Aminiya:
2025-12-13@11:53:35 GMT

Amurka ta kama jirgin ruwan dakon man Najeriya

Published: 13th, December 2025 GMT

Amurka ta kama wani katafaren jirgin ruwan dakon man Najeriya kan zargin safarar ɗanyen mai na sata.

Jami’an tsaron Amurka sun kama jirgin mai suna Super Tanker, mai lamba 9304667, ne, bayan sun gano cewa ya yi basaja, inda ya maƙala tutar wata kasa daban maimakon ta Najeriya yayin shigarsa ruwan Amurka.

Wannan ya haifar da shakku kan sahihancin jirgin da ma wadanda ke tafiyar da shi. Daga bisani kuma aka gano cewa ba ya cikin tsarin jiragen da ake tsammani a hukumance.

Hukumomin Amurka sun ƙaddamar da bincike kan jirgin, wanda ake hasashen zai bankaɗo badaƙalar safarar man sata da fataucin miyagun ƙwayoyi da ayyukan ’yan fashin teku da ke shafar ƙasashe da dama.

An shafe shekaru ana magana ba kan matsalar yawan satar ɗanyen mai ayankin Neja Delta mai arzikin mai ya zame wa al’umma tamkar tamkar masifa.

Bayanan kama jirgin

Jirgin mallakin wani babban ɗan kasuwa a Najeriya mai kamfanin Thomarose Global Ventures, yanzu haka yana tsare a hannun jami’an tsaron Amurka.

Bayanan farko sun nuna cewa an fara gudanar da bincike kan alakar jirgin da safarar muggan ƙwayoyi da kuma harkokin barayin kan teku, musamman a zirin Tekun Gunea da ke addabar kasashe da dama, ciki har da Najeriya, Kamaru, Sao Tome da Ghana.

Alƙaluman da aka fitar a watan Nuwamba, shekarar 2025, sun nuna cewa Najeriya ta yi asarar kimanin dala biliyan 300 sakamakon satar ɗanyen mai a ciki da wajen kasar.

Wannan satar mai ba wai kawai tana jawo asarar kudi ba, har ma tana barin baya da kurar gurbata muhalli, lamarin da ke ci gaba da kassara yankin mai arzikin mai na Niger Delta.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ɗanyen mai Najeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na  Venuzuela

Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta kakaba sabbin takunkumi kan bangaren manfetur na kasar Venuzwela da kuma iyalan shugaban kasar Nicolas Maduro da hakan ya shafi tattalin arziki, siyasa da kuma kara matsin lamba kan gwamnatin carakas.

Tattalin arzikin venuzuwela ya doru ne kan man fetur don haka sabon takunkumin kai tsaye zai cutar da gwamnatin maduro ne da kudaden shigarta na asali suna fitowa ne daga man fetur, gwamnatin Amurka ta sanar da sanya sabbin takunkumi kan bangaren man fetur din kasar Venuzuwel da kuma wasu mutane Ukku yan uwan matar Moduro,

Jaridar new york times ta fitar da rahoton cewa takunkumin na Amurka ya tilastawa gwamnatin moduro sayar da manfetur ta barauniyar hanya  ta hanyoyin masu shiga tsakani da kuma tankomin mai,  don haka shugaban Amurka Trump yayi amfani da wannan mataki wajen ci gaba da ikirarinsa na rusa gwamatin Muduro saboda zarginsa da fataucin miyagun kwayoyi,

Yanzu haka dai Amurka tana so ta yi amfani da  matakin doka wajen kwace tankokin mai na kasar venzuwela , kuma ta sanya takunkumi ga kamfanonin mai guda 6 dake da kyakkyawar dangantata da safarar manfetur na kasar venuzuwela.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta Ce Ci Gaba Da Kai Hare-Haren Isra’ila Ya Nuna Gazawar Tsarin Duniya Na Dakatar Da Ita. December 13, 2025 Matatar Mai ta Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699 December 13, 2025 Iran da Rasha sun jaddada aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa a tsakaninsu December 13, 2025 Ali Nuhu, ya yaba wa Iran kan haskaka Musulinci ta hanyar fina-finai December 13, 2025 MDD ta amince da kudurin da ke neman Isra’ila ta bada damar shigar da agaji a Gaza    December 13, 2025 Benin ta fitar da sammacin kama dan fafutuka Kemi Seba December 13, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Za ta Yi Zama Da Bangarorin Da ke Yaki A Sudan December 12, 2025 Birtaniya Ta yi  Barazanar Yanke Gudunmawar Da Take Bawa Kotun Duniya December 12, 2025 Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare December 12, 2025 Shuwagabannin Kasashen Iran Da Iraqi Sun Tattauna A Wajen Taron Zaman Lafiya A Kasar Turkmanistan December 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Ta Sanya Sabbin Takunkumi A Bangaren Manfetur Na  Venuzuela
  • Benin ta fitar da sammacin kama dan fafutuka Kemi Seba
  • Duniyarmu A Yau: Iran Da Amurka A Yakin Kwanaki 12 Wa Ya Sami Nasara
  • Kamfanin CRCC Ya Kammala Shimfida Hanyar Jirgin Kasa A Gadar Layin Dogo Mafi Tsawo A Afrika Dake Algeria
  • ‘Sojojin Najeriya da na Ivory Coast 200 sun shiga domin tsaftace Jamhuriyar Benin’
  • NAJERIYA A YAU: Alfanu Da Kalubalen Sabon Jadawalin Karatun Makarantu Da Gwamnati Ta Bijiro Dashi
  • Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Sha Alwashin Wadata Al’ummarsa da Tsaftataccen Ruwan Sha
  • Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa.
  • An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara