
Kwamandan NFSS na Jihar Kano, Abdullahi Al’amin, ya ce wannan shi ne karo na 15 da ake gudanar da irin wannan horo, yana mai kara da cewa ba da jimawa ba za su fito fili su nuna shirinsu ga ’yan kasa a matsayin hanyar karfafa amincewar jama’a ga hukumar NFSS.
Ya tabbatar da cewa hukumar na da cikakken niyyar kawar da ’yan bindiga da sauran miyagun mutane daga dazuka da sauran yankunan kasar.
Shima Shugaban Sashen Fasaha da kirkire-kirkire na hukumar ta (NFSS) DCG Y. A. Abdulkareem, ya ce hukumar za ta yi amfani da sabbin hanyoyin tattara bayanan leken asiri da fasahohi sadarwa don inganta ayyuka da karfafa tsaron dazuka a fadin Nijeriya.
Haka zalika, an gudanar da atisayen kai farmaki na karshe, inda jami’an suka nuna kwarewarsu ta yadda za su kewaye daji, su toshe hanyoyin tserewa, sannan su fatattaki duk wata kungiya ta miyagu da ke cikin yankin.
Wani jami’i daga cikin mahalarta atisayen ya ce: “Mun dauki wannan horo da muhimmanci domin kare rayukan ’yan kasa. Za mu shiga dazuka ba tare da tsoro ba har sai mun kawar da barazanar ta’addanci.”
Da yawan jami’an tsaron dajin da suka zanta da wakilinmu sun tabbatar da cewa jama’ar yankunan arewa sun nuna gamsuwa da wannan mataki, suna masu fatan cewa sabon shirin zai kawo karshen matsalar rashin tsaro da ta dade tana addabar su.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: tabbatar da cewa
এছাড়াও পড়ুন:
‘Sojojin Najeriya da na Ivory Coast 200 sun shiga domin tsaftace Jamhuriyar Benin’
Ministan Harkokin Waje na Jamhuriyar Benin, Olushegun Adjadi Bakari, ya ce kimanin sojoji 200 daga Najeriya da Ivory Coast yanzu haka na cikin kasar shi a matsayin wani ɓangare na aikin tsaro don tallafa wa gwamnati.
Ƙaramar ƙasa ta Yammacin Afirka ta girgiza da yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar Lahadi, wanda ya sa Najeriya, Faransa da Ivory Coast suka tashi tsaye wajen goyon bayan gwamnatin farar hula.
Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin mota“A halin yanzu akwai kusan sojoji 200 da suka zo don ba da taimako ga rundunar tsaron Benin a cikin aikin sharewa da tsaftacewa,” in ji Olushegun Adjadi Bakari ga ’yan jarida a taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Alhamis.
Wata majiyar tsaro daga Ivory Coast ta ce Abidjan ta turo sojoji 50 a matsayin ɓangare na wannan aiki, inda ƙungiyar ECOWAS ta bayyana cewa za a haɗa da sojoji daga Ghana da Saliyo.
Najeriya ta ce sojojinta sun isa Benin tun ranar Lahadi. ECOWAS ba ta bayyana adadin sojojin da ake sa ran za su shiga ba.
Bakari ya ce lokacin da rundunar Benin ta nemi taimako, shirin juyin mulkin “ya riga ya yi wargaje.”
Ya ce sojojin Benin masu biyayya sun fatattaki harin farko, amma lamarin na buƙatar kulawa sosai don kauce wa asarar rayukan fararen hula.
“Mun nemi goyon bayan ’yan’uwa ba saboda rundunarmu ba za ta iya ba, amma saboda Shugaban Ƙasa bai so a yi asarar rayuka masu yawa ba.”
Ya ƙara da cewa kai hari kai tsaye zuwa sansanin masu juyin mulkin na iya haifar da zubar da jini mai yawa. “Shi ya sa Shugaba Patrice Talon ya nemi goyon bayan Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.
“Rundunar Benin ta yi nasarar fatattakar wannan yunƙurin juyin mulki, amma haɗarin asarar rayuka da dama ya sa aka buƙaci martani na haɗin gwiwa.”
Ana ci gaba da tattaunawa kan ko sojojin tsaro na yankin za su ci gaba da zama na ɗan lokaci, amma Bakari ya ce duk wani mataki “za a ɗauka ne tare da haɗin gwiwar rundunar tsaro ta Benin, wadda ta nuna jarumta.”
Yadda Najeriya ta taimaka wa Benin — TuggarA taron ministocin ECOWAS da aka yi a Abuja, Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya ce saurin matakan diflomasiyya, na soja da na leƙen asiri tsakanin Najeriya da Benin ne ya taimaka wajen dakile juyin mulkin.
Tuggar ya ce lamarin ya nuna yadda za a iya kare dimokuraɗiyya idan ƙasashe makwabta suna sadarwa yadda ya kamata.
Ya ce, “Haɗin kai don tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da kasancewa a Benin ya yi nasara, kuma wannan misali ne na abin da ya kamata a yi duk lokacin da dimokuraɗiyya ke fuskantar barazana a yankinmu.”
A halin yanzu, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa Pascal Tigri, wanda ake zargi da jagorantar juyin mulkin da bai yi nasara va, tare da abokan aikinsa suna buya a Togo.
A ranar Laraba, jami’an gwamnatin Benin suka shaida wa Reuters cewa shugaban juyin mulkin yana gudun hijira a Lome 2, unguwa a babban birnin Togo inda gidan shugaban ƙasar, Faure Gnassingbe yake.