Buɗe cibiyar horas da sabbin sojoji a Kudu zai taimaka — Janar Shaibu
Published: 14th, December 2025 GMT
Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar-Janar Shaibu ya yaba, ya bayyana cewa buɗe cibiyoyin horas da sabbin kuratan sojoji (Depot) a jihohin Kudu zai ƙara ƙarfin rundunar wajen karɓar sabbin ma’aikata a faɗin ƙasa.
Laftanar-Janar Shaibu ya bayyana cewa za a buɗe sabbin cibiyoyin horas da sabbin kuratan sojojin ne a Osogbo da ke Jihar Osun da kuma Abakaliki a Jihar Ebonyi.
Ya bayyana haka ne a yayin bikin yaye sabbin dakarun soji 3,439 da aka yi a Cibiyar Horas da Sabbin Kuratan sojoji (Depot) da ke Zariya, inda ya shawarce su da su zama masu kishin ƙasa da jajircewa.
Ya yaba wa sabbin sojojin bisa jajircewa, juriya da ƙwarewa da suka nuna a tsawon watannin da suka shafe suna karɓar horo a cibiyar.
Shirin kafa ‘Hisbar Ganduje’ ya tayar da ƙura a Kano Dalilin da ya sa muka ziyarci Obasanjo — TurakiLaftanar-Janar Shaibu ya bayyana ranar a matsayin ranar nuni da babban ci gaba wajen cika manufar rundunar sojojin Najeriya ta faɗaɗa karfin ma’aikata.
Ya taya sabbin sojojin murnar kammala horon farko na soja, wanda, a cewarsa, shi ne matakin farko na doguwar tafiyar sadaukarwa, kishin ƙasa, da hidima ga al’umma.
“Kuna shiga rundunar soja ne a wani lokaci mai muhimmanci a tarihin ƙasarmu, lokacin da ƙalubalen tsaro ya yi yawa. Ku ɗauki wannan dama da muhimmanci domin ku zama wani ɓangare na mafita ga matsalolin ta’addanci da rashin tsaro,” in ji shi.
Ya buƙace su da su riƙe gaskiya, ladabi, da bin ƙa’ida a duk inda suka samu kansu, yana mai cewa horon da suka samu (a Depot NA) ya shirya su wajen fuskantar manyan ayyukan soja na zamani.
Janar Shaibu ya bayyana cewa manufar sauya tsarin rundunar soja a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Sojoji na nufin kafa runduna mai ƙwarewa, ɗorewa, da shirye-shiryen fuskantar ƙalubale cikin haɗin kai da sauran hukumomin tsaro.
Ya kuma jinjina wa Kwamandan Depot na Zariya, Janar Ahmadu Bello Muhammad, da malamai da jami’an horo saboda jajircewarsu wajen ganin an kammala horon cikin nasara.
Haka kuma, Babban Hafsan Sojoji ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, wanda shi ne Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya, bisa jagoranci da goyon bayan da yake bai wa rundunar, tare da godewa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, da al’ummar Zariya saboda kyakkyawar alaƙa da rundunar soja.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Janar Shaibu ya
এছাড়াও পড়ুন:
2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe
Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanninta a Jihar Gombe, inda ta jaddada muhimmancin haɗin kai da farfado da jam’iyyar tun daga matakin ƙananan hukumomi zuwa jiha gabanin zaɓen 2027.
Taron ya halarta bayan zuwan wakilai daga dukkanin ƙananan hukumomin jihar.
Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 2, sun ƙwato makamai a BornoMambobin jam’iyyar sun yaba da yadda komai ya gudana cikin lumana da tsari, abin da suka ce alama ce ta daidaito a cikin jam’iyyar.
Elder Ambrose Ismail Mairungu ne, ya zama sabon shugaban NNPP na jihar, yayin da Yakubu Adamu Tela, ya zama mataimakinsa.
Abdullahi Ali Mohammed, ya samu kujerar sakataren jiha, sannan Hon. Amatiga Yila Naboth (ACG) ya zama sakataren yaɗa labarai.
Sauran da aka zaɓa sun haɗa da Musa Mohammed Gargajiga (Jagoran Matasa), Hajiya Hauwa Mohammed (Shugabar Mata), da Kabiru Mohammed Puma (Sakataren Tsara Ayyuka).
A jawabin da ya gabatar bayan rantsar da su, Mairungu, ya gode wa ’yan jam’iyyar bisa amincewa da suka nuna gare shi, inda ya bayyana cewa sabbin shugabannin za su yi aiki da adalci da tsari, tare da haɗa kowa domin ci gaban jam’iyyar.
Ya ce za su mayar da hankali wajen gina jam’iyyar daga matakin unguwanni, ƙara yawan mambobi, da ƙarfafa shiga matasa da mata a harkokin jam’iyya.
Wasu masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yaba da sabbin shugabannin, inda suka ce suna da damar gyara jam’iyyar kafin tunkarar babban zaɓe.
Haka kuma, sun yi godiya ga Jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, bisa tallafi da goyon bayan da ya bai wa taron.