Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-12-12@22:42:16 GMT

Ma’aikatar Ilimi ta Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 18 a 2026

Published: 13th, December 2025 GMT

Ma’aikatar Ilimi ta Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 18 a 2026

Daga Usman Muhammad Zaria 

Ma’aikatar ilimi matakin farko ta jihar Jigawa ta ce za ta kashe fiye da naira miliyan dubu 18 domin gudanar da harkokinta a sabuwar shekara.

Kwamishinan ma’aikatar, Dr. Lawal Yunusa Danzomo ne ya bayyana haka lokacin da yake kare kiyasin kasafin kudin 2026 a gaban kwamatin ilimi matakin farko na majalisar dokokin jihar Jigawa.

Dr. Lawan Yunusa Danzomo ya ce zasu mayar da hankali ga aikin gina ajujuwa da gyaran wadanda suka lalace.

Za kuma a samar da littatafan darussa da tebura da kujeru domin inganta harkokin koyo da koyarwa.

Hakazalika za a  gina bandakuna da samar da ruwan sha da wutar lantarki da tsaro.

Danzomo, ya ce aiwatar da haka zai yi matukar tabbatar da kyakkyawar da’irar ilimi da ta kunshi samar da ilimi cikin sauki ta hanyar shiga makaranta har a kammmala karatu.

Dr. Lawan Danzomo ya kara da cewar za a dauki malaman wucin gadi har su 4000 a karkashin shirin J-Teach.

Ya kuma yi nuni da cewar, za a shirya jarrabawa ga kason farko na malaman J-Teach su 1,450 na gwamnatin da ta gabata domin daukar su aiki na dindindin.

A nasa jawabin shugaban kwamatin ilimi matakin farkio na majalisar dokokin jihar Jigawa kuma wakilin mazabar Fagam, Alhaji Yahaya Zakari Kwarko ya bada tabbacin hadin kai da goyon baya domin samun nasarar da ake bukataa sabuwar shekara.

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano

Ya ce, wanda ake kara ya nema kuma an bashi kudin fansa har Naira miliyan 15 daga iyalan wanda aka kashe kafin su kashe shi.

 

“Sun bugi wanda aka kashe a kai da ƙirji da sanda sannan daga baya suka binne gawar a gidan Adamu da ke Dawakin Kudu,” in ji mai gabatar da kara ga kotun.

 

Da take yanke hukunci, Mai Shari’a Aisha Mahmoud ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da hujjoji game da karar da suka shigar a kan Adamu ba tare da wata shakka ba.

 

“Ina yanke wa Adamu hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya buga wa wanda aka kashe sanda a kansa da ƙirjinsa, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Ubangiji ya yi masa rahama,” in ji ta.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yan Siyasa Ne Ke Zagon Ƙasa Ga Ci Gaban Nijeriya — Sarki Sanusi II December 11, 2025 Labarai Mahajjata 2,235 Ne Suka Yi Rijistar Aikin Hajjin 2026 A Sokoto December 11, 2025 Manyan Labarai Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara December 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Sama da Naira Biliyan 2.6 Domin Aikin Hajjin 2026
  • Hukumar Alhazai ta Jigawa ta Kiyasta Naira Biliyan 3 Don Ayyukan Hajjin 2026
  • Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Garkuwa Da Kashe Mai Gidansa A Kano
  • Hukumomin Ilimi a Jihar Jigawa Sun Kare Kasafin Kudinsu a Gaban Majalisa
  • Gwamnatin Jigawa Ta Kara Samar da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Buƙata ta Musamman
  • NAFDAC ta lalata kayayyakin Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa
  • Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest
  • Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudinta a Gaban Majalisa
  • Ministan Makamashi: Iran Tana Da Sanayya Ta Ilimi Na Samar Da Hadari Domin Yin Ruwan Sama