2025-12-08@19:07:55 GMT
إجمالي نتائج البحث: 78

«a makarantar kananan yara»:

    An ceto ’yan matan nan 24 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar sakandaren Gwamnati ta GGCSS da ke yankin Maga da ke Jihar Kebbi. Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idiris a taron manema labarai a ranar Talata fadar gwamnatin jihar ya tabbatar da an karɓo ɗalibban da aka sace a farkon makon nan. Ya ce “an karɓo ɗiyanmu ’yan makaranta waɗanda aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya baiwa jami’an tsaro umarni a tafi a gano inda yaran suke kuma a karɓo su muna tabbatar wa uwayen yara da al’ummar Kebbi yara sun dawo. “Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro musamman sojoji da ’yan sanda da Sibil difens da sauransu da suka...
    Ɗalibai 50 da aka sace a Makarantar St. Mary’s da ke garin Papiri, a Ƙaramar Hukumar Agwara ta Jihar Neja, sun tsere daga hannun ’yan bindiga. ’Yan bindigar da suka sace su, sun kai hari makarantar da safiyar ranar Juma’a. Barin jama’a su kare kansu ne ke rura rashin tsaro — Sojoji An rufe duk makarantu a Kebbi Maharan sun harbe mai gadin makarantar sannan suka sace ɗalibai sama da 200 da ma’aikatan makaranta 13, ciki har da malamai. A farko, Shugaban Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a Jihar Neja, Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ne mamallakin makarantar, ya ce ɗalibai 215 tare da ma’aikata 12 aka sace. Sai dai a ranar Asabar, ya ce har yanzu ba inda ɗalibai 88...
    Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas. Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki. Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa. Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar bilAdama wadanda aka ceto yara 17 daga hannunsu a garin Zariya. Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ta bayyana cewa yaran da aka ceto ana zargin an shirya safarar su ne zuwa Abuja da wasu sassan ƙasar da ma ƙetare. An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe Atiku ya karyata ba sojan da ya yi takaddama da Wike kyautar motar SUV Sanarwar ta bayyana cewa “an tari hanzarin ababen zargin ne da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar 12 ga watan Nuwamba. “A wannan lokaci ne jami’an sashen Ɗan Magaji da...
    Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya. Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka Gwada Don Samar da Abinci da Ƙara Darajar Kayayyaki a Najeriya”, da aka gudanar a Ilorin. Ya ba da shawarar kafuwar cibiyoyin injinan noma a kowanne yanki na ƙasa, domin horo, gyara, da tsara fasahohin aikin gona. A cewarsa, bayan samun injina, mafi muhimmanci shi ne kafa tsarin daidaitawa, haɗa na’urori a gida, da tsarin kulawa, domin tabbatar da cewa kowanne injin da aka tura...
      Haka kuma, daga ranar 10 ga watan Nuwamba, kasar Sin za ta soke matakin da ta dauka a kan wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin kamfanoni marasa aminci da ta sanar a ranar 4 ga Maris na wannan shekara, kamar yadda wani mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana a cikin wata sanarwa.   Mai magana da yawun ma’aikatar ya kara da cewa kamfanonin cikin gida za su iya gabatar da bukata da neman yin ciniki da kamfanonin Amurka da aka ambata a sama da zarar an amince da bukatunsu. (Amina/Abdulrazaq Yahuza Jere) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika November 5, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kaddamar...
    Daga Usman Mohammed Zaria   Majalisar Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa ta bayar da tallafin abinci ga fursunonin cibiyar gyaran hali ta Babura a matsayin wani ɓangare na ayyukan jin ƙai na majalisar. Yayin ziyarar, Alhaji Hamisu Muhammad Garu ya bayyana cewa, wannan taimako ya biyo bayan lura da bukatun fursunonin yayin da ya kai ziyara ta duba cibiyar a baya. A cewarsa, manufar bayar da tallafin ita ce don tallafa musu wajen kyautata rayuwarsu da kuma karfafa musu gwiwa su zama mutane nagari bayan sun fito daga gidan gyaran hali. A nasa jawabin, jami’in da ke kula da cibiyar gyaran hali ta Babura, ASP Muhammad Ali, ya gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa wannan karamci, yana mai cewa...
    Manajar  ofishin na NIWA,  da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci. Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu. “Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah. “ Aikin ya wuce batun fannin samar da...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Ra'ayi Riga Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Ci Gaban Kasashen Afirka? October 27, 2025 Labarai Ba Za A Samu Ƙarancin Man Fetur A Lokutan Bukukuwan Ƙarshen Shekara Ba – Dangote  October 27, 2025 Labarai An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga  October 27, 2025
    Majalisar Tattalin Arzikin Ƙasa (NEC) ta amince da shirin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu na sake fasalin da kuma zamanantar da cibiyoyin horar da jami’an tsaro a faɗin ƙasar. Wannan mataki ya biyo bayan taron majalisar na 152 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda Ministan Tsare-tsaren Kasafi da Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya gabatar da jawabi kan dabarun cimma burin Shugaban Ƙasa na samar da tattalin arzikin da ya kai darajar dala tiriliyan guda. An kafa kwamitin da Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ke jagoranta don tsara cikakken tsari na gyaran da sabunta cibiyoyin horar da jami’an ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro cikin wata guda. Mambobin kwamitin sun haɗa da gwamnonin jihohin...
    Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma, gwamnan ya gyara Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zamfara (ZACAS). A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama a faɗin jihar. Don rage mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa, ya ɗauki ƙarin ma’aikatan lafiya, tare da samar da magunguna da kayan aiki, tare d harkar kyautata kiwon...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira biliyan ɗaya domin gyaran ajujuwan karatu a wasu makarantu na gwamnati. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Dutse. A cewarsa, majalisar zartarwar jihar ta amince da kashe fiye da Naira miliyan 528 domin gyaran ginin ajujuwa a wasu zababbun makarantu na gwamnati a fadin jihar. Ya bayyana cewa, manufar aikin ita ce inganta yanayin karatu, tabbatar da tsaro, da kuma samar da iingantaccen ilimi karkashin shirin gwamnatin jihar na farfado da ilimin asali. Sagir Musa ya kuma ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 512 domin  samar...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da shirin AGILE na tallafin karatun yara mata da tallafin gyaran makarantu, domin inganta ilimi a faɗin jihar. A wajen bikin da aka gudanar a Otal ɗin Custodian, Gwamna Inuwa, wanda Mataimakinsa Dakta Manasseh Jatau, ya wakilta, ya ce gwamnati na da niyyar kawar da duk wani abin da ke hana yara mata zuwa makaranta. ’Yan sanda sun ƙwato miyagun ƙwayoyi a Gombe Ba mu ji dadin yi wa mahaifinmu afuwa tare da riƙaƙƙun masu laifi ba – Iyalan Herbert Macaulay Ya ƙara da cewa: “Idan ka ilmantar da ’ya mace, ka ilmantar da al’umma gaba ɗaya; idan ka karfafe ta, ka karfafu zuri’a baki ɗaya.” Gwamnan, ya gode wa Bankin Duniya,...
    Kwanturola na hukumar gyaran Hali a Najeriya reshen jihar Zamfara, Murtala Muhammad Haruna, ya yi kira da a shigar da fursunoni cikin tsarin inshorar lafiya na kasa (NHIS) domin tabbatar da samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.   Ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga kwamishiniyar lafiya ta jihar Zamfara, Dakta Nafisa Muhammad Maradun, a ofishinta da ke Gusau.   Haruna ya ce shirin ya yi dai-dai da hangen nesan babban kwamandan hukumar gyaran hali ta Najeriya da nufin inganta jin dadin fursunonin da ke gidajen yari.   Kwantirolan ya kuma jaddada bukatar inganta asibitin hukumar da ke cibiyar tsaro ta matsakaita, Gusau, da samar da isassun kayan aikin likita da magunguna masu mahimmanci...
    Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Dokta Aishatu Umar Maigari, ta ce talauci da nuna bambanci na daga cikin manyan dalilan da ke hana yara mata damar samun ilimi a jihar. Ta bayyana hakan ne a wajen bikin Ranar Yara Mata ’Yan Makaranta ta Duniya ta shekarar 2025, wanda Shirin AGILE tare da Access Initiative Africa da Nudge Initiative suka shirya a Gombe. Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno A wajen bikin, Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Asma’u Inuwa Yahaya, ta yaba da yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tabbatar da cewa ba a bar wata yarinya a baya wajen samun ilimi....
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya kiyasta cewa Najeriya ta yi asarar kimanin dala biliyan 10, kwatankwacin Naira tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana hakan a Maiduguri ranar Laraba yayin ƙaddamar da wani shirin farfaɗo da rayuwar yara da rikici ya shafa ta hanyar ba su horo da tallafi. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Majalisa ta yi watsi da zargin Amurka na yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya An wakilta Saeed ta hannun Manajan Kare Yara na UNICEF, Shah Mohammad Khan, inda ta ce rikicin da ya daɗe ya rage girman tattalin arzikin ƙasar, ya kuma lalata...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
    Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba. Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram...
    Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri na rajistar yara kyauta domin rage adadin waɗanda ke zaune gida ba tare da zuwa makaranta ba. Bincike ya nuna cewa fiye da yara 787,000 ne ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sanya gwamnatin ta tashi tsaye wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi. Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja Uwargidan Gwamnan Gombe, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ce ta ƙaddamar da shirin a hukumance, inda ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ganin kowane yaro ya samu damar karatu. A cewarta, shirin zai taimaka...
    Shekara guda matafiya da direbobi a ƙauyukan Malori-Guskuri da Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi na ci gaba da fama da wahala bayan da ruwan sama ya karya babban titin Kano–Maiduguri. A ranar 7 ga Agusta, 2024 ne ruwa ya cinye babbar hanyar a Malori-Guskuri, ya kuma yanke babban ɓangare na hanya. Mako guda bayan nan kuma wani ɓangaren ya rushe a Sabon Gari. Shekara guda da wata ɗaya bayan faruwar lamarin, wanda ya mayar wuraren da suka rushe sun koma tarkon mutuwa da ke haddasa haɗurra da suka kashe mutane da raunata wasu da dama. Wakilinmu da ya kai ziyara ya samu wani kamfanin gine-gine ya dawo Malori da kayan aikinsa. Mazauna sun tabbatar da...
    Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar. “Mun fara wannan shiri fiye da shekara...
    A cikin shekaru uku da kafuwarta, gidauniyar Misilli, ta mayar da yara 150 makarantar boko a Jihar Gombe, ciki har da mata 88 da maza 62, tare da ɗaukar nauyin kuɗaɗen karatunsu. Wannan mataki ya taimaka wajen rage nauyin iyaye marasa hali, inda suka samu ’yancin zaɓar makarantun da ke kusa da su. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan kuɗi a Akwa Ibom Shirin AGILE ya tallafa wa gidauniyar da litattafai domin ƙarfafa wannan yunƙuri, lamarin da shugabar shirin a Gombe, Dokta Amina Haruna Abdul, ta yaba da shi tare da alƙawarin yin haɗin gwiwa. Ita ma, Dokta Hauwa Yahaya Umar daga SUBEB, ta ce irin wannan...
    Kasashe takwas, ciki har da Pakistan, Morocco, Syriya, Libya, Jordan, Lebanon da kuma Masar, sun himmatu wajen bayar da fifikon kula da cutar kansa ta yara, ta hanyar kula da ka’idojin kasa, ta hanyar yin gwajin cutar da a kan lokaci, samar da ingantattun magunguna da kuma samar da kudade don bai wa iyali kariya. Kwanan nan, Maroko ta karbi bakuncin taron bita na farko, kan kula da lafiyar yara, yayin da Lebenon kuma ta kafa kwamitin kula da cutar kansar yara, wanda ya shafi wadanda suka tsira da rayukansu, ma’aikatan jinya, sauran ma’aikata da kuma wakilan Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
      Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata.   A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shi a matsayin kakakin sa sama da shekaru biyu.   A shekarun baya na yi rubuce-rubuce da dama a kan Dauda Lawal, ma’aikacin banki kuma mai taimakon al’umma.   Amma, yayin da ya cika shekara 60 a yau, zan so in fitar da wasu ’yan muhimman abubuwa da Dauda Lawal ya yi a matsayin gwamna, wanda ke mayar da Jihar Zamfara daga kufai da...
    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham, ’yan mintoci kalilan bayan fara tafiyar. Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” Injin jirgin da kuma tarago biyu da ke biye masa sun samu mummunar illa, a yayin da ragowar taragu shida...
    Farashin Man Fetur Ya Fadi Kadan Sabuda Fatan Kyarar Bututun  DRUZHBAC Na Kasar Rasha Farashin man fetur ya tashi a kasuwannin duniya bayan da ana saran za’a kammala gyaran bututun kwararar man fetur na kasar Rasha watu DRUZHBA wanda yake kai man fetur zuwa kasashen turai ta kasashen Slovakia da kuma Hungary. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa farashin man ya tashi a jiya laraba, amma kuma tare da wannan fatan ya sake tashi. A cikin makonnin da suka gabata ne sojojin kasar Ukraine suka kai hare-hare kan bututun man tare da amfani da jiragen yaki  wadanda ake sarrafasu daga nesa. Labarin ya kara da cewa tuni kamfanonin man fetur a kasashen Slovakia da kuma Hungary sun bayyana cewa...
    Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya.   A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.”   Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan.   Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasar shawara Mahdi Sanaei, ya ce Pezeshkian zai bar Tehran zuwa Yerevan a ranar Litinin din nan, sannan ya wuce Minsk. Ya kara da cewa, a ziyarar ta kwanaki biyu da shugaban zai  kai, yana shirin tattaunawa da manyan hukumomin Armeniya da Belarus, kan hanyoyin da za a bi wajen fadada dangantakarsu, musamman a fannin kasuwanci, da kuma sanya hannu a kan takardun yarjeniyoyi a tsakaninsu. Sanaei ya kara da cewa an shirya kai ziyara a kasashen Armenia da Belarus a karshen watan Yuni, amma aka dage. Ya...
    Tawagar Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta kai ziyarar ta’aziyya ga sabon Sarkin Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a fadarsa.   Ziyarar ta biyo bayan rasuwar marigayi Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, wanda aka yi ta murna da shi a bisa kyakkyawan jagoranci da kuma gudunmawar ci gaban masarautu da jihar Zamfara.   Hajiya Larai Musa Lawal, ta mika sakon ta’aziyyar uwargidan shugaban kasar ga iyalan gidan sarautar tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahama.   Ta kuma mika sakon taya murna ga sabon sarkin, tare da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya mai cike da hikima da zaman lafiya da hadin kai.   A nasa jawabi, sabon Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim...
    Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka. Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou  ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama tamfar alaƙaƙai a Najeriya. Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya   “A cewarsa cutar Kwalara na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya, inda ƙasar ke fama da ɓarkewar cutar a ‘yan shekarun nan.” “Ya zuwa ƙarshen watan Yuni, Najeriya ta samu adadin mutane 3,109 da ake zargin...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano. Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama na jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya shafi kudurori da sabbin batutuwa dangane da gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.” Sanata Barau ya tunatar da cewa Majalisar Ƙasa ta riga ta amince da gyaran kundin tsarin mulki sau biyar, da aka fi sani da alteration acts na farko zuwa na biyar. Ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da ke buƙatar ƙarin...
    ‎Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace yara da yin garkuwa da su sannan ta kashe su. Rundunar ta ce wadannan kananan yara biyu mata ne ‘yan shekara bakwai, lamarin da ya jawo tarzoma da kona coci. Kakakin Rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya shaida wa manema labarai haka a Bauchi ranar Alhamis. NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso Wakil Ya bayyana cewa an samu rahoton faruwar lamarin ne a ranar 22 ga watan Yulin 2025, da misalin karfe 3:00 na rana. Ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata a ce ana ware wa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya. NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin...
    Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya. A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai dubban ƙananan yara da gwamnati ta rufe su ba kuma tare da cikakken bayani ga iyalansu ba, wasu ma a yanzu babu cikakken bayani kan inda suke ko kuma halin da suke ciki. Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Asusun ya ce a Nijeriya rufe ƙananan yara tare da...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa unguwar Qua da ke ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato. ’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Adadin waɗanda aka kashe mutum 32 da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara suna cikin...
    Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa Fursunoni 58 suna rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa NECO ta shekarar 2025. Wannan ci gaba ya samu ne bayan biyan kudin rajista da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Kofar-Nasarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano. Ya ce wannan karamci na gwamnatin jihar Kano shaida ce ta jajircewarta wajen kula da walwalar fursunoni, gyaran dabi’unsu da kuma dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata. “Biyan kudin rajistar jarrabawa da gwamnatin Kano ta yi alama ce ta jajircewarta wajen samar da dama ga fursunoni domin su...
    Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum shida hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 120, bisa samun su da laifin satar yara da kuma sayar da su. Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mercy Paul, Ebere Ogbono, Emmanuel Igwe, Loise Duru, Monica Oracha, da Chinelo Ifedigwe. PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta An same su da laifin ɓoye bayanai, taimakawa wajen aikata laifi, satar yara da kuma safarar su. An sace yaran ne daga Kano, sannan aka sayar da su a garin Onitsha da ke Jihar Anambra. Shugaban tawagar, Paul Onwe, tuni aka yanke...
    Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu.   Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023.   A cewar sa, inganta haɗin gwiwa da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a Zamfara.   Dangane da ababen more rayuwa kuwa, Gwamna Lawal ya ba da misali da ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa da kuma waɗanda aka kammala a ƙarƙashin shirin “Renewal Project,” wanda ya haɗa da gine-gine da gyaran hanyoyi, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya...
    Don girmama ziyarar shugaban ƙasa, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu domin bai wa mazauna yankunan damar halarta taron da kuma bin diddigin abubuwan da suka shafi ziyarar. Wannan ita ce ziyarar farko da Tinubu ya kai Jihar Benuwe tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta. Jama’a da dama na kallon wannan ziyara a matsayin gwada gwamnati kan yadda za ta shawo kan matsalolin tsaro, musamman a jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, rikicin makiyaya da na ƙabilanci. Kisan da aka yi a Yelwata, wanda shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren, ya janyo suka damuwa a faɗin ƙasar tare da ƙara matsin lamba ga shugaban ƙasa da ya ɗauki matakin gaggawa don tabbatar...
    Jimillar fursunoni: 80,879 Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256 Kashi na rijista da aka kammala: 74% Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki. Hukumar ta bayyana wannan aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin dijital, da sake gyaran rayuwa, da shigar da fursunoni cikin tsarin ƙasa. Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanansu daga hukumomin da suka dace kafin wallafawa domin kaucewa yaɗa bayanan da za su iya dagula fahimtar jama’a ko rage ƙwarin gwuiwar al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
      A wani yunkuri na rage adadin yara da suka daina zuwa makaranta, Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da shiri mayarda yara 200,000 zuwa makaranta a cikin shekaru hudu masu zuwa, karkashin shirin Reaching Out-of-School Children (ROOSC).   An bayyana wannan shiri ne a wani taron bita na kwanaki biyu da aka shirya tare da haɗin gwiwar Save the Children.   A cewar, wakilin Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Salisu Baba Lawal shirin zai shafi dukkan ƙananan hukumomi 23 a faɗin jihar.   “Wannan shiri na Gwamnatin Jihar Kaduna ne tare da haɗin gwiwar abokan ci gaba da masu aiwatar da ayyuka,” in ji shi.   “Gwamnatin Jihar Kaduna ta samo lamunin tallafin kudi domin aiwatar da wannan shiri da...
    Kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya sun bayyana rashin jin dadinsu ga Isra’ila, kan hana su ziyartar yankunan Falasdinawa Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun bayyana rashin jin dadinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar kungiyar kasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gabar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasdinawa. A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa’ud, ya ce matakin da Isra’ila ta dauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya. A dai tsara a wannan Lahadi ne ministocin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Qatar, da Turkiyya, karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan za su isa birnin Ramallah domin ganawa...
    Babbar jami’a a hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Shen Haiping, ta ce a shekarun baya bayan nan koshin lafiyar yaran kasar Sin na kara inganta. Jami’ar wadda ta bayyana hakan ga wani taron manema labarai a yau, ta ce a shekarar 2024, alkaluman mace-macen jarirai a kasar ya ragu zuwa jariri hudu cikin duk jarirai 1000, yayin da na yara ‘yan kasa da shekaru biyar ya ragu zuwa yara 5.6 cikin duk yara 1,000, adadin da ya yi kasa sosai cikin jerin kasashen duniya, dake rukunin masu al’ummun dake sama-sama a matsakaicin samun kudin shiga.   Shen Haiping ta kara da cewa, idan aka nazarci wadannan alkaluma, za a ga cewa cikin sama da shekaru goma da suka gabata,...
    Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a. Kasar ta ce wuraren da haramcin ya shafa sun hada da makarantu da tashoshin mota ko na jirgi, wuraren shakatawa, wuraren wasanni ko kasuwanni saboda kada yara kanana su gani. Yadda ambaliyar Neja ta ci mutum 12 ’yan gida daya NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ministar Lafiya da Iyali na kasar, Catherine Vautrin ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ta ce, “Dole a daina shan sigari a wuraren da yara suke. “’Yancin shan sigari ya kare ne a inda ’yancin yara na shakar tsaftatacciyar iska ya fara,” kamar yadda ministar ta shaida wa jaridar Ouest-France...
    Bayanai daga Falasdinu na cewa wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai cikin dare a wata makarantar Gaza dake zaman matsugunni ga masu neman mafaka ya yi sanadin shahadar Falasdinawa 30, ciki har da yara da dama, a cewar jami’an kiwon lafiya da na fararen hula. Da sanyin safiyar yau litinin ne sojojin gwamnatin Isra’ila suka kai hari a makarantar Fahmi al-Jarjawi da ke yankin Daraj na zirin Gaza, inda daruruwan iyalai da suka rasa matsugunansu daga garin Beit Lahia da ke arewacin kasar da Isra’ila ke fama da hare-haren bama-bamai suka samu mafaka.   Hukumar tsaron farar hula ta Gaza ta ce masu aikin ceto sun tsamo gawarwakinmutum 20 daga makarantar, ciki har da yara da dama. A...
    Bincike ya yi nuni da cewa an bar dukkan al’ummomi ba tare da ingantattun makarantu ba a jihohi kamar Borno, Yobe, da Adamawa. Sama da makarantu 1,500 ne aka lalata tun farkon rikicin Boko Haram, inda sama da malamai 19,000 suka rasa matsugunansu, kuma da yawa ma suna fargabar komawa. ‘Yan mata suna cikin hadari, galibi ana tilasta musu auren wuri ko aikin gida ko aikin jima’i maimakon a ba su damar koyo. Wata kwararriyaa fannin ilimi da ke zaune a Jos, Jihar Filato, Misis Peace Pernam, ta ce, “Ilimi wata hanya ce ta rayuwa mai muhimmanci da ke kawar da fatara, rage matsalar tsaro, da samar da ci gaban kasa, duk da haka, ga miliyoyin yara a yankin Arewa...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta yi kira ga hukumomin gwamnati da shugabannin makarantu da su ba da fifiko wajen kula da duk wasu gine-ginen makarantu da aka gyara domin kiyaye abubuwan da kuma tabbatar da ci gaban fannin ilimi.   Gwamna Dauda Lawal ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da sabuwar makarantar sakandaren Larabci ta mata ta gwamnati da aka gyara tare da inganta ta a garin Gusau.   Ya bayyana cewa, aikin sauran makarantun da ake gudanarwa a fadin jihar, wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na farfado da tsarin makarantun kwana, tare da karfafa tsaro domin kare makarantu da kewayen su.   A cewar Gwamna Lawal, inganta kayan aikin makarantu na da matukar muhimmanci wajen...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu maza biyu bisa zargin yi wa ƙananan yara mata fyaɗe a lokuta daban-daban a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun kama wani mutum mai shekara 47, da zargin yi wa ‘yar matarsa mai shekara biyu fyaɗe a Tudun Wada, Shamaki a ranar 5 ga watan Mayu. ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara  Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Bayan samun rahoton daga matarsa, rundunar ’yan sandan ta garzaya gidansu inda ta kama wanda ake zargin, sannan suka kai yarinyar Asibitin Ƙwararru na Gombe domin duba lafiyarts. Ya ce...
    Saraki, shi ne zai jagoranci kwamitin sai kuma ƴan kwamitin da suka haɗa da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare; gwamnan jihar Filato, Caleb Muftiwang da kuma gwmanan jihar Enugu, Peter Mba.   Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson da Sanata Ibrahim Dankwambo da tsohon gwamnan jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu.   Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da gwamnonin Enugu da Zamfara da Adamawa da Taraba da Osun da Oyo.   Ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike shima ya je taron sai kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Maƙarfi.   Suma ƴan jam’iyyar irin su Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Sule Lamido da Samuel Ortom da Gabriel Suswan da Seriake...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa: Gaza na gaf da afkawa cikin babbar masifa saboda zaluncin ‘yan mamayar Isra’ila A yayin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke ci gaba da killace Zirin Gaza sama da watanni biyu, abubuwan da ke faruwa a kowace rana, abubuwa ne da suke yadda bala’i ke shafar kowane gida, kowane titi, da kowane yaro, tare da cewa a kowace rana, ana kara gargadin cewa; Lokaci ya fara kurewa don ceton abin da za a iya cetowa. Ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sabunta gargadi game da bala’in da ke tafe saboda ci gaba da rufe mashigar yankin da kuma tsaurara matakan hana shigowa da madarar jarirai, da abinci mai gina jiki, da kuma...
    Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa. Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace mazabar Sanata, a halin da ake ciki a Makarantar Firamare ta Bare ba ta san da hakan ba. Wannan makaranta tana nuna sakaci da gazawar masu mulki. An kafa makarantar ce a shekarar 2005 karkashin shirin Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Gombe (SUBEB). Tun daga lokacin har zuwa yanzu, ba a taba samun gyara ko ci-gaba ba. Maimakon zama alamar ci-gaba, makarantar ta...
    Hare-haren sojojin mamayar Isra’ila sun kona kananan yara a garin Khun-Yunis da ke kudancin Zirin Gaza Hukumar tsaron fararen hula a Zirin Gaza ta fitar da wani faifan bidiyo a yau alhamis, inda ta ke nuna irin mummunan halin da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa suka shiga a Khan Yunis, bayan da jiragen saman yakin gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila suka yi luguden bama-bamai a kan tantunan ‘yan gudun hijiran Falasdinawa da suka rasa matsugunansu, Tun da tsakar daren jiya ne jiragen suka fara luguden wutan kan tantunan ‘yan gudun hijiran zuwa wayewar garin yau Alhamis, inda wutar bama-baman suka kone gawarwakin yara da mata, bayan shahadan mutane da dama. Rahotonni sun bayyana cewa: An hae-haren sun janyo shahadan yara da mata...
    Hukumar UNICEF ta MDD mai kula da yara ta bada sanarwan cewa kimani yara 3,500 suka rasa rayukansu a kokarin ketara tekun Medeteranina a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Spunic na kasar Rasha ya nakalto hukumar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar dangane da hakan. Labarin ya kara da cewa, wannan ya nuna cewa akalla yaro guda ne ya ransa ransa a ko wace rana. Kuma kashi 7/10 daga cikinsu sun halaka ko sun bace ne su kai ba ba tare da rakiyar iyayensu ba. Har’ila yau rahoton ya kara da cewa akalla mutane 20,803 suka halaka a tsakiyar tekun na Mediterranean a kokarinsu na tsallakawa zuwa kasashen na turai. Daga karshe hukumar...
    Wasu kafofin yada labarai a duniya na ganin cewa, idan gwamnatin Amurka ta ci gaba da saka shingayen haraji, to sauran kasashe za su maye gurbinta a bangaren samar da hidimomi. Abin da gwamnatin ta yi biris da shi yayin da take kididdigar harajin da za ta kakabawa sauran sassa, har yanzu wannan bangare na shiga gogayyar ciniki.   Bisa bayyanan da aka fitar, Amurka ta dade tana cin rarar kudin ciniki a bangaren ba da hidimomi. Alal misali a shekarar 2024, yawan rarar kudin da ta samu a wannan bangare ya kai dala biliyan 300. Kuma Abin lura shi ne, cinikin hidimomi na matukar dogaro da cinikin kayayyaki. Gibin kudin cinikin da Amurka ta samu a bangaren cinikin kayayyaki...
    Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin. Ko da yake babu wanda ya rasa ransa a wannan lamarin, wani ma’aikacin hukumar kashe gobara ya samu raunuka yayin da yake kokarin kashe gobarar. Wani ganau ya ce, “Gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar tukunyar gas — inda wani kara mai ban tsoro ya sa ma’aikata da matafiya a yankin suka yi ta gujegujen domin tsira.” Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Mahara sun...
    An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP). Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito ne daga ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba. Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno A yayin da take zantawa da manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a ta ce an yaudari yaran daga unguwar su aka yi safarar su zuwa jihohin Kudu maso Gabas. Ta ce, sun...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
    Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da kayayyaki. Daga bisani me kasar Sin ta yi? Ta samar da tunanin gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya, inda aka nanata bukatar ba sauran mutane damar jin dadin zaman rayuwa, matukar wani mahaluki na son samun zaman rayuwa mai inganci. Bisa wannan tunani ne, kasar Sin ta samar da jerin shawarwari masu alaka da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da cudanyar mabambantan...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya sanar da cewa, yara a Gaza suna fuskantar matsakar kwakwalwa da ba a taba ganin irinsa ba a kan kananan yara. “Ba mu da wani bayani a tarihin wannan zamani dangane da ke bukatar tallafin lafiyar kwakwalwa kamar yaran Gaza,” in ji mai magana da yawun UNICEF James Elder a wani taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva. Sannan kuma jami’in  ya yi Allah wadai da tauye hakkin yara da ake yi da gangan a Gaza, ya kuma bukaci masu karfin fada a ji a duniya da su dauki mataki. Ya kara da cewa an toshe alluran rigakafi 180,000 na rigakafin yara masu mahimmanci, da na’urorin saka jariran da ba...
    Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan. Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis. Sanƙarau ta kashe mutum 55 saboda rashin tsafta a Kebbi Dabarun Rabauta Da Kwanaki 10 Na Ƙarshen Ramadan “Muna bai wa makarantun Tsangaya 85 kayan abinci 85, biyar a kowace Ƙaramar Hukuma, inda muke ciyar da almajirai tsakanin 300 zuwa 400 a kowace makaranta,” in ji shi. Ya ƙara da cewa Gwamna Mai Mala Buni ne, ya amince da wannan shiri domin tallafa wa yara marasa...
