Shugaba Bola Tinubu ya yi alƙawarin hanzarta aiwatar da ci gaban Nijeriya ta hanyar amfani da fasahar kere-kere da tattalin abinci don samun nasarori irin na sauran ƙasashe masu tasowa kamar Brazil. A yayin da yake jawabi a ranar Talata a lokacin da ya gana da wasu ‘yan Nijeriya mazauna kasar Brazil, shugaba Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kawo sauyi ta hanyar kere-kere, gyare-gyare, da kuma samar da ci gaba mai dorewa.

Sin Da Kasashen Afirka Za Su Rubuta Sabon Babin Hakkin Dan Adam Bisa Ci Gabansu NRC Ta Dakatar Da Sufurin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna Bayan Hatsarin Da Ya Yi  “Dole ne mu sanya Nijeriya a gaba wajen ci gaban Afirka, ta hanyar amfani da fasahar kere-kere, tattalin abinci, da jajircewa wajen sauya irin kaddararmu,” in ji Tinubu a wata sanarwa da kakakinsa, Bayo Onanuga ya fitar. ‎ A cewar Tinubu, Nijeriya da Brazil a wani lokaci sun taba zama a matsayi daya. “Amma duba Brazil a yau, fasaharta da tsarin tattlin abincinta. Dole ne mu tambayi kanmu: menene suke da shi wanda ba mu da shi? Muna da ilimi, makamashi, da matasa. Muna da duk abin da muke bukata. Yanzu, dole ne mu tashi tsaye mu yi aiki.” Da yake yabawa al’ummar Nijeriya mazauna kasashen waje, Tinubu ya bukace su da su dauki kansu a matsayin masu ruwa da tsaki wajen gina sabuwar Nijeriya mai tushe a fannin fasahar kirkire-kirkire, al’adu, da kuma aiki tare. Ya amince da matsalolin da ‘yan kasar ke fuskanta sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da ake ci gaba da yi, yana mai jaddada cewa wadannan muhimman matakai ne na tabbatar da ci gaban kasa da za a gani nan gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace

 

Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC October 31, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala
  • Tinubu zai gana da Trump kan zargin kisan Kiristoci a Nijeriya 
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Jerin Gwarazan Taurarinmu
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede