2025-12-02@07:33:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1136
«gidauniyar yaki da cutar kansa»:
Daga Ali Muhammad Rabi’u ’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda,...
A birnin Dublin na kasar Ireland an cire sunan tsohon sugaban “Isra’ila” Chaim Herzog,daga wata lambu na shakatawa a unguwar Ratgar, tare da maye gurbinsa da sunan Shahida Hind Rajab. Jaridar “Vadiot-Ahranot” ta ‘yan sahayoniya ta buga labarin cewa, hukumar birnin Dublin a Ireland ta amince da a sauya sunan shugaban “Isra’ila” ta shida Chaim...
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi, bayan wani taron gaggawa da Majalisar Koli ta ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar. Shugaban NARD, Muhammad Suleiman, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya bayyana cewa an dakatar da...
Asibitin Kula da masu lalurar kwakwalwa da ke Kaduna na Jagorantar Sauye-Sauren Lafiyar ƙwaƙwalwa a Arewacin Najeriya — Farfesa Aishatu Armiya’u Ta Bayyana Muhimman Nasarori a Shugabanci da Ayyuka da Hadin Gwiwa Shugabar gudanarwa kuma daraktar lafiya ta Asibitin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa dake Kaduna, Farfesa Aishatu Yusha’u Armiya’u, ta tabbatar da kudirin asibitin...
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya. CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan...
Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kyalian Mbappe ya samu nasarar zura kwallaye huɗu rigis a ragar Olympiacos a wasan mako na biyar na kofin zakarun nahiyyar turai da suka buga a yammacin jiya Laraba. Real Madrid dai caskara Olympiacos 4-3 ne a wasan, lamarin da ya ba ta damar haɗa...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta gano harsasai 210 da aka jefar a kan babbar hanyar Zariya zuwa Funtuwa, a unguwar Dogo Itace da ke Samaru, Zariya. Lamarin ya faru ne lokacin da DPO na Samaru tare da tawagarsa suke sintiri a kan hanyar. Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Juyin mulki ya...
Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
Kungiyar ta kasa da kasa mai gudanar da a ayyukan agaji, ta sanar da janye ma’aikatanta daga asibitin Darfur, bayan da aka bude musu wuta, ya kuma kai ga kashe daya daga cikin masu aikin agaji. Kungiyar ta yi kira ga rundunar kai daukin gaggawa RSF da ta tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiyar...
Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su gudanar da muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Mai bai wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya sanar cewa, taron gwamnonin Arewa da aka shirya a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya....
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan. A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila. Mayaƙan...
Yayan kungiyar yan ta’adda ta ‘the Islamic State West African Province (ISWAP) ta bada sanarwan kamawa da tsare yan mata 13 a karamar hukumar Askira-Uba na jihar Borno a jiya Lahadi. Jaridar Daily Trust ta Nageriya ta nakalto Abdullahi Askira dan majalisar dokokin jihar Borno mai wakiltan Askira yana tabbatar da labarin ya kuma kara...
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da dukkan ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya, sakamakon harin da ta ce jami’anta sun fuskanta a Jihar Imo. Ƙungiyar ta bayyana cewa wasu jami’an ’yan sanda ɗauke da makamai ne suka kai wa ma’aikatanta hari a Egbu 132/33kB Transmission...
Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA) ta yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalar ambaliyar ruwan da ke addabar al’ummar Ƙaramar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa. Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana hakan bayan karɓar roƙon da jama’ar yankin suka miƙa ta hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar, Jamilu Ɗan Malam Mai...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane...
Ƙaramin kwamitin majalisar dokokin Amurka kan harkokin kasashen Afirka ya yi wani zama kan batun zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Nijeriya da batun yadda Shugaba Donald Trump ya ayyana kasar a matsayin “wadda Amurka ke nuna damuwa a kanta kan walwalar addini,” sai dai kawunan mambobin majalisar sun rarrabu a kan...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin tallafin hadin gwiwa na kowace shekara domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana...
Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha. Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da kasar...
Ƙungiyar ɗalibai ’yan Jihar Kano ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da su kawo ƙarshen taƙaddamar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU. Ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa reshen Jihar Kano (NAKS) ta roƙi shugabannin da su gaggauta aiwatar da duk mai yiwuwa domin warware taƙaddamar da ke tsakanin gwamnati da ASUU....
Kwamitin hukumar hana yaɗuwar makamin nukiliya IAEA a Majalisar Dinkin Duniya, ya buƙaci ƙasar Iran da ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka. Wannan dai na zuwa ne bayan kwamitin ya amince da wani ƙuduri da zai tilasta wa Iran bayyana musu yawan makamashin nukiliyarta. An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da...
Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Iran da malesiya sun cimma yaejejeniyar kara fadada dangantar yin aiki tare a bangaren Addinin da Ala’adu musamman a bangaren kimiyar alkur’ani bayan tarurruka da manyan jami’an gwamnati suka yi a birnin kuala Lumpur babban birnin kasar, Wannan yarjejeniyar za ta kara karfafa hadin guiwa tsakanin manyan kasashen musulmi adaidai...
Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga...
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta...
Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya. Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano,...
Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da...
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Iran tana da kyakkyawar alaƙa ta musamman da kuma al’adu da membobin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran ya ce, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), kuma...
Wasu masu ibadar Umara 42 sun mutu bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kusa da birnin Madina da ke kasar Saudiyya. Dukkan masu ibadar ’yan kasar Indiya ne, kuma hatsarin ya ritsa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Makka bayan kammala ziyara a birnin Madina. Ministan harkokin wajen...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025 Manyan Labarai Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon November 17, 2025 Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025...
Gwamnatin kasar ta DRC da kuma kungiyar ‘yan tawaye ta M23 sun rattaba hannu akan wasu takardu da su ka kunshi yadda za a kai ga samun zaman lafiya mai dorewa a gabashin kasar. A jiya Asabar ne dai bangarorin biyu su ka rattaba hannu akan takardun a birnin Doha na kasar Qatar domin kawo...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci al’umma su ƙara kula da tsaro tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro, yayin da ’yan bindiga suka fara kai hare-hare a ƙauyukan da ke iyaka da Jihar Katsina. Sarkin, ya yi wannan kira ne yayin ziyarar jaje da ya kai wa al’ummar...
Amfani da jami’an tsaro: Abu na farko dai dole ne kungiyoyi su yi aiki tare da yansanda, NSCDC, da jami’an tsaro na sirri wajen tsara tsare-tsaren tsaro a ranar da za su buga wasa, domin kuwa Bahaushe na cewa, “tun za a, ake shiri ba sai an dawo ba”, hakazalika yana da mahimmanci a...
Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma ta yi kira da a girmama hurumi da cikakken yancin Venezuela. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce...
Kifi mai nama ko naman rago, Ataruhu da tattasai, Barkono ja, Albasa, Daddawa, Gauta (baobab leabes),Yaji, gishiri da maggi, Manja ko man gyada. Yadda ake hada miyar: A wanke kifi ko naman da kyau, a nika attaruhu, tattasai, barkono ja da albasa a hade. A zuba kifi ko naman a tukunya tare da dan...
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari
Ta ce, “Kungiyar ta fi kai hare-hare a shagunan EE, inda suke amfani da barazana da tashin hankali wajen tilasta ma’aikata su bude dakunan ajiya na sirri kafin su gudu da wayoyi masu tsada da sauran na’urori.” A jimlace, sun sace kayayyaki da darajarsu ta kai fam miliyan £240,000. Jami’an tsaro sun gano masu laifin...
Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin...
An Gudanar Da Taro Mai Taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa” A Johannesburg Dake Afirka Ta Kudu
An gudanar da taro mai taken “Shugabancin Duniya: Ayyukan Matasa”, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya dauki nauyi, a Johannesburg dake Afirka ta Kudu a ranar 11 ga wata. Jigon taron shi ne, “Matasa su tattauna kan tsarin shugabancin duniya, kuma su hada kai don samar da makoma irin...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sin Ta Bukaci Japan Ta Daina Yi Wa Masu Fafutukar “‘Yancin Kan Taiwan” Ingiza Mai Kantu Ruwa November 12, 2025 Daga Birnin Sin Peng Liyuan Da Sarauniya Letizia Ta Spain Sun Ziyarci Cibiyar Kula Da Nakasassu A Beijing November 12, 2025 Daga Birnin Sin Madalla Da...
Shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin da shugaban ma’aikatan fadar Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila da Dr Abdullahi Umar Ganduje, sun ziyarci zauren Majalisar Wakilai ranar Alhamis domin shaida sauya sheƙar ƴan majalisa biyu daga NNPP zuwa APC. Ƴan majalisar da suka sauya sheƙar sun haɗa da Hon....
Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa...
Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25
1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari...
Gidauniyar fadakar da al’umma akan dokoki da ka’idoji ta Nijeriya ta kaddamar da kwamiti a jihar Nasarawa domin aiwatarwa da sa ido kan shirin mata, zaman lafiya da tsaro, da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa wajen gina zaman lafiya a cikin jihar. Daraktan gudanarwa na gidauniyar, Mista Peter Maduoma, ne ya bayyana hakan a Lafia yayin...
Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su
Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar. Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na...
Kungiyar Kare Muradun Musulmai (MURIC) ta bukaci a gaggauta tsige Farfesa Joash Amupitan daga shugabancin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), saboda matsayinsa kan batun rashin tsaro a Najeriya. Aminiya ta rawaito cewa, a cikin wani rubutu a baya, Amupitan wanda a lokacin malami ne a Jami’ar Jos da ke Jihar Filato, ya ce “abu ne...
Uwargidan Shugaba Xi Jinping na kasar Sin Peng Liyuan, da Sarauniya Letizia ta kasar Spain, wacce ke rakiyar Sarki Felipe na VI na Spain a ziyarar da ya kawo kasar Sin, sun ziyarci cibiyar gwaji ta kula da nakasassu ta Beijing a yau Laraba. A cibiyar, Peng da Letizia sun saurari bayanan da aka yi...
A yau Laraba ne aka sanar da zaman Iran memba a cikin wannan kungiyar ta ( ISKO) wacce aka bude reshenta a cikin kasa tun a 2011. Farfesa Rahmatullah Fattahi ne ya bude reshen kungiyar ta ” Ilimomin Tattara Bayanai Da Kere-Kere” wacce kuma ta ci gaba da gudanar da ayyukanta har zuwa 2019. An...
A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni. Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati,...
Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya sanya hannu kan dokar kafa cikakkiyar rundunar tsaro ta kasa a wannan Laraba. Maduro ya jaddada bukatar kafa cikakkiyar rundunar tsaro, wacce ta hada dukkan cibiyoyin soja na gwamnati da kuma dakarun sa kai najama’a a safiyar yau Laraba. Dokar na da nufin tsara da kuma hada dukkan cibiyoyin gwamnati,...
Ana fargabar cewa an yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara huɗu fyaɗe a ƙaramar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe. Da yake zantawa da manema labarai fyaɗe da safiyar Litinin, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta samu mummunan rauni a al’aurarta. John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi An ceto mutane 86...
Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdel-Aty ya karbi bakuncin Wakiliyar Musamman ta Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Libya, Hanna Tetteh, a matsayin wani bangare na ci gaba da hadin gwiwa da tattaunawa ta kut-da-kut da Majalisar Dinkin Duniya game da abubuwan da ke faruwa a Libya da kuma goyon bayan kokarin da ake...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da bunkasa hanyoyin sufuri a fadin jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya kaddamar da wani muhimmin aikin gina hanyoyi a karamar hukumar Mallam Madori. Yayin taron kaddamarwar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa aikin...
Gidauniyar Sarkin Musulmi kan Zaman Lafiya da Ci-gaba ta bayar da tallafin kayan da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.3 domin tallafa wa makarantun Jihar Kebbi. Kayan da aka bayar sun haɗa da kujeru da teburan karatu da aka samar karkashin shirin gidauniyar, domin rabawa makarantun jihar a matsayin gudummawa don inganta yanayin ilimi. Sarkin...