Ministan Makamashi: Iran Tana Da Sanayya Ta Ilimi Na Samar Da Hadari Domin Yin Ruwan Sama
Published: 10th, December 2025 GMT
Ministan makamashi na Iran Abbas Ali Abadi ya bayyana cewa; A halin yanzu Iran tana da ilimin aikewa da sanadarori cikin sararin samaniya da za su samar da hadari domin yin ruwan sama
Ministan makamashin na Iran wanda ya gabatar da jawabi a gaban majalisar shawarar musulunci ta Iran a jiya Talata ya ce; Aiki da aka yi a tsakanin gwamanti da majalisar dokoki da kuma cibiyoyin kwararru, shi ne ya kai ga samar da hukumar da take sanya idanu akan sauyin yanayi wanda ke iya samar da hadari da kuma yin ruwan sama.
Ministan ya yi Ishara da cewa sun bi matakai hudu domin ganin an isa wannan matsayin; Na farko dai shi ne; Amfani da na’urorin Radar domin bin diddigin yadda yanayi yake tafiya; Na biyu; yin kere-keren da su ka hada injinin samar da makamashi mai karfi; Sai kuma wasu fitilu da za su iya harba sanadarori na sanyi da zafi a sararin samaniya, da kuma jirage marasa matuki na musamman.
Bugu da kari ministan makamashin na Iran ya ce an kafa cibiyoyi 12 a fadin kasa domin sanya idanu akan yadda yanayi yake tafiya,wanda yana cikin mafi ci gaba a cikin wannan yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Babban Jami’in Banki December 10, 2025 Ganawa A Tsakanin Mataimakan Ministocin Waje Na Kasashen Saudiyya, China Da Minista Arakci Na Iran December 10, 2025 Antoni Gutress Ya Yi Allawadai Da Kutsen Da “Isra’ila” Ta Yi A Cibiyar Unrwa December 10, 2025 Iran da Saudiyya sun sake jaddada fadada dangantakarsu December 9, 2025 Faransa ta ce da hannunta aka dakile juyin mulki a Benin December 9, 2025 RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne December 9, 2025 An cire Tony Blair daga jerin wadanda zasu jagoranci Gaza December 9, 2025 Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon December 9, 2025 Trump Ya Yi Gefe Da Kasashen Turai Dangane Da Tattaunawa Kan Rikicin Ukraine December 9, 2025 Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba December 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana sabbin dabarun tsaron Amurka na cimma maradun gwamnatin Isra’ila ne.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce sabbin dabarun tsaron Kasa na Amurka (NSS) da ke bayyana ka’idojin Washington da muhimman manufofin harkokin waje a zahiri cimma maradun tsaro ne ga gwamnatin Isra’ila ne.
Esmaeil Baghaei ya yi wannan furucin ne a lokacin wani taron manema labarai, kwana biyu bayan gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta bayyana sabbin dabarun tsaron na NSS na 2025.
A kwanan ne gwamnatin Amurka ta sanar da sabbin dabarun tsaron na ta wanda ya tanadi har da soke bada mafaka ga ‘yan kasashen duniya 19.
Kasashe sun suka hada da Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia, Sudan, Burundi, Saliyo da kuma Togo, Afghanistan, Burma, Haiti, Iran, Yemen, Cuba, Laos, Turkmenistan, da Venezuela.
Matakin ya shafi ‘yan kasashen 19 da suka shiga Amurka a ranar 20 ga Janairu, 2021 ko bayan haka don tantance duk barazanar da ke akwai ga tsaron kasar da tsarin jama’a.”
Wannan shawarar ta zo ne bayan da Shugaba Donald Trump da Sakataren Tsaron Cikin Gida Kristi Noem suka yi kira da a tsaurara matakan tsaro kan shige da fice bayan harbin da aka yi wa wasu jami’an tsaron National Guard guda biyu a makon da ya gabata a Washington, D.C.
Wanda ake zargin, dan kasar Afghanistan ne mai shekaru 29 wanda aka ba shi mafaka a watan Afrilu, ya shiga Amurka a shekarar 2021 bayan janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan kuma ya taba yin aiki a wasu hukumomin gwamnatin Amurka, ciki har da CIA, a cewar kafofin watsa labarai na Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167 December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166 December 7, 2025 Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya December 7, 2025 Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba December 7, 2025 Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa December 7, 2025 Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya December 7, 2025 Venezuela: Ba Mu Tsoron Kaudin Amurka Na Wuce Gona Da Iri December 7, 2025 Iran Ta Zama Zakaran Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21 December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci