HausaTv:
2025-12-13@16:12:12 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171

Published: 13th, December 2025 GMT

171-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddeen Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin wannan Shirin.

/////….Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan al-Mujtaba(a) dan Fatimah (s) diyar manzon Allah (s)  da muke kawo maku.

Mun fara Magana kan yadda mu’awiya dan Abusufyan ya ke bayyana riko da addinin musulunci a Zahiri bayan da y afara rigima da Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib(a) da kuma dansa Imam Al-Hassan(a) a bayansa. Wannan ya sa mutanen sham suna daukarsa mutumin kirki ne ya kuma kula da addini. Amma sulhunsa da Imam Al-Hassan (a) ya bayyanawa mutane kome. Don abinda ya faru bayan ya karbi iko da daular musulunci ya bayyana na farko kiyayyarsa ga addinin musulunci da kuma musulmu, musamman iyalan gidan manzonnAllah (s), Musamman Imam Ali (a) inda ya sunnata La’antar sa da kuma Imam Al-Hassan da Alhussain kan mimbarin musulmi, haka sauran sarakunan banu umayya suka dauka har zuwa lokacinda Umar dan Abdulaziz sarki na 8 daga cikin sarakunan Banu Umayya ya zo yah ana.

Banda haka yayi kokarin dutse hasken addinin musulunci gaba daya, said ai ya kasa yin haka. Ya sami nasarar sauya wasu daga sunnonin manzon Allah (s).

Sannan mun bayyana cewa Mu,awiya dan Abusufyan ya gaji kiyayya ga addinin musulunci a wajen iyayensa wadanda basu taba Imani da Allah basu kuma taba Imani da manzon Allah (s) ba.

Ba don kome bas ai don sun share shekaru kimani 20 suka yakar addinin musulunci suna yakar manzon Allah (s). babansa Abusufyan ne ya jagoranci yakin uhudu da Ahzaba, sannan shi yake goyon bayan yahudawa wadanda suka yaki manzon Allah(s).

Sannan a yakin Badar manzon Allah (s) ya kashe danginsa banu umayya da abokansu kurasihawa da dama, wadanda rashinsu ne yam aida shi shugaba a kan kuraishwa. Don haka a iya tunaninsa yana jiran ranar daukar fansa a kan manzon Allah (s) ko kuma zurriyarsa. Abinda kuma yayansa Mu\awiya da Yazid suka yi kenan.

Mun bayyana yadda ya bukaci Imam Ali (a) ya fito ya yaki Khalifa Abubakar don kwace hakkin khalifancin da suka kwace a hannunsa. Amma Imam Ali (a) ya gano mummunan manufarsa ta kawo karshen addinin musulunci idan har an fara yakin basasa a cikin al-ummar musulmi a lokacin. Sai ya ki amincewa, ya kuma fada masa cewa ya san irin sharrin da yake kullawa musulunci da musulmi.

Sannan Abusufyan ya jira har zuwa lokacinda Khalifa Uthman ya karbi Khalifanci, sannan ya fito ya fara bayyana kiyayyarsa ga manzon Allah (s) da kuma danginsa Banu Hashim.

Watarana ya shigo wajen Khalifa Usman, tunda ya makance a lokacin ya yi tambaya, shin akwai wani wand aba mu ba a nan sai suka ce masa babu. Sai ya masu, yak u Banu Umayya ku yi ta jujjuya Mulki a tsakaninsu, na rantse da abinda Abusufyan yake rantsewa da shi babu al-janna babu wuta. Sannan wata rana ya fito zuwa Uhudu, ya je kan kabarin Hamma ammin manzon Allah (s) yana kiransa yana cewa : Ya kai Baban Ammar wannan abunda muka yi sabani a kansa da takubbammu a halin yanzu ya koma hannun yayammu. Sannan yana ta tattaka kabarin.

Wannan shi ne Abu safyan mahaifin Ma’awiya, amma mahaifiyarsa Hindu, ta kasance tana kin manzon Allah (s) da danginsa fiye da mijinta. Saboda ya kashe danginta masu yawa a yakin Badar.

Da farko sunata Hindu diyar Utbatu dan Rabi, an kashe babanta a Utbatu dan Rabi a ranar Badar, sannan an kashe dan’uwanta Al-Walidu dan Ubtbah shi ma a yakin Badar sannan an kashe amminta dan uwan babanta Shaibatu dan Rabi shima a yakin Badar.

Sannan an kashe wadannan mutane uku ne a yakin fito na fito na daddaiku a yakin Badar, Kuma wadanda suka kashesu sune Aliyu dan Abitalib da Ubaidullahi dan Haritha dan Abdulmuttalib da kuma Hamza dan Abdulmuttalib, don haka dukkaninsu banu Hashim ne dangin manzon Allah (s).

Wannan tabon, da bakin ciki ya shiga zuciyar Hindu kuma har ta bar duniya tana bakin cikin kissan wadannan danginta. Tana kin manzon Allah(s) da kuma danginsa saboda su hatta bayan musuluntarta.

Malaman tarihin sun bayyana cewa bayan labarin kissan mahaifinta da amminta da kuma dan’uwanta ya zo mata, sai aka ce mat aba zaki yi taron makoki ba, ta ce, ai ba zata yi bas ai ta dauki fansa. Don haka shekara guda tana Shirin daukar fansarsu, har zuwa ranar Uhudu, ta sa aka kashe Hamza dan Abdulmuttalib, ammin manzon Allah (a). ta sa aka farke cikinsa, ta sa aka fidda hatansa ta gutsura ta tauna a bakinta, saboda haushi. Banda haka ta sa aka yi masa muthla, aka yanke hancinsa, da kunnuwarsa da gabansa.

A lokacinda manzon Allah (s) ya ga amminsa bayan Hindu ta yi masa haka, yayi bakin cikin bai bai taba yi ba. Yasa aka rufe gawarsa da mayafi kada wasu su gani, sannan yayi masa sallar mamaci har sau 70. Kafin ya sa shi a kabarinsa.

Mu’awiya dan abusufyan ya gaji kiyayyar manzon Allah (s) daga iyayensa wadanda ko da suka musulunta, manzon Allah ya sa shi mijinta cikin mu’allafatu kulubuhum, yana bashi kudade da dukiyoyi don rike shi cikin addina saboda bai yi Imani ga gaskiya ba. Ya dai mika wuya don an fi katrfinsa.

Malaman tarihi sun bayyana cewa a lokacinda aka kama Abusufyan ya kuma musulunta don kada a kashe shi, sannan aka shigo da shi makka yana fadar cewa, duk wanda ya shiga gidansa ya tsira sai hindu matarsa ta zo ta dakeshi a fuskansa, saboda ta yaya zai dauki wannan kaskancin.

An ruwaitota tana cewa ba zata sanya mai a kanta ba, ba zata yi kome na jin dadi ba sai ta dauki fansar kissan mahaifinta da amminta da kuma dan uwanta daga Muhammadu da sahabbansa. Kuma ta ce da ta san cewa kuka zai tafiyar da bakincinta da ta yi, amma kuka bai isa ba, sai fansa.

Bayan fatahin Makka manzon Allah (s) bai kusanto da Banu Umayya sosai ba. Saboda abinda ya kasance tsakaninsu da shin a tsawon tarihin gwagwarmaya don yada addinin musulunci.

Ya nesantar da wasu daga cikinsu daga Madina, kamar Hakam da dansa Marwan dan Hakam, da kuma Sa’id bin Ass dan Umayya, saboda cutar da shi da suke yi. Da walid

Wadannan su ne iyayen Mu’awiya dan Abusufyan, don haka ya gaji dukkan wadannan kiyayya da gaba ga banu Hashim dangin manzon Allah (s) daga wajensu. Kuma wannan ba Magana ce kawai muka fada ba, abinda ya faru a zahari a cikin shekaru 20 da yayi yana shugabancin al-ummar musulmi ne suka tabbatar da haka. Haka ma abinda yayansa da sauran danginsa suka yi har zuwa shekaru kimani 80 da suka yi suna iko sun tabbatar da haka. Wannan kiyayyar ya bayyana ga kowa, daga cikin musulmi larabawa da ajamawa. Har sai da ya kai ga ajamawa daga yankin Khurasan na kasar Iran karkashin jagorancin Abumuslimul Khurasani suka taso daga Iran suka zo suka kauda dangin banu umayya, suna masu kirari da daukan fansar iyalan gidan manzon Allah (s) daga dangin babu umayya.

Sannan saboda girman abinda zai faru a cikin al-ummarsa na bakin ciki, musamman ga iyalan gidansa wadanda kuma sune wasiyyansa, ya fadi al-amura da dama dangane da Mu’awiya dan abusufyan, inda yake cewa:

{Wani mutum wanda za’a tada shi ranar kiyama ba bisa addini ba zai bullo ta wannan hanyar sai, mu’awiya ya bullo ta hanyar} kamar yadda ya zo cikin littafin tarikhin umamma wal-muluk JZ 8 Sh 186.

Sannan mai littafin ‘Siffin’ ya kawo hadisi mai kama da wannan inda manzon Allah (a) yana cewa {Wani mutum wanda zai mutu a lokacinda zai mutu baya kan sunnata  zai bullo ta wannan hanyar, sai Mu,awaiya ya bullo ta hanyar}. Sh 247.

A wani hadisin wata mata ta zo wajen manzon Allah (s) tana neman shawararsa kan auren Mu’awiya sai ya ce mata kada ta aureshi don shi Sahluk .

A wani hadisin manzon Allah (s) ya sami ilmi daga ilmin gaibi kan cewa Mu’awiya zai zama shugaba nan gaba, sai ya gargadi musulmi dangane da shi, inda yake cewa {Idan kunga Mu’awiya yana khuduba a kan mimbari na ku kashe shi} wannan kamar yadda ya zo cikin Musnad Ahmad dan Hambal, JZ na 4 sh 421. Sannan a duk lokacinda Hassan dan Ali (a) ya tuna da wannan hadisin yakan ce {Basu aikata ba kuma ba zasu rabauta ba}.

Wannan shi ne rayuwar Mu’awiya dan Abu Sufyan a rayuwar manzon Allah (s), a Madina, bayan fatahin Makka.

Amma bayan manzon Allah(s). Khalifa Umar ya yi watsi da dukkan hadisan da manzon Allah (s) ya fada dangane da shi, ya kusanto da shi ya kuma bashi walin kasar Sham. Inda yayi shekaru 40 yana iko da yankin da ma daular musulunci daga can har ya mutu. Yayi haka ne bayan Yazid dan Abusufyan Yayan Mu’awiya walin sham na farko ya rasu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169 December 13, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon  A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta December 13, 2025 Ziyarar Da Shugaban Rasha Ya Kai Indiya Ta Kara Karfafa Dangantakar Mosko Da Delhi December 13, 2025 Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na  Venuzuela December 13, 2025 Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Matatar Mai ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699 December 13, 2025 Iran da Rasha sun jaddada aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu December 13, 2025 Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai December 13, 2025 MDD ta amince da kudurin da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agaji a Gaza    December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Mu awiya dan Abusufyan mu awiya dan Abusufyan dan Abusufyan ya a yakin Badar wadanda suka Mu awiya da Banu Umayya banu umayya

এছাড়াও পড়ুন:

Manchester United ta shiga zawarcin Sergio Ramos

Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester United ta fara zawarcin tsohon ɗan wasan Real Madrid Sergio Ramos, mai shekara 39,wanda ya bar Ƙungiyar Monterrey ta Mexico.

Ramos wanda a shekarun baya, United ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa, yanzu haka yana da damar komawa ƙungiyyar a matsayin kyauta.

Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky

United dai yanzu haka tana fuskantar matsaloli daga ’yan wasan baya, inda Harry Maguire ke fama da rauni, yayin da sauran ’yan wasan ke tafka kura-kurai.

Manchester dai yanzu haka ta amincewa mai horarwa ta Roben Amorim ya sayi ɗan wasan baya da tsakiya a watan Januairu.

Kawo yanzu dai ƙungiyyar na mataki na 6 da maki 25 cikin wasannin 15 da ta buga a gasar Firimiyya.

A ranar Litinin ƙungiyyar zata karɓi bakuncin Bournemouth a wasan mako na 16 a filin wasanta na Old Trafford.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Abubuwan Da Ba Ku Ji Ba Kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • Yadda Rashin Bincike Ke Haifar Da Yawaitar Mutuwar Aure
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169
  • Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
  • Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa
  • Manchester United ta shiga zawarcin Sergio Ramos
  • Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky