Kalibaf: Iran Da Habasha Suna Bunkasa Alakokin Siyasa Da Tattalin Arziki
Published: 13th, December 2025 GMT
Shugaban Majalisar Shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf wanda ya gana da takwaransa na kasar Habasha Tagseh Chapo ya bayyana cewa: Kasashen biyu da suke da alakar diplomasiyya ta tsawon shekaru 70, sun Shata hanyoyin bunkasa alakokin tattalin arziki, siyasa da al’adu.
Haka nan kuma ya ce; kasantuwar kasashen biyu mambobi a cikin kungiyar Bricks yana kara dankon alakar da take tsakaninsu.
Shugaban Majalisar shawarar musuluncin ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya kuma ce; A shekarar da ta gabata na kai ziyarar aiki zuwa Addib Ababa,mun gana da Mr. Tagseh Chapo, inda na gayyace shi ya kawo Ziyara Iran, kuma an yi wannan ziyarar ce dai a lokacin da kasashen biyu suke mambobi na kungiyar Bricks.
Haka nan kuma shugaban Majalisar Shawarar musuluncin ta Iran ya ce; Habasha Babbar kasa ce a cikin nahiyar Afirka, musamman ta fuskar yawan jama’a, kuma ta yi tarayya da kasashen musulmi akan al’adu masu, musamman ma Iran.
Bugu da kari Kalibaf ya ce, alakar kasashen biyu ta fuskokin siyasa da tattalin arziki ta kai tsawon shekaru 70, kuma an Shata manufafofin da ake son cimmawa a wadannan fagagen.
A nashi gefen, shugaban majalisar dokokin kasar Habasha ya ce; Alakar kasashen biyu ta kai shekaru 70, kuma shekaru 60 da su ka gabata, sarkin kasarmu ya kawo Ziyara Iran,a wannan lokacin kuma tawaga mai girma daga Habashan ta sake zuwa Ziyara Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169 December 13, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Kudancin Labanon A Ci Gaba Da Keta Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta December 13, 2025 Ziyarar Da Shugaban Rasha Ya Kai Indiya Ta Kara Karfafa Dangantakar Mosko Da Delhi December 13, 2025 Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na Venuzuela December 13, 2025 Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Matatar Mai ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699 December 13, 2025 Iran da Rasha sun jaddada aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu December 13, 2025 Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan
Gwamnatin kasar Iran ta yi kakkausar suka ga kasashen duniya wadanda suka rage yawan kudaden da suke bayarwa don tallafawa yan gudun hijira daga kasar Afganisatan a cikin kasar Iran.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jakadan kasar Iran a MDD Amir Saeed Iravani yana fadar haka a jawabinda ya gabatar a taron kwamitin tsaro na MDD dangane da kasar ta Afganistan a jiya Laraba.
Iravani ya kara da cewa a halin yanzun Iran tana ci gaba da daukar bakwncin yan gudun hijiran Afganisatan fiye da miliyon 6 wanda ya hada da da shi da shansu da karatun yayansu da kuma tallafin da gwamnatin kasar take bayarwa na gidajen zamansu da ruwa da wutan lanatarki. Wanda a halin yanzu tana kashe akalla dalar Amurka billion $1o don yin hakan.
Kafin haka dai kwamitin tsaro na majalisar ya tsaida shawarar rage kashe 65% na kudaden da take bawa kasar Iran dangane da yan gudun hijiran Afganistan fiye da miliyon 6 da suke zama a kasar a shekara mai zuwa wato 2026.
Iravani ya musanta zancen tsohon jakafan Amurka a Zalmay Khalilzad wanda ke cewa ai Iran ta kore mafi yawan yan gudun hijiran Afganisatan a kasar. Ya ce wadanda Iran ta kora sune wadanda suka shiga kasar ba tare da takardun shaida ba. Wannan kuma an amince da shi a ko ina a duniya.
Iravani ya bayyana cewa, wannan matakin ya sabawa al-kawalin da kasashen duniya suka dauka na daukan nauyin yan gudun hijira a duniya. Ba zasu bar nauyin a kan kasa guda ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka December 11, 2025 Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan December 11, 2025 ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci