2025-04-30@19:00:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 332
«rashawa»:
Bayanai daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 35 dane suka hada da kananan yara aka kashe a wanisabon kisan kiyashi na Isra’ila a zirin Gaza. A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 35 tare da jikkata 109 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon...
Amurka ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu kamfanoni 7 da ta ce suna da hannu wajen siyar da man kasar Iran, a wani mataki na kara matsin lamba duk da tattaunawar da aka yi kan shirin nukiliyar Iran. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar ta ce, bangarorion da takunkumin ya shafa sun...
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki...
Mataimakin ministan harkokin waje mai kula da bangaren siyasa, ya bayyana cewa; Ko kadan ba a bijiro da batun dakatar da tace sanadarin uranium a Iran ba, ko kuma batun makamanta masu linzami. Mataimakin ministan harkokin wajen na Iran ya tabbatar da cewa, wadannan abubuwan biyu wato dakatar da ci gaba da tace sanadarin uranium...
Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa aiwatar da jerin manyan ayyuka a fadin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata. Hakimin ya yi yabon ne yayin bikin kaddamar da wani littafi a garin Kafin Hausa. A jawabinsa yayin taron, Gwamna...
A wani hari da jirgin sama maras matuki da dakarun kai daukin gaggawa su ka kai akan sansanin ‘yan hijira a Jahar ” Nahrun-Nil” a Arewacin Sudan sun kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu, haka nan kuma sun yi sanadiyyar yanke wutar lantarki a yankin. Kafar watsa labaru ta “al-muhakkak” ta ce; Dakarun...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya yaba da yadda tattaunawa da Amurka kan shirin Nukliyar kasar yana tafiya kamar yadda ta dace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Aragchi yana fadar haka bayan, bayan ya fito daga taron tattaunawa ta ukku wanda aka gudanar...
Jiragen yakin HKi sun kai hare-hare da safiyar yau Asabar a birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama. Mutane 4 sun yi shahada a harin na jiragen ‘yan sahayoniyar akan wani gida dake unguwar “al-Sabrah’ a kudancin birnin Gaza. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wani harin da...

Kasar Sin Ta Goyi Bayan Rawar Da Hukumar IAEA Ke Takawa Wajen Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diflomasiyya
Li ya kara da cewa, Sin da Rasha sun bayyana goyon baya ga Iran wajen karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da hukumar IAEA. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...

Muscat Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin Domin Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka
Ministan harkokin wajen Iran ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a yau domin gudanar da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya sanar da cewa: A yau ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya nufi birnin Muscat na kasar Oman a karkashin jagorancin tawagar diflomasiyya...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi kashedin kan illar ci gaba da killace Gaza da kuma hare-haren ta’addancin ‘yan mamaya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da rashin hukunta ‘yan sahayoniyya kan kisan gillar da suke yi a zirin Gaza da Gabar yammacin kogin Jordan, da kuma mamayar wasu yankunan...
Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran. A yayin taron...

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma...
Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jinjinawa kasashen Sin da Rasha a matsayin abokan hulda na kut-da-kut da kasar, yayin da ya isa birnin Beijing domin yin shawarwari da manyan jami’an kasar Sin, gabanin yin tattaunawa zagaye ta uku da Amurka kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Abbas Araghchi ya shaida wa kafar yada...
Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba, shugaban kasar Iran zai kai Ziyara can kasar. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci bayan ganawa da takwaransa na China ya ce; Na yi doguwar ganawa da ministan harkokin...
Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Iran ba za ta taba gudanar da shawarwari kan tsaronta ba A cikin jawabinsa na shirye-shiryen shirin zaman taron Carnegie kan manufofin nukiliya na kasa da kasa da aka soke a yanzu, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa kamfanonin Amurka za su iya cin gajiyar...

Al’ummar Gaza Suna Tsananin bukatar Agaji Da Kiran A Tilastawa Gwamnatin Mamayar Isra’ila Bude Mashigar Yankin
Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata...
Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar ta bayyana...
Gwamnatin Amurka ta kakabawa kamfanonin kasar Iran sabbin takunkumi, duk da tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyar. Ofishin kula da kadarorin waje na ma’aikatar baitul malin Amurka (OFAC) ya sanar a cikin wata sanarwa jiya Talata cewa, ya kara sunan wani dan kasuwa dan kasar Iran, Seyyed Assadollah Emamjomeh da kamfaninsa cikin jerin...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana farin cikisa bisa da shirye-shiryen da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa NAHCON, ta gudanar ya zuwa yanzu, domin aikin Hajjin shekarar 2025. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa,...
Kamfanoni da masana’antun America da dama sun dakatar da harkokinsu, dubban mutane sun rasa aikin yi. Don haka wannan mataki bai haifar da sakamakon da Mr. Trump ke bukata ba, musamman idan aka yi la’akari da yadda kasuwar hannayen jari ta shiga cikin rudani, gami da hali na rashin tabbas da manoman America suka samu...
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba su da niyyar gudanar da tattaunawa da Amurka a fili Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba...
Jamuhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada matsayinta kan batun tace sinadarin yuraniyo. Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta bayyana cewa, Iran na kokarin yin shawarwari ne domin samar da amana da samar da gaskiya game da shirinta na nukiliya domin dage takunkumi kanta. A cikin taron manema labarai na mako-mako da ta...
Kungiyar Hamas ta yi kira ga jami’o’in Yammacin Kogin Jordan da su shirya zanga-zangar nuna goyon baya ga Gaza da kuma kin amincewa da kisan kare dangi Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta yi kira ga jami’o’in Yammacin Kogin Jordan da su tashi tsaye wajen gudanar da gangami da zanga-zanga a ranar Talata, domin nuna...
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da yadda tattaunawa tsakanin kasarsa da Iran ke gudana, yana mai bayyana ta a matsayin mai matukar kyau. Da yake magana da manema labarai a fadar White House jiya litinin, Trump ya ce tattaunawa da akayi da jami’an Iran sun yi matukar inganci. A ranar 12 ga watan...
Kasashen Masar da Kuwaiti sun fitar da sanarwa a yau Litinin ta yin tir da kiraye-kirayen da wasu yahudawa masu tsattsauran ra’ayi suke yi domin a rusa masallacin kudus, suna masu yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa domi a tsayar da tsokanar da Isra’ilawa suke yi. Kasashen biyu dai sun fitar da wannan sanarwar...
Wasu Falasdinawa sun yi shahada a cikan kwana na 35 a sabon yakin da yahudawan sahayoniyya suka sake daurawa kan Zirin Gaza Sojojin gwamatin mamayar Isra’ila suna ci gaba da yakin kisan kiyashi a Zirin Gaza tun bayan sake ci gaba da yau tsawon kwanaki 35 da suka gabata, bayan da Fira minista Benjamin Netanyahu...
Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudirin baya bayan nan na Isra’ila na kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa domin tsagaita bude wuta a Gaza, tana mai kiran hakan a matsayin wani yunkuri na gurgunta ‘yancin Falasdinu. Tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Hamas ta tsaya cik, inda Isra’ila ta matsa kaimi...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yaba Da Zaman Tattaunawan Iran Da Amurka Zagaye Na Biyu A Birnin Roma
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tattaunawa da Amurka an yi ta ne cikin yanayi mai inganci da hangen nesa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, wadda Oman ta shiga tsakani a birnin Roma na kasar Italiya, da cewa an gudanar...

Mai Ba Da Shawara Ga Jagora Ya Bayyana Cikakken Ikon Tawagar Masu Tattaunawan Iran A Zaman Shawarwari Da Amurka
Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Masu sasantawa Iran a birnin Roma suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu Ali Shamkhani mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa: Masu gudanar da shawarwari na Iran sun tafi birnin...
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Irna” cewa; An sami cimma matsaya a tsakanin tawagogin Iran da na Amurka akan cewa a ranar Laraba mai zuwa za a dora daga inda akan tsaya a tattaunawar Nukiliya,” Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kara...
Iran da Amurka za su shiga zagaye na biyu na tattauna batun taƙaita shirin nukiliyar Tehran a yau Asabar. Masu shiga tsakani za su haɗu a birnin Roma bayan zagayen farko na tattaunawar da aka yi a makon jiya a Oman. Ministan harkokin wajen Iran ya ce za a iya cimma yarjejeniya idan Amurka ba...
Yau Asabar Washington da Tehran, ke tattauanwa a birnin Rome na kasar Italiya, wace ita ce ta biyu a shiga tsakanin kasar Oman kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Tattaunwar wacce ba ta gaba-da-gaba ba an gudanar da irin ta a ranar Asabar data gabata a birnin Muscat na kasar Oman, inda bangarorin biyu...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata halarci zaman tattaunawa da kasar Amurka kan shirin kasar na makamashin Nukliya tare da fatan bangaren Amurla ma tana bukatar cimma yarjeniya da ita, matukar Amurka bata kawo wani abu wand aba zai yu Iran ta amince ba. Tashar talabijin ta Presstv a...
Kasar Chaina ta musanta zargin shugaban kasar Ukraine ga kasar, dangane da tallafawa kasar Rasha da makamai. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar wajen kasar China Lin Jian yana fadar haka a safiyar yau Jumma’a ya kuma kara da cewa, kasar China bata taba daukar bangaren a yakin na Ukraine...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayyana Cewa: Makiya Suna Adawa Da Fadada Alaka Tsakanin Iran Da Saudiyya
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna adawa da fadada dangantakar Iran da Saudiyya Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da ministan tsaron Saudiyya Khalid bin Salman a jiya Alhamis. A yayin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa, alakar da ke tsakanin...
Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horaswa gaa malamai daga dukkan kananan hukumomi 27 domin shirya su, su horar da maniyyata aikin hajjin 2025 na jihar. Darakta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya ga sabbin masu wa’azin...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta shirya taron horaswa gaa malamai daga dukkan kananan hukumomi 27 domin shirya su, su horar da maniyyata aikin hajjin 2025 na jihar. Darakta Janar na hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani na kwana daya ga sabbin masu wa’azin...
Sayyid Ammar Hakim shugaban jam’iyyar ‘ تيار الحكمة الوطني’ na kasar Iraki ya bayyana cewa kasar Iraki ce kasa ta farko wacce zata amfani da tattaunawa tsakanin Iran da kasar Amurka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sayyid hakim yana fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa kasashen Iran da...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa babu batun tattaunawa kan shirin kasar na tace sinadarin Uranium wanda ke a matsayin wani bangare na shirin nukiliyar kasar na zaman lafiya. Abbas Araghchi ya kuma ce tattaunawar Tehran da Washington ba za ta haifar da wani sakamako ba idan ana amfani da matsin mata lamba da...
An yanke wa tsohon shugabar ƙasar Peru, Ollanta Humala hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari. Wata kotu a ƙasar ce ta yanke masa hukuncin bisa samunsa da laifin halatta kuɗin haram a badaƙalar cin hanci da katafaren kamfanin gine-gine na Brazil Odebrecht ke yi don samun kwangila. Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC —...

Kakakin Sojojin Kasa Na Dakarun IRGC Ya Ce Butun Tsaron Kasar Iran Da Karfin Sojojin Kasar Ba Abinda Tattaunawa Da Makiya Bane
A wani taron manema Labarai a nan birninTehran, kakakin sojojin kasa na dakarun IRGC a nan JMI, Burgediya Janar Ali Muhammad Naeini ya fadawa yan jaridu cewa, tsaron JMI da kuma makamanta baa bin tattaunawa ne da makiya ba. Ya kuma kara da cewa, tsaron kasar Iran jan layi ne, haka ma, karfin sojojin kasar....

Jagoran Ya Ce: Iran Ba Ta Kallon Tattaunawan Iran Da Amurka A Matsayin Kawo Karshen Takaddama A Tsakaninsu
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa: Za a gudanar da zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukuliyar Iran zagaye na biyu ne a birnin Muscat na kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Zaman tattaunawa zageye na biyu wanda ba na kai tsaye ba, tsakanin Iran da Amurka...

Lauyoyin London Suna Tattara Bayanai Kan ‘Yan Birtaniya Da Suka Yi Yaki Cikin Sahun Yahudawan Sahayoniyya A Gaza
Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki...
Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 tare da jikkata wasu 69 a cikin awa 24 a yankin Gaza, inda ta kai harin sama a wani asibiti da ke yankin Khan Younis. Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta sanar cewa jiragen Isra’ila sun kashe wani jami’in lafiya tare da jikkata wasu tara a Asibitin Kuwaiti da ke yankin Al-Musawi...