Daga Usman Muhammad Zaria

Ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Jigawa za ta kashe naira milyan dubu 10 da milyan 599 wajen gudanar da manyan ayyuka da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara.

Kwamishinar ma’aikatar, Hajiya Hadiza Abdulwahab, ta bayyana hakan lokacin kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa.

A cewar ta, za su mayar da hankali wajen inganta shirye shiryen bunkasa rayuwar mata da al’amuran da su ka jibinci kananan yara domin bada kariya ga masu rauni a cikin al’umma.

Hajiya Hadiza Abdulwahab ta ce ma’aikatar ta samu nasarori wajen aiwatar da tanade tanaden kasafin kudin 2025, yayin da za su ci gaba da daukar matakan da su ka dace domin inganta ayyukan su a sabuwar shekara.

Ta kuma yi nuni da cewar, batun kula da rayuwar masu rauni a cikin al’umma ya kasance ginshiki daga cikin kudurorin Gwamna Malam Umar Namadi.

Hajiya Hadiza, ta bada tabbacin aiki tukuri domin samun nasarar da ake bukata a sabuwar shekara.

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa Ma aikatar Mata

এছাড়াও পড়ুন:

An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa”

Masu aikin ceto a Falasdinu, sun fada a ranar Litinin din da ta gabata cewa; An fito da gawawwakin shahidai 98 da aka binne su cikin gaggawa a lokacin yaki, a cikin harabar asibitin al-Shifa a cikin birnin Gaza.

An fito da gawawwakin ne dai domin kai su zuwa sanannun makabartun da ake da su a cikin yankin na Gaza,domin binnewa.

Sanarwar hukumar ceton ta ce; A tsakanin shahidan da akwai wasu 55 da ba iya tantance ko su wanene ba, sai dai an mika su ga kwararrun likitoci domin tantance da gano ko su wanene.

Ma’aikatan agaji suna ci gaba da fito da wasu gawawwakin na shahidai da aka binne a cikin asibitin, domin tantance su, kuma ana yin hakan ne dai a cikin kare hurumin matattun.

A farko-farkon kwanakin yakin Gaza, sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, sun kai hari akan wannan asibitin, wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane 500 a lokaci daya.

A wani labarin na daban, ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa; A cikin sa’oi 24 da su ka gabata an kai gawawwakin shahidai 5, uku daga cikinsu sun kwanta dama ne sanadiyyar sabbin hare-haren da sojojin mamaya suke kai wa, duk da cewa an tsagaita wutar yaki. Sauran shahidan biyu kuwa wadanda aka fito da su ne daga karkashin baraguzai na gine-ginen da ‘yan sahayoniya su ka rusa gidaje da mutane a cikinsu a tsawon ranakun yaki.

Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ta kuma ce, har yanzu da kawai adadi mai yawa na shahidai da suke a karkashin baraguzai, ana kuma samun jinkirin fito da su ne saboda rashin kayan aiki.

Daga  tsagaita wutar yaki a  ranar 11 ga watan Oktoba 2025 zuwa yanzu  adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 376, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 981. Haka nan kuma an tono gawawwakin shahidai 626.

Idan aka koma zuwa Oktoba na 2023 kuwa, to adadin shahidan Falasdinawa ya kai 70,365, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 171,058.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka  Talauci Yana Karuwa A “Isra’ila” Bayan 7 Ga Watan Oktoba December 9, 2025 AU Ta yi Tir Da Harin RSF  A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80 December 8, 2025 MِِِِDD:  Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Matsaloli December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest
  • Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jigawa Ta Nemi Kotuna Su Daina Jan Kafa Wajen Aiwatar da Shari’a
  • Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa
  • Karamar Hukumar Agwara ta Jinjinawa Gwamnati Bisa Tabbatar da Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Jama’a
  • Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
  • Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Ta Taya Oluremi Tinubu Murnar Nadin Sarauta a Ile-Ife
  • Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin
  • An Fito Da Gawawwakin Shahidai 98 Da Aka Binne Cikin Gaggawa A Asibitin “Ash-Shifa”
  • MِِِِDD:  Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya