A yayin da ake gudanar da shagulgulan ranar zaman lafiya ta Duniya ta Bana, Kungiyar rajin tabbatar da zaman lafiya da hadin Kai da kuma cigaban Arewacin Nigeria ta yi Kira ga Gwamnati a dukkan matakai da kuma Hukumomin tsaro su karfafa amfani da bayanan tsaro na sirri wajen kare rayukan al’ummar Kasa.

Shugaban Kungiyar ta ACI Dakta Abdullahi Idris ya yi wannan Kira a wani taron manema labarai da Kungiyar ta Kira a Kaduna.

Ya yi bayanin, Kungiyar ta lura da matakan da Gwamnati da Hukumomin tsaro suka dauka domin maido da zaman lafiya a wasu sassan Arewcin Kasar nan.

Dakta Abdullahi Idris ya ce, matakan da aka dauka abin a yaba ne, Amma kuma sun yi kadan matuka wajen magance matsalalon tsaro da suka addabi Kasar nan.

Ya jadda da bukatar ganin Shugabanni da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro su daina nuna son zuciya da siyasantar da sha’anin tsaron Kasa domin amfanin al’umma.

Dakta Abdullahi Idris ya tunatar da Shugabanni cewa Allah zai tambaye su yadda suka Shugabanci al’umma, a ranar gobe kimyama.

Daga nan sai Shugaban Kungiyar ya bukaci Gwamnati a dukkan matakai da Hukumomin tsaro su rubunya kokarin da suke yi kana su yi amfani da rahitannin tsaro na sirri wajen maganin wannan matsala ta tsaro.

COV/LERE

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Yan Najeriya Rana zaman lafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar amincewa da dage takunkumin da ya sanya wa al-Julani

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’a a ranar Alhamis domin amincewa da daftarin kudirin da zai cire takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa Shugaban rikon kwaryar kasar Siriya Abu Muhammad al-Julani da Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar Anas Khattab, inda kasashe 14 suka kaɗa ƙuri’a kan amincewar, yayin da kasar China ta kauracewa kada kuri’a.

Daftarin kudurin, wanda Amurka ta rubuta kuma ta gabatar, ya yi kira da a dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba wa al-Julani da Khattab.

A cewar jami’an diflomasiyyar Majalisar Dinkin Duniya, ofishin jakadancin Amurka ya rarraba daftarin kudurin ga mambobi, kuma an sanya shi a karkashin “tsarin shiru” har zuwa safiyar Laraba. Wannan matakin na tsari ya ba wa mambobin Majalisar Tsaro damar gabatar da koke kafin a shirya kada kuri’a.

Daftarin kudurin ya sami kuri’u 14 na goyon baya, yayin da China ta kauracewa kada kuri’a.

Ya bukaci akalla kuri’u tara a goyon baya, kuma babu wani takunkumi daga Rasha, China, Amurka, Faransa, ko Birtaniya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Karuwar Matsalar Jin Kai Mafi Girma A Duniya A Sudan Saboda Ci Gaba Da Masifar Yaki A Kasar November 7, 2025 An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas November 7, 2025 Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jinin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar November 7, 2025 Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Ce: Amurka Ta Bukaci Duba Kudurin Neman Kafa Rundunar Kasa Da Kasa A Gaza November 6, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kashe Mutum Guda Tare Da Jikkata Wasu Uku A Kudancin Lebanon   November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nigeria: Za A Ci Gaba Da Zaman Shari’ar Shugaban Kungiyar “IPOB” A ranar 20 Ga Watan Nan Na Nuwamba
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi a Aso Rock
  • Matsalar Tsaro: Mun samu gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • Matsalar Tsaro: Mun sami gagarumin ci gaba a shekaru biyu – Tinubu
  • Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti
  • Majalisar Wakilai Ta Yi Tir Da Harin Da Aka Kai Wa Tawagar Ɗan Majalisar Neja
  • Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya
  • Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro
  • DRC: Kungiyar M23 Ta Kafa Kotunanta A gundumar Kivu Ta Arewa