    Rahotanni sun nuna cewa gobara ta kashe yara uku tare da jikkata wasu 13 a ƙauyuka tara na Jihar Yobe, tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2025. Gobarar ta kuma lalata gidaje 86, inda ta bar mutane da dama ba tare da matsuguni ba. Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas Ba tarbiyya nake koyarwa ba — Sadiq Sani Sadiq Babban sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Yobe (YOSEMA), Dokta Mohammed Goje, ya bayyana cewa rashin kula da wutar lantarki, amfani da gas, ƙonewar daji, da kuma zubar da shara ba bisa ƙa’ida ba, ke haddasa yawan gobara a jihar. Ya ce lamarin ya fi shafar yankunan Damaturu, Gulani, da Yusufari, inda mazauna ke kokawa...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana  tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna  kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
    Jiya Litinin, kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya sanar da cewa, a bana, kasar Sin za ta gaggauta aikin gyara da kyautata ababen aikin gona a muhimman yankunan shuka kayan lambu cikin manyan rumfuna. A matsayin muhimmin matakin kara bukatun al’umma da karfafa bunkasar tattalin arziki, majalisar gudanarwar kasar Sin ta fara aikin kyautata na’urorin aiki da kuma maye gurbin tsoffin kayayyaki da sabbabi a bara. A bana kuma, an habaka wannan aiki zuwa harkar noma, inda za a mai da hankali wajen gyara da kyautata tsoffin manyan rumfuna masu aiki da hasken rana, da rumfuna na roba, domin karfafa tsarin kiyaye tsaro, da kara yin amfani da gonaki. Haka kuma, bisa wannan shiri, za a...
    Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu. “Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu. “Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai...
    Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu. “Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu. “Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai...
    An gurfanar da wadanda ake zargin ne bisa laifuka daban-daban, da ke da alaka da laifukan zamba ta yanar gizo, mallakar wasu takardu da ke dauke da shaidar karya, da kuma satar bayanan sirri.   Dukkansu sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su a lokacin da aka karanta musu tuhumar, sai dai lauyan masu shigar da kara, Nnaemeka Omewa, ya bukaci kotun da ta dage zaman shari’ar tare da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali.   Mai shari’a Osiagor ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2025 domin ci gaba da shari’a, sannan ya bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana jin dadinta bisa gagarumin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da manufofinta guda 12 don inganta rayuwar al’umma da ma ci gaban jihar baki daya. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. Ya bayyana cewa shirin da ke da nufin kusantar da jama’a ga gwamnati, zai kuma tabbatar da cewa manufofi da shirye-shiryen da aka aiwatar sun dace da  muradin al’umma. Don haka Namadi ya yabawa al’ummar yankin bisa yadda suka rungumi ayyukan da gwamnatin jihar ke  aiwatarwa hannu bibbiyu, tare da yin alwashin ci gaba da samar da ingantattun ayyuka. Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa, zai yi nazarin...
      Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari.   Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi online – Kula da shafukan da suke ziyarta da kuma mutanen da suke magana da su. Amfani da ‘Parental Control’ – A saita wayoyin yara domin hana shiga shafuka masu illa. Ilimantar da yara kan sirri – A koya musu kada su bada bayanan sirrinsu kamar lambar waya, adireshi, ko hotuna. Kafa iyaka kan amfani da intanet – Iyaye su saka ka’ida kan lokacin da...
    Jakadan Iran a Lebanon ya bayyana cewa: Suna maraba da matakin jigilar jiragen saman Lebanon zuwa Iran da sharadin rashin soke jigilar jiragen Iran zuwa Lebanon Jakadan kasar Iran a kasar Lebanon Mujtaba Amani ya bayyana cewa: Bangaren Iran yana maraba da samar da jigilar jiragen saman kamfanonin jiragen saman kasar Lebanon zuwa kasar Iran, ba tare da batun soke jigilar jiragen saman Iran zuwa kasar Lebanon ba. Gidan talabijin din kasar Iran a yau Juma’a ya sanar da cewa: An yi watsi da furucin wasu kamfanonin jiragen sama guda biyu da suka ce, gwamnatin Lebanon ta hana tafiyar jiragen saman Iran guda biyu zuwa kasar Lebanon da suke tashi a ranakun Alhamis da Juma’a, don haka ofishin jakadancin Iran...
    Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar. Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu. An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Jagoran majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne, ya jagoranci tattaunawar, inda ya jaddada buƙatar sauta tsarin harajin Najeriya. Ya ce dokokin za su sauƙaƙa biyan haraji, cire harajin kayayyakin buƙatu na yau da kullum kamar abinci da kiwon lafiya, tare da samar da rangwame ga ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi. Yawancin ’yan majalisar...
    Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar na nuna da cewa, Kano tana da kimanin yara 837,479 da ba sa zuwa makaranta, adadi mai ban mamaki da jihar ke kokarin magancewa.   Tawagar tantancewar, karkashin jagorancin jami’a mai kula da ilimin yara mata ta jihar, Hajiya Amina Kassim, ta ziyarci kauyuka da dama, inda ta tattauna da iyaye, da shugabannin gargajiya, da malaman addini. “Tawagar ta gano muhimman abubuwan da...
    Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu varna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya. “Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu. “Haka zalika za a bukaci masu gudanar...
    Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu barna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya. “Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu. “Haka zalika za a bukaci masu gudanar...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
۱