Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza
Published: 12th, December 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Faidan ne ya bayyana cewa; kasarsa za ta iya daukar nauyin wararen matsalar Falasdinu, kuma a shirye take ta aike da sojoji zuwa yankin na Gaza idan bukatar hakan ta taso.
Fidan ya fada wa kamfafen watsa labaru cewa; Tukriya a shirye take ta yi duk abinda za ta iya yi, ta kuma dauki nauyin da ya dace akan batun Falasdinu.
A can Amurka kuwa, manzon musamman na Amurka akan harkokin yammacin Asiya, Barrack ya fada wa jaridar “Jerrusalem Post” cewa: Kasar Turkiya tana da sojoji masu karfi, kuma tana hulda da Hamas, a dalilin hakan shigarta cikin rundunar da za a aike Gaza, zai yi amfani.”
A ranar 18 ga watan Nuwamba ne dai kwamitin tsaro na MDd ya amince da rinjaye akan wani kuduri da Amurka ta gabatar domin kawo karshen yakin Gaza. A karkashin wannan kudurin zai a kuma aike da sojojin kasa da kasa daga nan zuwa karshen 2027.
Kudurin ya kuma tanadi cewa za a kafa gwamnati a yankin na Gaza ta kwararru wacce kwamijin tsaro ne zai rika kula da tafiyar da ita.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Yi Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi AkanDoron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Hamas: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji
Al’ummar ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sakkwato sun bayyana farin ciki bayan samun labarin kashe fitaccen ɗan bindiga da ya dade yana addabar yankin gabashin jihar, Kacalla Kallamu.
Rundunar Sojoji ta 8 ta hallaka jagoran ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a wani samamen haɗin gwiwa da aka kaddamar a ƙaramar hukumar Sabon Birni.
Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – SoyinkaWata majiyar soja da ta tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar Talata ta bayyana samamen a matsayin “babbar asara ga cibiyar ’yan bindigar Bello Turji,” tana mai cewa Kallamu shi ne babban na hannun daman Turji.
A cewar majiyar, an kashe Kallamu tare da wani daga cikin manyan masu samar wa Turji kayayyakin aiki a lokacin samamen da aka gudanar da safe a kauyen Kurawa ranar Litinin.
Majiyar ta ƙara da cewa aikin ya samu muhimmiyar gudunmuwar kungiyoyin sa‑kai na yankin.
“Mun dade muna bibiyar Kallamu. Kashe shi wata babbar nasara ce wajen raunana karfin ’yan bindigar da ke Sabon Birni da kewaye,” in ji majiyar.
Mamacin, wanda asalin ɗan Garin Idi ne a Sabon Birni, ya dade yana addabar al’ummar yankin.
Ana zargin ya gudu zuwa Jihar Kogi bayan ya tsere wa luguden wutar sojoji a watan Yuni 2025, amma ya sake shigowa yankin kwanan nan ba tare da an sani ba.
Majiyar ta yaba da ƙarin bayanan sirri da ake samu daga al’ummomin yankin, tana mai cewa haɗin kai tsakanin mazauna yankin da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin baya‑bayan nan.
Manema labarai sun ruwaito cewa an ci gaba da murnar labarin a Sabon Birni, yayin da mashawarcin musamman ga Gwamna Ahmad Aliyu kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya yaba wa dakarun bisa “ci gaba da jajircewa da ƙwarewa” wajen yaƙi da ’yan bindiga.
Mutanen garin Sabon Birni sun fito maza da mata suna murnar nasarar da aka samu, har suna cewa suna jin wannan rana kamar ta Sallah.
Sun yi fatan a ci gaba da samun nasarori irin wannan domin kawar da ’yan bindiga a yankin, a jihar, da kuma Arewacin Najeriya gaba ɗaya.