Jaridar Daily Trust da gidan talabijin na Trust TV, dukkansu mallakar kamfanin Media Trust, a bana ma sun sake yin fice bayan ’yan jaridansu suka lashe kyautar binciken kwakwaf ta Wole Soyinka ta bana.

’Yan jaridar na Daily Trust da Trust TV, Afeez Hanafi da Muslim Muhammad Yusuf, sun lashe gasar ne a matsayin zakaru a rukunin rahoton jarida da kuma na talabijin mafi daraja a bana a Najeriya.

Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato

Hanafi ya lashe rukuni na rubutu bisa labarinsa mai taken: “Bincike: Dan jarida ya samu ayyuka biyu da takardun bogi na Oluwole.”

Wanda ya zo na biyu da na uku a rukunin na rubutu su ne Kingsley Jeremiah da Ann Godwin, dukkansu daga jaridar The Guardian.

Sai dai kamar yadda aka saba, babu wanda ya lashe kyautar a rukuni na rediyo, kuma babu wanda ya fito a matsayin na biyu ko na uku.

A rukuni na yanar gizo, Theophilus Adeokun na National Record ya lashe gaba ɗaya da labarinsa mai taken: “Dangote, a neman makamashi mai arha, yana zubar da guba cikin kogunan Binuwai.”

Wanda ya yi na biyu shi ne Kunle Adebajo daga HumAngle, yayin da Isah Ismaila, shi ma daga HumAngle din ya zo na uku.

A rukunin hoto kuwa, Elliot Ovadje na jaridar Punch ya fito a matsayin zakara, sannan shi ɗin ne ya sake fitowa a matsayin na biyu da na uku.

A bangaren girmamawa, tsohon Alkalin Kotun Ƙoli, Justice Ayo Salami, ya samu kyautar mai rajin kare hakkin dan Adam, yayin da fitaccen marubuci kuma mawaki, Odia Ofeimun, ya samu kyautar kwarewa a aikin jarida.

Tun kafin gabatar da kyaututtuka, shugabar alkalai ta shekarar 2025, Abigail Ogwezzy‑Ndisika, a jawabinta ta ce an samu shigar da rubuce‑rubuce 180, amma aka tace su zuwa 129.

Ta jaddada abubuwan da aka yi amfani da su wajen tantance kowanne rubutu da suka hada da jarumta, zurfi, daidaito, tasiri da kuma jajircewa ga muradun jama’a.

“Mun yi wannan aikin ne daban‑daban kuma ba tare da katsalandan ba, ta amfani da wasu ka’idoji da suka shafi rufe batutuwan cin hanci, take hakkin ɗan adam, laifuka da ayyukan ɓoye, da kuma kyawawan hanyoyin binciken jarida,” in ji ta.

Marubucin da aka saka wa gasar sunansa kuma mai lambar yabo ta Nobel, Wole Soyinka, ya taya dukkan wadanda suka samu kyautar murna, yana mai gargadin kada su yi sakaci.

“Wasu daga cikin jaruman da za su ceci wannan ƙasa za a same su a cikin kafafen yada labarai. Amma a lokaci guda, dole ne in roƙi kafafen yada labarai su yi dada takatsantsan, su yi bincike mai zurfi kan abin da suke wallafawa. Akwai labarai masu yawa da ake wallafawa da ba daidai ba ne,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga jaridun da su inganta rahotanninsu, yana nuna damuwa kan yawan labaran karyar da ke yawo a kafafen sada zumunta.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba

Ana taro kan yadda manzon Allah mohammad dan Abdullahi (a) ya zauna da wadanda ba musulmi ba a rayuwarsa a Madina.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto hukuma mai kula da al-adu da kuma al-amuran addinin Musulunci a nan Iran tana cewa ana gudanar da wannan taron ne a dai dai lokacinda aka fara bukukuwan cika shekaru 1500 na hijirar manzon Allah (s).

Labarin ya kara da cewa an sabi baki wadanda suka gabatar da jawabi masu muhimmanci daga kasashen Iran, Lebanon da kuma Masar.

Ahmad Mobaleghi na mamba a kwamitin al-amuran addini na hukumar ya kawo ayoyin al-kur’ani wadanda suka yi mgana kan yadda manzon Allah yayi mu’amala da yahudawan da ya samu a Madina, kuma ya ce wadannan ayoyi kekyawar misali ne nazamantakewar Musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Louis Saliba wani marubu ce kirista daga kasar Lebanon, wanda kuma ya gabatar da Jawabinsa ta kafar Bidiyo daga kasar Lebanon yay aba da yadda manzon Allah (s) yayi mu’amala da nasaran Najran wadanda suka zo masa daga kasar  yemen.

Sai kuma Abdolsalam Emami, mai bawa ma’aikatar al-adu shawara kan mabiya mazhabar sunna a nan Iran yayi magana a kan yadda manzon Allah (s) ya zauna da yahudawa a Madina ya kuma kawo misalai da dama wadanda suka shafi hakan.

Sai kuma Amani Mahmoud Ibrahim, sheikhin malami a Jami’ar Al-Azhar ta kasar Masar wanda ya kawo yadda yahudawan Madina suka saba al-kawalin da suka cimma da manzon Allah (s) a farkon hijira da kuma yadda yayi mu’amala da su.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Najeriya: Jirgin Sojojin Kasar Yana Kan Hanyarsa Ta Zuwa Portugal, Amma Ta Sauka A Burkina Faso December 9, 2025 Saudiya da Qatar Zasu Gina Layin Dogo Mai Sauri Tsakanin Kasashen Biyu December 9, 2025 Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki December 9, 2025 Pakistan ta Bai Wa Taliban Ta Aghanistan  Zabi A Tsakanin Mu’amala Da Ita Ko  Da  ‘Yan Ta’adda December 9, 2025  Kasashen Iran Da Turkiya Za Su Bunkasa Alakarsu A Fagen Ilimi Da Musayar Fasaha December 9, 2025 An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa” December 9, 2025  Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba December 9, 2025 AU Ta yi Tir Da Harin RSF  A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80 December 8, 2025 MِِِِDD:  Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Jamhuriyar Benin – Soyinka
  • RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne
  • Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba
  • NAJERIYA A YAU: Kudaden Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi Zai Lashe
  • Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka  Teke Fuskanta
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168
  • Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166